BABI NA SHA UKU

1.6K 99 4
                                    

DOGARO DA KAI
©Ayeesh Chuchu
August,2016
{13}

"Habibty ga ni na shigo kuna ta wajen ina?".
"ka jira ba sai ka fito ba, na hango ka".
Ta datse kiran.
"Jidda ta so mu tafi".
"ba in da za ni Zee".
"Wallahi sai kin je idan kuma kaffara za ki sa ni to shikenan good & fine".
Ba ta da yanda za ta yi, haka ta bi bayan Zainab.
Kwantar da kanshi ya yi saman steering motar. Karar kwankwasa gilas ɗin motar ya ji ya yi unlocking ɗinta.
Zainab ta buɗe ma Jidda bayan motar ta shiga. Sannan ta zagaya ta buɗe ta gaban.
Ya ðago idanunshi da su ka rine zuwa kalar ja, ya sauke su akan Zainab.
Murmushi ya sa ki ganin yanayin fuskar Zainab mai tattare da aminci da salama.
"Habibty kin wahalar da ni".
"Hafeez ina tunanin mun bar wannan maganar, mi yasa ka ke son maida hannun agogo baya ne?".
"ban fahimce ki ba?".
"ai ina ce mun gama magana tsakanina da kai? Hafeez ka rantse mun da Allah ba ka son Jidda".
"ba zan ma ki karya ba dan ba mu gina soyayyarmu akanta ba, quite right Ina son Jidda amma ba kamar yanda ni ke sonki ba".
Murmushin yake ta yi, zuciyarta na bugawa da karfe. Wani irin kishi ya taso ma ta,dole ta danne zuciyarta.
"abinda ni ke son ji kenan. Hafeez ga amanar Jidda na ba ka,ba ni da burin da ya wuce in gan ku a karkashin inuwa ɗaya".
"Zainab ba zan iya ba, idan har na rasa ki ba ni da sauran buri a rayuwa,dan haka ki cire wannan maganar ma a ranki".
"Toh wallahi tunda ka buɗe baki ka ce kana son ta, you've no any other option, ko ka so Jidda ko kuma in nuna man duniya evidence ɗin cewa kun ci amanata".
Hotunan da ta dauke su ta buɗe tare da nuna ma shi.
"Zainab please ki goge hotunan".
"ka yi man alkawarin zama da Jidda har abada, za ka bata duk wata kulawa da take bukata ".
" na yi ma ki alkawari, amma ke fa?".
"ka bar magana ta Hafeez,ina son tarayyarmu ta zama tarihi ka manta cewa ka taɓa son wata 'ya mace wai ita Zainab".
"Zainab wannan horon da ki ke man ya isa haka, I can't take it anymore".
"Ok! Ga ka ga Jidda ina ma ku fatan alkhairi,Jidda ga amanar Hafeez nan".
Sai a sannan ya juya baya ya kalli Jidda.
Zainab na fita Jidda ta dawo gaban motar.
Hawaye ta ji suna zarya a saman fuskarta. Hannu tasa ta goge su, ta karasa in da ta yi parking mota ta shiga. Ji ta yi ba ta iya jiran Jidda, ta ba motar wuta cikin wani matsiyacin gudu, da kariyar Allah ta isa gida.
Momi da Hajiya ta iske a falo su na fira, ta gaida su za ta wuce Hajiya ta ce "mi ke damunki ne Auta?".
"kaina ne ke ciwo".
"Allah shi sauwake".
"Amin".
Daki ta shige, ta kwanta ta rasa abinda ke ma ta dadi.
********
BAYAN SHEKARA BIYU
"Momi ki duba hanyata in the next three weeks za mu gama bautar kasarmu".
"MashaAllah Auta! Allah shi nuna mana lafiya. In ji dai ba wa ta matsala?".
"A'a babu Momi,nagode kwarai Allah shi kara buɗi".

Kwance ta ke saman katifar da ke ɗakin ta tsirawa silin ido,ta yi zurfi cikin tunanin da ta ke. Laptop ɗinta da ke makale a caji ta janyo tare da kunnawa,bayan ta dau wasu dakiku sannan ta buɗe wa ta folder da ta sa muna MY DREAM! Hotuna ne birjik a ciki, ta buɗe ɗaya daga ciki.
Murmushi ta yi a sa'ilin da idanuwanta su ka yi tozali da kyakkyawar fuskarshi dake dauke da murmushi.
Baki ne, amma bakin shi mai kyau ne dake tattare da tsagoran hutu da jin dadi. Kyakkyawar fuskarshi da ta kyayatu da smokey eyes wadanda ke dauke da gashin gira gazar-gazar, da dagon hancinsa da ya dace da matsakaicin bakin sa da ke kewaye da saje da ya kwanta luf-luf! A saman fuskar. Kirar jikinshi kadai za ta tabbatar da isasshen namiji ne kuma kosasshe, ma'abocin motsa jiki. Yana da tsayi da kauri hakan ya kara ma shi kwarjini sosai a idon mutane.
Samir Alkali kenan! Dan kimanin shekara talatin da biyu. Dan asalin jihar Zamfara a karamar hukumar Shinkafi. Da ɗaya tal a gurin mahaifiyarshi Inna Rabi, ɗa na goma sha uku a wajen Alkali Ahmadu Sani, alkali ne a kotun karamar hukuma. Matan babanshi uku, mahaifiyarshi ce cikon ta uku.
Akwai Amina wadda su ke kira da Mama mai 'ya' ya biyar. Sai gwaggo Adama mai ya'ya bakwai.
Akwai kishi mai tsanani a tsakanin matan, hakan ya sa ba su jituwa haka ma 'ya'yansu.
Samir na da shekara bakwai Allah yai ma mahaifiyarshi cikawa. Tun daga nan ya shiga KUNCI na rayuwa, yana samun matsin lamba daga matan babanshi.
Duk yayyenshi maza basu yi zurfi a karatu ba, saboda yanayin babu da su ke fama da ita, duk suka tsunduma a harkar kasuwanci da noma.
Samir na matukar son yin karatu, hakan yasa dole yake duk wani faɗi tashi dan ya taimaki kan shi. Ya riga ya saba da wahala, shiyasa duk wuyar aiki in dai zai samu kudi na halal zai yi dan ya dogara da kan shi.
Shi ne dako, shi ne guga da wanki duk dan ya rufa ma kan shi asiri. Da kyar ya kammala makarantar sakandire ya fito da sakamako mai kyau.
Ganin be da hanyar wucewa karatu ya sa ya fara koyan sana'ar dinki. Da yake yana da hazaka cikin lokaci kankani ya iya dinkin. Gaskiya da rikon amanar shi yasa ogansu ya buɗe ma shi shago a cikin garin Gusau tare da wasu yara suna dinki, duk sati za'a basu kudin aikinsu. Duk kudin da ya samu tara su yake yi.
A haka har ya samu ya buɗe na shi shagon kan shi yana dinkin kayan ma ta da maza.
Da haka ya samu gurbin karatu a jami'ar Usman Danfodio dake Sokoto fannin Business Administration, yana dan shekara ashirin da ɗaya.
A can Sokoto yana karatunshi yana sana'ar shi ta ɗinki. Cikin ikon Allah ya samu daukaka a fannin ɗinki har yana da yara da ke ɗinki idan yana makaranta ko yaje ganin gida.
Duk da irin yanda ya taso cikin halin ko in kula daga gidansu hakan be hana shi taimakawa 'yan uwanshi ba.
Shekarar shi hudu ya kammala digirin ɗinshi ya tafi bautar kasa a garin Lagos.
A can Lagos ne ya kara gogewa da harkar ɗinki, kusa da inda yake bautar kasa akwai shagon fashion design. Da yake yasa ma ranshi sana'ar duk inda ya san zai karu zai je. Da haka ya baro garin Lagos cike da dumbin nasarori.
Dawowar shi gida ya samu cigaba sosai a shagon shi. Kwatsam yaga wa ta talla a shafin internet na INTERNATIONAL TALENT SUPPORT, da su ke nema duk wani wanda ke da basirar fashion design ya shiga gasar da za su ta hanyar tura ɗinkin da mutum ya yi tare da sunan in da yake aikin da duk wani bayani da ya shafe shi, duk wanda ya ci gasar zai sami schoolarship in da zai yi masters ɗin shi akan fashion design.
Ba tare da sanin kowa ba Samir ya shiga wannan gasar, ya dade yana nazarin dinkin da zai yi, kafin daga bisani ya dinka riga da wando na maza da yaɗin dake nuna suturar ɗan Africa.
Duk wani bayani da su ke bukata sai da ya tura tare da fatan samun nasara.
Tsayin watanni uku da tura wannan gasa, Samir ya samu sako a e-mail ɗin shi na samun nasarar da yayi ya zo na biyu cikin 'yan yankin Africa.
Birnin Trieste da ke Italy za su, in da za'a karrama su.
Murna wajen Samir ba'a magana, ya je ya samu mahaifinshi da maganar ya nuna amincewarshi tare da sa ma shi albarka.
Cikin sati daya aka yi ma shi duk wani cuku-cuku na tafiya. Sun samu tarba ta musamman a Kasar Italy in da mutumin da ya kirkiri International Talent Support' Barbara Franchin' ya karrama su.
Sun sami lambar yabo tare da kyaututukka, in da aka ba su takardar samun gurbin karatu kyauta anan Italy.
Ya dawo gida tare da dumbin alkhairi, watan shi guda a gida ya tafi Italy dan karatun shi.
Shekarar shi biyu ya kammala masters ɗin shi akan fashion design.
Dawowar shi gida Nijeriya ya bude SAA FASHION DESIGN a Lagos, in da ya ke da branch a Sokoto. Dinki su ke masu kyau da kyayatarwa wadanda aka dinka da yadikanmu na nan Africa. Kwazon Samir yasa ya shahara, ya samu award a irin su Nigerian Fashion Designers a matsayin youngest fashion designer, Mercedes Fashion Week a matsayin best African male fashion designer. Ya samu award da dama daga mabambamta kungiyoyi.
Arzikin ya bunkasa inda ya gyara ma mahaifinshi gida zuwa ginin zamani, haka ma yan uwanshi na cin gajiyarshi. Haka ma matasan dake samu a karkashinsa suna da yawa.
Ya gina tamfatsetsen gidanshi a Tudun Wada inda yake sauka idan ya zo Gusau.
*****************
Murmushi ta saki tare da kura ma system ɗin idanu, wani irin abu ke fizgarta kamar maganaɗisu. Soyayya ce da kauna wacce ba algus a cikinta ke fizgarta. Ba ta san lokacin da ta fara son Samir Alkali ba, ta tuna ranar da ta fara ganinshi a Jifatu store.
Yanzu kam ba ta san inda za ta gan shi ba, dan ta san SAA yafi karfin ajinta.

***************
Janye ta ke da akwatinta tana mai kewar garin na Bakori inda ta yi NYSC ɗin ta a Community Girls College Bakori.
Ta ji dadin zaman garin saboda mutunci da karrama bako irin na yan garin.
Mota ta hau zuwa Funtua, in da ta samu motar da za ta sada ta da garin Gusau cikin awannin biyu saboda yanayin hanya da kuma motar haya.
Iska mai dadi ta shaka ta garin Gusau. Dai-dai gefen titi motar da ta hau ta sauke ta, ta sauka tayi shatar keke napep zuwa gida.
Zaune a falon Daddy ita da su Momi.
"Muna godiya da Allah ya nuna mana wannan rana ta kammala bautar Kasar Mamana. Allah shi albarkaci karatun da ta yi ".
Su ka amsa da" Amin".

Dawowarta gida ya sa ta dukufa da sana'arta ta snacks, tunda babu aikin gwamnati. Tana taɓa zanen ta akai-akai, har ya kai telolin da su ka san ta tana saida ma su, tun kan wani style da tai kai ma Kasuna ya ma ta,ya yi ma mutane ya samu alheri sosai akan shi, tun daga nan idan yaran masu kuɗi sun kawo ma shi dinki Zainab yake kai ma wa ta zana ma shi.

Zaune take da waya a hannunta ta tsunduma duniyar gizo, ta na kan Twitter dan duk cikin social network ta fi jin dadin Twitter.
Trends din da ke yawo a Twitter ta duba in da ta ga wani hashtag an rubuta #NABACONTEST ta danna kan hashtag ɗin ta ga cikakken bayani akan NABA (Nouva Accademia Di Belle Arti) Milano.
Su suka shirya gasar zane a bangaren fashion design na matasa masu matakin karatu na digiri a ko'ina daga faɗin duniya.
Zainab bata yi kasa a gwuiwa ba wajen karanta ka'idar shiga gasar.
Falo ta fito dan ta nuna ma Momi.
"Auta idan kin ga za ki iya ki tura ma su, kila a dace".
Da Shawarar Momi ta samu kwarin gwuiwa tura zanen doguwar riga abaya, cikin kwarewa dan sai da ta natsu sannan ta zana.
Cafe ta je aka yi scanning sketch ɗin da sauran takardun shedar karatunta da shedar zama yar kasa da takardar haihuwa, tare da hotonta. Sai da ta tabbatar komi ya yi yanda ta ke so sannan ta sa aka tura ma su ta email ɗinsu.
Bayan awa arba'in da hudu (kwana biyu) ta samu sakon cewa sun ga aikinta.
*********************
"Yanzu Jidda har asa ranar auren ku da Hafeez ki kasa faɗi mun".
"wallahi kunyar ki ni ke ji Zee, kuma aure ne gashi nan yana ta tangaɗi. Na rasa gane kan Hafeez".
"Haba Jidda tun yaushe muka wuce wannan babin. Tangaɗi kamar ya?".
"Zee komi na yi ma Hafeez ban iya ba, sannan akwai halayen da ba ki san shi da su ba, Hafeez ya canza daga yanda ki ka san shi, inna yi magana yace hakanan zan yi hakuri in aure shi".
"Ya Salam! Shi Hafeez ɗin da kan shi ya ke haka?".
"shi ɗin fa,taimako ɗaya za ki mun ki shawo man kan shi".
"harda laifin ki Jidda namiji ba a nuna ma shi irin wannan zazzafar soyayyar gani zai yi idan ba shi ba ki rayuwa, ki ban number Hafeez zanyi magana da shi In Shaa Allah komi zai daidaita ".

****************
" Hafeez abinda ka ke ma Jidda ka kyauta kenan?".
"ki fahimce ni Zee, halinku ba ɗaya ba ke da Jidda, har yanzu ba gama fahimtar waye Hafeez ba, ta kasa gane mi ni ke so, mi ye ban so".
"ok na ji, amma kasan kai za ka koyar da ita ko?".
"Au! Ke koyar da ke nayi kenan?".
"Oho! Amma dai kar ka manta da alkawarin da ka daukar mun na rike Jidda da amana".
"ban manta, amma ita ma ta gyara na ta halin".
"wannan tsakanin ku ne".
Ta kashe wayarta.
Ta kai duba ga TV da ke ta magana ita kadai, Bugun zuciyarta ya karo a yayin da tayi tozali da kyakkyawar fuskar shi, ya na furta haruffa cikin natsuwa.

Ku yi hakuri ban yi posting jiya ba, na yi typing ban samu damar Sending ba, due to network problem. Ku gafarce ni.

©Indo A'i

chuchungaye.wordpress.com or wattpad @ayeesh_chuchu

DOGARO DA KAI Where stories live. Discover now