DOGARO DA KAI
© Ayeesh Chuchu
August,2016I dedicated this chapter to hanas291011, bint1998, KhadijaAminu, salmasardauna & deeAbdul for your comments and votes. Love you loads.
{10}
Suna nan tsaye bakin titi, Zainab ta yi tsaki bayan ta duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta.
"Ni fa ban san ɓata lokaci".
"Lallai Zee ke da za'a biya hakkinki shi ne kike nuna gajiyawarki".
"Haba ji yanda rana ta kwale".
Mota ce kirar SABARU LEGACY mai kalar ruwan toka, ta yi parking a gefen titi.
"Yaa Allah! Zee kalli motar nan ta tafi da ni wallahi".
"Hahaha ke dai kina son mota".
"ba motar ba, mamallakin motar ma na san yafi motar kyau".
"uhmm ga taxi nan tafe ni dai mu tafi".
Kamar daga sama ta ji an ce "friend".
Murmushi ta saki ganin sa tsaye, ya harde hannu a kirji.
Sanye da kanana kaya, Polo Shirt mai ruwan bula sanye a jikin sa samfurin Ralph Lauren hade da wandon jeans. Kafarsa sanye cikin blue & black sneakers.
Jidda da ke tsaye ta kura ma shi idanu kamar za ta cinye shi ɗanye.
"ba ka iya sallama ba ne?".
"oh Sorry Ustaziya Assalamu Alaikum".
"Wa alaikumus Salam wa rahmatullahi wa Barakatuhu, ko kai fa".
Murmushi ya yi, Jidda da ke tsaye mamakin ta ke ina wannan mutumin ya san Zainab.
"Meet my friend Jidda Umar".
hannu ya mika ma Jidda su ka gaisa.
"Am Hafeez Sulaiman Ibrahim nice to meet you".
"it's my pleasure to meet you".
Wata muguwar harara ta balla ma su.
Yanzu ta fara fahimtar Hafeez, tsab dabi'un turawa gare shi.
"ba ni sakona sauri ni ke in tafi gida".
"mu tafi in kai ku gidan, dama abinda ya biyo da ni kenan".
"A'a ni fa ba zan bi ka ba".
"please Zee mu je". Yanda ya wani langaɓe fuska ya sa ta bi shi, Jidda na biye da su a baya.
Shi ya bude ma Zainab ta shiga. Sun fara tafiya yake tambayar Course ɗin da su ke, Jidda ce ke ta ba shi amsar yawancin tambayoyinshi.
"Jidda wannan kawar ta ki na da aljanai ma su hana ta magana ko?".
"A'a haka dai ta ke".
"Hmmm ni ma haka ni ke, ita ke sa ni surutu fa, this is the second time I met her, Amma na zama talkative a wajenta I don't know why ".
" I think you've crush on her".
"Yes! Yes!! Yes!!! Ashe kin gane?".
"Eh na yi reading mind ɗin ka".
Tsaki Zainab ta yi, ji take kamar tayi ta ihu dan takaicin abinda Jidda ke yi.
"kin ganta ko Jidda, tsoro ta ke ba ni".
"shikenan ka bada Maza in dai Zee ce za ta rika ba ka tsoro".
"No! Ta mun kwarjini ne,I can't hide it anymore Jidda Ina son kawarki, please ki taya ni campaign".
"kar ka damu an gama sai yanda ka yi da Zee in dai ina raye".
Surutu su ke ta yi har su ka iso Layin da kwatancen Jidda, ita su ka fara saukewa sannan ya wuce da Zainab.
Zaman kurame su ke har su ka isa bakin gate ɗin gidan su Zainab.
Zata bude motar, yayi locking ɗinta.
Ta juyo da masifa, kallon da ya ke ma ta yasa ta sadda idanunta kasa, ba za ta iya jure haɗa ido da Hafeez ba, ya matukar kashe ma ta jiki.
"Zee please ki saurare ni, ba wasa ni ke ba tun last three days ni ke neman ki, ban san in da Zan same ki ba, sai dazu Mum ta ban number ɗin ki da sakon da Zan kawo ma ki. I feel like I'm in the heaven,hoping that Zainab will accept my request".
