BABI NA SHIDA

1.5K 115 4
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016
{6}
Labeeba da Habiba sun sami admission a Federal University, Gusau. In da aka ba Labeeba B. Ed English Language, Habiba kuma Bsc. Computer Science. Kullum Danliti ke kai su ya dawo daukar su. Ko basu da lectures na safe ka'ida takwas saura ake kai su, a dawo 6pm. Doka ce daga Daddy dan yace be son almubazzaranci. Da kyar ma ya yarda a rinka kai su, shi ma dan Momi ta sa baki ne, tace za ta rika bada kudin man fetur duk bayan sati biyu.
Hakan ya kara ma ta daraja a idanunsu Labeeba, duk da haka Hajiya ba ta yada makamanta ba na kiyayyar Momi.
Zainab sun koma makaranta, sun dage da karatu ganin gab su ke da fara SSCE. Ita da Jidda ba su da lokacin komi sai karatu. Zaune su ke a class su na solving past questions na Q&A.
"Jidda zan ga ranar da zamu yi graduating, har na fara plan ɗin duk abinda zanyi idan mun koma matukar Allah ya ara man rayuwa".
"Zee ba ki rabo da buri ke dai".
"Ki bari kawai Allah kadai ya san abinda ke raina, I have a lot of things running into my heart".
"Allah dai shi nuna mana dai".
"Amin ya Rabbi".

