DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August, 2016
{15}Mr. Charles yai ma su jagoranci duk wani abu da za su sun yi shi. An basu dakunan kwana duk wani abu da suke bukata. Ba su suka samu kan su ba sai wajen zkarfe biyar na yamma (05:00pm).
"Abdul na wuce ɗakinmu, sai gobe dan na gaji yau".
"ina son fita ni dai in siyo layi ina son yin waya gida, dan tun a gida na bar simcard ɗina".
"ni ma fa ka tuna mun, wajen 8pm sai mu tafi sannan mun huta".
Da haka kowannensu ya kama gabansa. Sai kalle-kalle ta ke, ganin yanda aka kawata bangon makarantar da zane-zane ma su ban sha'awa. Duk in da ta gifta fitulu ne reras ke ta haskawa.
Da haka ta isa ɗakin da aka bata tabi kwatancen da ke jikin takardar. Saboda gajiyar da ta yi da kyar ta ke jan akwatinta, har ta isa ɗakin.
Shigar ta ɗakin ta ajiye akwatinta, ta bi ɗakin da kallo, gadaje biyu ne 'yan madaidaita sai kafet malale a dakin,gefen kowane gado akwai wardrobe, tare da study table,daga can gefe ɗan karamin fridge ne. Kofofi biyu ta gani da ke kallon juna, ta bude ta hannun damanta,kitchen karami da duk abinda ake bukata dai-dai dalibi. Sai dayar kofar toilet & bathroom ne, da washing machine Dan dai-dai.
Kayanta ta shirya cikin wardrobe ɗin, sannan tayi wanka ta yi sallah.
Ta kwanta tana jiran Abdul ya fito su tafi kasuwa. Takwas saura kwata ta fito cikin doguwar rigar material, ta samu mayafi kalar rigar ta naɗa a kanta.
Ta na fita ta iske shi waje yana jiran ta.
"Rashin waya na rasa in da zan neme ki".
"ni ma sai bayan ka tafi na san mun yi wauta".
"ai shikenan yanzu dai tunda za'a yi maganin abin".
Daga makarantar a kafa su ka fara takawa suna kallon gari ko za su samu shopping mall, sun mike titin da makarantar su yake, sun yi tafiyar da akalla za su kai 30mins, sannan su ka kai titin al-olaya Street. Anan suka ci karo da tamfatsetsiyar shopping mall mai suna RIYADH GALLERY.
"Wow! What a beautiful mall. Abdul mu shiga please ba za mu rasa abin siye ba".
"ko ba mu siya komi ba ma yi kallo, na ga har da restaurant gare su".
Su ka shiga cikin mall ɗin sai rarraba idanu su ke, shaguna ne barkatai a ciki kowanne da abinda ake saidawa.
Sashen wayoyi su ka fara zuwa, Abdul ya siya sabuwar waya da layi. Zainab layi kadai ta siya, sannan su ka shiga wajen restaurant ɗin, pizza suka zaɓa da orange juice. Sai da suka yi kat sannan su ka dawo school.
****************
"Wash! Gaskiya yau na gaji, kin ga irin aikin da mu ka yi a clothing laboratory kamar in dawo hostel kaina har ciwo yake".
"Zee kin cika raki kullum sai kin yi magana idan kin dawo class".
"hahaha Yasmeen har na kai ki ke da kullum sai kin yi mita".
Dariya su ka yi, duk cikin harshen turanci su ke maganar.
"wai ba ki dafa komi ba? Yunwa ni ke ji".
"ga jollof Macaroni nan".
"you've save a life sweetheart".
"hey! Zee you too much like food".
"Idan ba abinci ai ba rayuwa".
"yaushe za ki yi mana samosa da kika yi kwanaki?".
"ki bari sai weekend mu yi".
Watansu Zainab shida kenan a Riyadh,a bangaren fashion design kam ba'a cewa komi dan yanzu bangaren ɗinki da yanka ba abinda ba ta iya ba.
Dama shi ne matsalarta kuma ta iya yanzu.
Ta na jin dadin zamanta a Riyadh tare da roommate ɗin ta Yasmeen 'yar kasar Pakistan. Ga Abdul Hameed da suke haɗuwa akai-akai.***************
"Yasmeen ki tashi mu fita yawo please, bari in kira Abdul mu tafi tare".
"kin cika son yawo Zee".
"ki bar ni Ooh, in samu abin faɗa da nunawa idan na koma gida".
Kaya iri ɗaya su ka sa, wando da riga samfurin ZARA. Rigar ta kai ma su gwuiwa, armless top ce, sun dora jacket a sama. Mayafi su ka naɗa kalar rigar purple. Kafar su sanye cikin sneakers samfurin Kenneth Cole (KC) mai kalar blue & purple.