Ta kasa gane mi ta ke ji game da Hafeez.
"please say something Habibty".
"ka ba ni lokaci".
"zuwa yaushe?".
"zan faɗa ma later".
"Thanks Bae, kin yarda in rika kiranki muna gaisawa?".
Kai ta gyada ma shi.
"please unlock the door, zan fita ba ni son mutane sun ganni na fito daga cikin motar ka".
Murmushi ya yi "Feel free, ban zo da niyyar cutar ki ba".
Ya miko ma ta envelope guda biyu, ga sakon nan.
Ba ta tsaya dubawa ba, ta amsa.
"kace ma ta nagode kwarai, ina gaida ta".
"zan ce ma ta In-law ɗinta na gaidata".
Murmushi tayi, za ta fita ya riko hannunta.
Ta yi saurin fizgewa, "Hafeez kar ka sake gigin taɓa mun hannun bani son iskanci".
"Am so sorry banyi da wata niyya ba, bani son ki tafi ki bar ni ne".
"Ni dai na faɗa ma".
Fuu ta fita kamar guguwa.
Kallo ya bita da shi har ta shige cikin gidan ba tare da ya bar kallon gate ɗin ba.
Lumshe idanun sa yayi, sai dai ya dau a kalla mintuna biyu. Sannan ya ja motar shi ya tafi.
Gidan tsit dan school ta baro su Labeeba,Momi ma ba ta nan. Sallah tayi ta ci abinci.
Kan two seater da ke a falon ta kwanta, ba tare da ta kauda kwanukan da ta ci abinci ba.
Lumshe idanu ta yi, tana jin wani irin yanayi a tattare da ita mai wuyar fassarawa.
"Hafeez" ta furta a hankali wanda labbanta ne su ka motsa.
"Yes! Ina son shi, dabi'un shi ne ba su yi mun ba. Komi na shi dabi'ar turawa ce".
Wata zuciyar ta ce ma ta "Za ki iya canza shi tunda yana son ki, ki jajirce akan ya bar dabi'ar da yake yi matukar yana son ki, ki tsayu akan ra'ayinki kar ki bari soyayya ta canza ma ki akala, ya zama shi ke controlling ɗinki".
Murmushi ta yi bayan ta gama aminta da zancen zuciyarta.
Envelope ɗin ta dauko ta guda biyu ta gani, ta farkon ba suna, ta bude ta, kudi ne suka fado yan ₦1000 bandir guda, wanda ya kama ₦100,000. Hannuwanta ta daga sama tana mai godiya ga Allah. Sunan Momi ta hau kira sai ta tuno da ba ta nan.
Ďayar ta dauko, sunan shi ta ci karo da shi cikin wani tsararren rubutu da manyan baki "HAFEEZ".
Takardar da ke ciki ta fiddo mai kalar pink da zanen flowers a ciki, kamshi ne mai sanyin dadi an rubuta "I love you with all my heart Habibty". Murmushi ta yi wanda ya kara kawata fuskarta.
**************
A kwana a tashi kwanaki sun zama watanni, watanni sun zama shekara.
Zainab sun shiga 200 level, inda su Labeeba ke shekarar su ta karshe. Wanda da sun gama za'a yi bikin su. Zainab kuwa sana'a ba kama hannun yaro, damma makaranta da take zuwa shi ke taka ma ta burki,duk da haka tana samun alkhairi sosai,dan tafi maida hankali kan yin snacks.
Aunty Jamila ta sake haihuwa, ta samu diya mace mai sunan Momi (Fatima) ana kiran ta da Amatullah. Sam yaya Habib ya hana ta aiki, dan ta samu offer da kotun jiha. Case har wajen Momi amma ya shafa ma idanunshi toka, dole ta hakura dan jali ya ba ta ta kama sana'a.
"Wash Jidda yunwa ni ke ji".
"ki kira Lovey Dovey ɗin ki ya kawo mana takeaway".
"Allah shi kyauta kamar wasu Mayu, ni kin sa ni jin kunya ma".