***************
Zaune suke a exams hall ana raba ma su booklet da question papers. Jarabawar English suke rubutawa, Zainab da ta dukufa ta na ta rubutu cikin natsuwa, fatan ta samun nasara a wannan jarabawar.
A kwana a tashi yau ne su Zainab ke kammala jarabawar su ta NECO. Fuskar ɗaliban kadai za a duba a tabbatar da hakan,farin ciki kwance a saman fuskokinsu.
Zainab da Jidda tsaye da sauran kawayen su, suna maida yanda aka yi akan jarabawar da suka yi. Suna tsaye Zainab ta hango motar Yaya Habib, da gudu ta karasa gaban motar, Aunty Jamila ta fito rike da hannun Sultan dan kimanin shekara huɗu.
Ta ruga da gudu ta rungume aunty Jamila, tare da daukar Sultan da kyar ta na nishi. Ta ajiye shi ta koma wajen Yaya Habib ya dafa kafaɗarta yace "Auta anya kina karatu kuwa na ga kin kara girma".
"Allah ina yi, ka tambayi Jidda".
Jidda ta matso ta gaida su. Sannan su ka kama hanyar Gusau.
Awa ɗaya da rabi ta kai su Gusau saboda gudun da Yaya Habib ke yi. Jidda aka fara saukewa sannan suka wuce gida.
Farin ciki kwance a saman fuskar Momi ganin Autar ta, ji take kamar ta goya ta. Addu'o'i ta dinga kwarara ma su, tana sanya ma su albarka.
Dakinta ta shiga ta iske shi tsab a gyare, wanka ta faɗa. Bayan ta fito, ta yi shafa tarkacen cosmetics ɗinta na ORIFLAME (Milk& Honey). Bata da kayan shafa da su ka wuce na Oriflame, dan sun amshi fatar jikinta. Wadanda ta iske sabbi ne Momi ta siya ma ta, aka jera ma ta saman dressing mirror, na wanka kuma a bandaki aka jera su suma.
Doguwar riga kirar Bahrain ta dauko cikin jerin kayanta da ke ajiye a wardrobe, ta sanya tare da fesa turarenta na kaya. Kwalli kadai ta shafa da powder, sai lip gloss na VERYME. Sallah ta yi ta la'asar, ta dawo falo ta iske Momi da Aunty Jamila nan ta zauna tana ta basu labarin makaranta. Asabe ta fito daga kicin dauke da tray shake da abinci a jera, ta ajiye gaban Zainab.
"Uwar ɗakina ga abincin da ki ka fi so nan, harda tagomashin lemun kwakwar nan da abarba da na ga kin taɓa yi".
"Kai amma fa nagode Baba Asabe naga alamar ke kadai ke murnar dawota, kin ga ko su Yaya Labeeba ban gani ba".
Ta bude food flask da ke dauke da alkubus na alkama zalla, dayan kuma miyar tashe ce da ta ji gyada, sai ďayar na pepper chicken, da jug na coconut & pineapple juice.
Zainab ta fara cin abinci tana santi, saboda ɗaɗin miyar. Sallamar su Habeeba ta ji sun shigo falon, nan su ka gaida Momi da Aunty Jamila, su ka taya Zainab murna. Nan kuma hira ta barke, ana maida yanda aka yi.
Sai bayan maghriba Aunty Jamila suka tafi gida.
****************
"Momi dan Allah ki bar ni in shiga Najfar's Kitchen ɗin, duk abubuwan da suka shafi kitchen ake koyarwa, kin ga nima zan karo da wasu abubuwan".
"Ke ni ba ruwana ki je ki tambayi Daddyn ku idan ya amince, dan na yi maganar Computer training da ni ke son ki yi har yanzu be ce komi ba".
"Gobe da ya dawo daga Abuja zan je in faɗa ma shi, tunda shi Najfar's kitchen ɗin weekends ne".
"Yanda ki ka gani dai".
Washegari da dare misalin karfe tara na dare, Daddy na zaune a kayataccen falon shi yana kallon NTA news, Hajiya na gefen shi ita ke da girki ranar.
Zainab ta shigo da sallamarta, bayan ya amsa ta shigo tare da gaida shi bayan ta zauna.
"Daddy an dawo lafiya?"
"Lafiya lau Mamana, ya akayi ne?".
"Dama Daddy kan maganar Computer school ne da ni ke son shiga da catering school kafin jarabawarmu ta fito".
"Mamana kenan, na lura ba ki son dai zama hakanan, miye amfanin catering school ɗin ne?".
"Daddy ana koya yanda ake girki ne, duk wani nau'in abinci akwai yanda ake sarrafa shi kala-kala, har da yanda za a yi kasuwanci duk ta harkar abinci".
"Girkin ne ba ki iya ba Mamana ko kuwa?"
"A'a Daddy ina dai son in kara ne akan wanda na sani, Please Daddy".
"Shikenan, ki je duk abinda ake bukata ki lissafo ki rubuto man, sai ki ba Mamanki, za ki ji sakona wajenta".
"Toh Daddy nagode kwarai, Allah shi kara buɗi na alkhairi, ya tsare mana kai daga dukkan wani sharri". Ya dafa kanta tare da furta "Amin Amin Mamana,Allah ma ki albarka, ya ba ki miji nagari".
A kunyace ta mike, tare da faɗin "Amin", a kasan zuciyarta.
Hajiya da ke gefe sai hararsu ta ke, Zainab na fita, Hajiya tace "Yanzu Alhaji abinda ka ke ka kyauta kenan? Ka nuna bambanci tsakanin su Labeeba da Zainab, su sanda suka gama ai baka sa su a Computer school ba".
"Ban sa su, saboda basu nuna suna so ba, ita da ta nuna tana so ai ga shi zan ma ta. Dan haka ba ni son kananun maganganu".

Zainab ta fara zuwa Computer school, Monday zuwa Friday, karfe 10am zuwa 2pm take dawowa. Najfar's kitchen kuma Asabar da Lahadi take zuwa tun karfe goma na safe zuwa karfe shida na yamma.
Kwance ta ke, tana bacci ta ji wayarta na kara tana dauka ta ga Jidda ce, cikin karaji ta ce "Kai da gaske ki ke?".
Da gudu ta fito, ta faɗa ɗakin Momi.
"Momi, Momi, Momi exams ɗinmu ta fito yanzu Jidda ta kira ni".
"Alhamdulillah! Allah ya sa mu ga alkhairi, sai ki shirya ki je ki dubo".
Gaban Zainab na ta faɗuwa, haka suka jera ita da Jidda su ka hau keke napep. Tudun wada ya kai su, suka shiga Dinawa cafe.
Sun sayi scratch card, aka fara duba ma Jidda, aka miko ma ta, ta budawa ta ce "na shiga uku Zee, ba English ba Mathematics".
Zuciyar Zainab ta cigaba da harbawa cikin sauri, ana miko ma ta na ta, ta hau furta "Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un".
Hawaye ne ma su zafi su ka zubo ma ta.

Love y'all 😘..
chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now