DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
3rd September, 2016.
I dedicated this chapter to all my readers.. I so much love you, without you I'd have not been in this stage. Xoxo 😘 😘KARSHE
*********
"Ya Allah! Gaskiya ni kun dame ni a yi ta dirge ma mutum jiki. Haba so ku ke asthma ta kama ni, ni wallahi wannan hayakin turaren ya ishe ni. Am not smelling bad bare ku dame ni".
"heh! Village girl. Dan martabarki ake ma ki, kin bi kin dami mutane da surutu".
"Aunty J duk ke ce wallahi, ni fa na yi booking khumra daga Ziya'atulhaq. Mutane na son khumra ɗinta. Idan ki ka samu hmmm Yaya Habib sai ya dauki leave a office".
"Ooh ba za ki kashe ni ba Zee".
"Hajja Fannah do you best for my sister In-law ".
Tunda bikin Zainab ya rage sati biyu Aunty J ta dauko Hajja Fannah daga Maiduguri dan ta gyara Zainab.
Kwalliya kam ta biya kudin sabulu dan Zee ta yi kyau, jikinta kamar na jinjiri. Kamshi na fita a jikinta ko ta ina.
Su Labeeba sun je Abuja an shirya ma Zee gidan ta da ke Life camp.
Gidan ya tsaru iya tsaruwa.
KARFE 10:06PM
"Assalamu Alaiki my wifey!".
"Wa alaikumus Salam Mon Cherie".
"Cutie pie am missing you more than words can explain! Fisabilillahi su aunty J sun kunshe ki gida sun hanani ganin ki,ina kewar wadannan smokey and sparkling eyes dinki, with that soft and sweet voice that makes me feel like I'm the luckiest person ever".
"Ya Salam! Ka yi hakuri it is just a matter of time. Duk four days ya rage mana".
"This four days are like a hell to me".KAMU 04:00PM
"MashaAllah! Zee you look like a princess".
"Huh! You look like a baby doll".
"Wow! Zee you're more than beautiful ".
Sautin dariya ke tashi a ɗakin Zainab.
A hankali ta ke takawa har ta isa bakin motar da za ta kai su Fulbe Hall.
Suna isa su ka iske ango ya iso, sanye yake da blue & white kaftans na bugaggiyar shadda, ya kafa hular shi zanna bukar da ta dace da kayan shi. Tsintsiyar hannunsa daure da farar agogon fata samfurin LACOSTE. Murmushi ne dauke a saman labbanshi. Narkakkun idanunsa ya zuba ma ta a yayin da ta fito, ji yake kamar ya rungume ta.
Sanye ta ke da royal blue ɗin aso-ebi hade da fatsi-fatsin silver a jiki. Komi nata blue and silver ne. Simple ɗinki buba ne a jikinta da single zani da bai sauka kasa ba. Head gear ɗinta ya bude sosai, yanda ya kara fiddo da kyawun fuskanta.
Cikin takun isassun maza ma su ji da kansu ya karaso wajen. Tare suka jera kawayen amarya na take masu baya.
Zaune suke a yayin da kidan taushi ke tashi. A hankali ya kai bakin shi saitin kunnenta.
"Babe you smell good,what's the secret?"
Murmushi ta yi ba tare da ta ce uffan ba. Dan ya kashe ma ta jiki.
DAURIN AURE 11:00AMDubban jama'a ne suka halarci daurin auren Samir Ahmad Alkali tare da amaryar sa Zainab Isma'il Gumi. Mutane ne dankam a kofar gidansu Zainab. Duk wani masoyinsu ya zo taya su murna.
ZAINAB
"Allah! Allah!! Aunty J zuciyata bugawa take fat! Fat!! Fat!!! Yanda ki ka san ana lugude".
"Alhamdulillah! An daura kenan, Autar Momi ta shigo sahun manya".
"Auta gashi can an gama daurin aure". Faɗin Habeeba.
Labeeba ta rangada guda tare da rero wakar biki.
"alkawari ya cika amarya....".
Hawaye ta ji suna zuba bisa kuncinta.
Kamar daga sama ta hango Jidda.
"Jidda! Ke ce?".
"Ni ce Zee ".
" Yaa Allah! Banyi zaton za ki zo ba, ganin jiya ba ki zo kamu ba".
"na so zuwa jiyan matsala aka samu".
Kallon Jidda kawai ta ke yanda ta yi sanyi kamar ba Jidda da ta sani ba.
Hannunta ta ja su ka shiga daki.
"Jidda mi ke damunki? You're completely pale".
"Zee please ki yafe mun, I know I've been selfish na raba ki da Hafeez, ina tunanin zan samu duk abinda nike so, am totally mistaken. Hafeez be da hali Zee, tunda mu kai aure ban samu peace of mind ba. I always wish Ina ma ni ce ke, ki gode ma Allah Zee".
"Shhhh! Ya riga ya wuce Jidda ko da can ban rike ki ba. Ki yi biyayya ga mijin ki, ki so abinda yake so, ki kuma ki abinda yake ki,za ku zauna lafiya kamar sauran couples ".
Aunty J ce ta shigo ta ja hannun Zee.
" Ina za ki kai ni?".
"Samir ke neman ki, za ku dau hotuna".
Fitataccen photographer George Okoro ya gwangwajesu da hotuna ma su kyau, tun daga Abuja Samir ya yi booking ɗin shi.

YOU ARE READING
DOGARO DA KAI
RandomIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...