"Ni fa tsiya ta dake ke ala dole jan aji, ke kin san Hafeez ya fi ki kyau nesa ba kusa ba".
Maganganun Jidda sun taɓa ma ta zuciya, ta dai shanye ne gudun kar suyi yada hali.
Kamar daga sama ta ji kamshin turarensa wanda ko cikin bacci ta san ko na waye.
Murmushi su ka jefi junansu da shi.
"kun gama mu tafi?".
Kai ta daga ma shi dan tsabar yunwar da ta ke ji.
Basu zarce ko ina ba sai FULBE RESTAURANT. "Honey bunch!.."
Girar shi ya daga sama," don't say anything, nasan yunwa ki ke ji, ba ki san cewa ina karantar kowanne yanayi na ki ba".
"Ooh bayan karantar yanda ake kera furnitures har ka koma karantar mutane?".
"why not, tunda Ina tare da ke".
Fita ya yi yayo ma su takeaway ɗin roasted fish da chips, hade da lemuka ma su sanyi.
Sannan su ka tafi, ya sauke Jidda gidansu.
"Habibty ban so ki tafi, ban ki mu yi ta zama haka ba har Allah ya amshi rayuwarmu".
Murmushi tayi. "Allah da gaske haduwa ta dake alkhairi ne, kin sa na sauya dabi'u zuwa wanda ki ke so kuma nima na ji dadi, ya'yana zasu mori uwa ta gari,yaushe zan turo ne?".
"Kaga yanzu bikin su yaya Labeeba ne akan layi, sai anyi nasu tukunna".
"Allah ya nuna mana".
"Amin".
Ta fita suna daga ma juna hannu kamar kar su rabu.
Sallah ta iske Momi nayi, ɗakinta ta tafi, roasted chicken da chips ta fara ci sannan ta kora da lemu, sannan ta ji ta dawo dai-dai.
**************
Tun da ta tashi ta ji gabanta na faduwa, addu'a take a cikin zuciyarta na neman tsari.
Ba ta jin dadin jikinta ta kwanta.
"Auta dan Allah ki tashi mu tafi gurin event planner ɗin tunda ke kika san ta, za ta fi mana ragi".
"Sis Beeba Beeba kaina ke ciwo fa".
"Allah hakanan za ki tashi mu tafi".
Bata da yanda za ta yi, Hijab kawai ta daura saman riga da wandon da ke jikinta.
Motar Momi su ka dauka, Zainab ke driving tasa wakar Zain Bhika mai taken "Allah knows".
Ta na bin wakar tiryan-tiryan. Har su ka je Premier road ina shagon matar yake, sun zaɓi irin decoration ɗin da su ke so, sun bata rabin kudinta sannan su ka juyo.
Sun kai dai-dai pinks cafe Habiba tace "taimaka ki tsaya mu sayi burger da meatpie".
"ok ni ma ina son pizza ko shawarma idan suna da shi".
Sun yi parking gefen titi, suka fito.
"Sis Beeba kin ji yanda gabana ya faɗi, har kaina sai da ya sara".
"ba komi sai alkhairi".
Suna shi ga suka tambayi abinda ya kawo su ba tare da sun sami wuri sun zauna ba.
"kash! Ni fa ban son zama wajen nan mu koma mota mu jira kawai tunda ba wani dadewa za'a yi ba wajen hadawa".
"A'a Auta tunda dai ga wajen zama mu zauna da mu yi tafiya biyu".
Ba ta da yadda za ta yi dole suka sami wuri su ka zauna.
Idanunta a rufe ta jingina da kujera, kamar an tsikare ta ta bude su fes akan su.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un". Ta furta tare da runtse idanunta ta bude dan ta tabbatar da abinda ta gani gaskiya ne.
Hammmmmmm am 😦 yawning for yunwa. Dole ta sa zan dan dakata in nema ma cikina abin taunawa. #rotflWaiting for your votes, comments and suggestions.
Wattpad @ayeesh_chuchu or chuchungaye.wordpress.com.
A'ee na kaunarku much much more.
ESTÁS LEYENDO
DOGARO DA KAI
De TodoIt's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da k...