Sun matukar yin kyau. Tare suka jero, suna fita Zainab ta kira Abdul su ka hadu.
"Yanzu Zee ina kike tunanin za mu?".
"Nima fa ban sani ba, zaman school ɗin ne ya isheni ina son mu dan buɗe ido".
"mu tari taxi dai, ni chocolate ni ke son sha".
"bari in duba mana map mu ga ina zamu je". Faɗin Abdul.
"Wow! We guys are lucky, na samo mana wajen shan chocolate just near us".
"ina ne wajen Abdul?".
"Zee na gaba ne kadan Al-Ouruba road".
Taxi suka samu ya kai su har gaban MAYA LA CHOCOLATERIE.
"hmmm! I've smell it".
"kai Yasmeen daga tsayuwar mu".
"Nima fa na ji Zee".
"ku kam dai kamar Mayu ku ke, ni dai kar ku kunya ta ni, ba kamar kai Abdul kana dai ganin mu 'Yan bakake".
"Zee ba ki rabo da abin dariya, ai hasken fata kawai za mu nuna ma ki amma kina da kyau, ji yanda Riyadh ta karbe ki fatar ki na ta rikiɗa".
"kin gama mun sharrin? Ku wuce mu je".
A bakin kofar su ka karanta kamar haɗin baki "chocolate for a better world".
Bayan sun sami wajen zama, suka duba menu ɗin dake ajiye saman teburi.
"kowa ya zaɓi irin chocolate ɗin da yake so".
"Yasmeen karanto mu ji".
"akwai Belgian waffle chocolate, chocolate crepes, milk chocolate, vanilla scoop chocolate ku zaɓi cikin wadannan na gaji da karantowa".
Zainab ta ce "aban chocolate crepes".
"Ni milk chocolate ni ke so".
"toh ni kuma Belgian waffle ".
Mai kula da wurin ya zo suka faɗi duk abinda suke so.
Cikin minti goma (10mins) ya iso dauke da tray da filet a sama hade da cutlery set ya ajiye ma kowa na shi.
Zainab ta sa cokali hade da wuka ta yanko chocolate ɗin, runtse idanunta ta yi tana taunawa a hankali, wani ɗadi na ratsa ta har cikin kunnuwanta. Dariyar su ta ji, ta buɗe idanunta. Yasmeen ce ta saita Zainab da camera tana daukarta hoto.
************
Shekarar su guda kenan a Riyadh, sun sami hutun karshen shekara.
"Momi dan Allah a turo man kuɗin jirgi in zo in ga babyn aunty J, kin ga anyi bikin Jidda wata hudu da suka wuce, ina son in zo in ganku".
"yauwa Momi ai na san kinyi kewa ta, nagode Allah shi kara arziki".
Tsalle ta buga saman gado.
"Zee lafiyar ki kuwa?".
"gida Nigeria za ni in yi hutu na, ba zan iya zaman two months ba".
"wayau za ki mana kenan?".
"A'a ba dai ku so tafiya bane kuma".
Cikin kwana biyu Zainab ta gama shirin tafiya, tayi tsaraba himili guda. Ba wanda ba ta yi ma tsabara ba. Jakkarta tayi nauyi sosai, ba ta ma iya dauka.
NIGERIA
A Abuja su ka sauka, sannan ta sake bin wani jirgin zuwa Sokoto.
Isar su Sokoto kenan ta sauko tana janye da katon trolley bag da ba komi ciki sai tsarabar mutane.
Idanu ta ke ta rarrabawa tana tunanin ta inda zata hango su Momi.
Tana ɗaga kanta ta hango aunty J, ta saki trolley bag ɗin kasa. Sai a kan kafar shi.
"Ouch!" ya furta. Ya ɗaga kai dan ya tantance wanda yai ma shi wannan aikin.
Makalkale aunty J ta yi, sannan ta dauki Huzaifa.
"aunty J yaya Habib ya ma ki wayau, kamar shi sak".
"Auta! Wannan wane irin rashin hankali ne kin saki akwati a saman kafar mutumi ba ki ko damu ba kin zo kina surutu".
"Yaa Allah! Wallahi sam na manta fa da akwati a hannu na, kan kafar wa saki akwatin?".
"Oho! Ki je ki dauko abin ki ba ruwana ".
A hankali ta juya zuwa inda ta hango akwatinta. Ya juya baya yana amsa waya, ji ta yi zuciyarta na harbawa fat! Fat!! Fat!!!, ta ji zuciyar ta buga dam! A sa'ilin da ta yi arba da fuskar shi.
Kamshin turaren shi ya doki hancinta. A kasan zuciyarta ta furta Samir Alkali!chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu
KAMU SEDANG MEMBACA
DOGARO DA KAI
AcakIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...