BABI NA BIYAR

1.5K 116 1
                                    

DOGARO DA KAI

©Ayeesh Chuchu

August,2016

{5}
CIGABAN LABARI

Zaune suke a gaban hostel ɗin su,"Zee wallahi Labeebar gidanku ta iya muganci, wai kin ga dazu ta sa su Sanah Matazu jan gwuiwa tun daga dinning hall har class".
"Su suka kyale ta, ai ta san hali na Jidda, daga an ba su rikon kwarya shikenan sun addabi mutane".
"ai kinga Habiba ba ruwanta duk da ita ce headgirl".
"Ai halinsu ba ɗaya ba ma ko a gida".
*********
"Wow! Habeeba ji nike kamar in ta ihu dan dadi". Faɗin Labeeba suna tsaye bakin gate ɗin FGGC Bakori, suna jiran Danliti direba.
"Ba ihu za ki yi ba, Allah za ki gode ma wa da ya nuna ma ki wannan rana".
"Kai su Habeeba ustazai".
Suna tsaye Danliti direba ya zo daukar su,ya amshi kananan trolley bags ɗinsu ya jefa a boot. Labeeba na ta yauki ganin sabuwar motar da Danliti yazo daukar su da ita, dama burinta kenan aga irin daular da su ke ciki dan ba ta son raini.
Su Zainab sun samu hutun session, ta dawo gida in da za su kwashe wajen sati shida suna gida.
Tsaye ta ke a kitchen sai haɗa zufa ta ke, sanye take da doguwar riga ta material mai silbi, ta daura apron a sama, hannayenta sanye da hand gloves, ta na cake icing.
Muryar Jidda ta ji tana tambayar Momi ina Zainab bayan sun gaisa.
"Mutuniyarki na kitchen tana sana'arta".
Kitchen ɗin ta shigo. "Zee Gumi business woman".
Murmushi ta yi, "ki bari kawai ina ta fama da decorating wannan cake ɗin anjima da maraice ma su shi za su amsa na birthday ne".
"Kai amma ya yi kyau fa,ni zaman gidan ne ya ishe ni na fito".
"Lallai Jidda ki nemi abin yi ba za ki ji kin gaji ba, tunda zai sa kiyi ta kazar-kazar".
"Hmmm ni fa laziness ɗina ba zai bari in yi wani abin kirki ba".
"lallai Jidda da sauran ki, ni yanzu yanda ni ke ji na ba zan iya zama ba sana'a ba, wani abin sai ma mun gama secondary school dan zaman banzan nan da ake yi, ina ta tunanin abinda zanyi apart from snacks making".
"Zee ba ki da dama yanzu har wani tanadi ki ke ma gaba".
"Ki dai tsaya nan, sai dai ki ji ana neman professional snacks maker Zee Gumi".
Suka kyalkyale da dariya.
*************
Jarabawar su Labeeba ta fito inda kowaccensu ta samu 9 credits, murna wajen su ba'a magana.
Ganin irin nasarar da su ka samu yasa Momi ba su kyauta.
Kayan shafa ta haɗo ma su da inner wears duk designers. Kowacce da shopping bag ɗinta shake da kaya.
Zainab da ke zaune ta tattara hankalinta akan game ɗin da take bugawa da system ɗin Momi.
Momi ta fito ɗaki dauke da shopping bag ɗin su Labeeba ta ce "Auta tashi ki kai ma su Habeeba kayan nan".
Ta tsaida game ɗin da take, ta amsa ta wuce sashin su Labeeba.
Ta na shiga ta iske ba kowa a falon, ɗakin baccinsu ta wuce, Labeeba kwance tana karatun littafin Hausa, Habeeba kuma ta fito wanka tana goge jiki.
Ajiye kayan ta yi zaman gado ta ce"Gashi nan inji Momi gift ne ta baku na result ɗin ku".
Da sauri Labeeba ta tashi tare da zazzage kayan, Habeeba tace "Wow! Wannan designers ɗin namu ne?".
Zainab ta girgiza kai alamar "Eh".
Da gudu Habeeba ta dau ledar sai ɗakin Hajiya.
"Hajiya kinga abinda Momi ta kawo mana".
Tsaki Hajiya ta yi bayan ta duba su, "Wannan ai ba gwaninta ta yi ba kuɗin ubanku ne,dasu take takama".
"Haba Hajiya miya sa ki ke haka ne, kin san Momi dai tana aiki, kuma ga Yaya Habib ma".
"Dalla can sakarar banza kan wannan abin har ta siye ku".
Labeeba ce ta shigo, ta ce "Gaskiya Momi yar aljanna ce duk abinda ake ma ta sam bata damuwa".
Tsaki Hajiya ta yi, "ku tashi ku ban waje kar ku dame ni da batun Fatima".

chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DOGARO DA KAI Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang