Ni Macece Part 1

183 9 0
                                    


                                         🌠🌠🌠🌠🌠🌠 01 🌠🌠🌠🌠🌠🌠

 Idan akayi la'akari da yanda take tura garuwan za'a gane cewa karfin halin da takeyi yafi karfin dake jikinta, abunda taakeyi duk dauriya ceda karfin hali. Turawa takeyi kirjinta na bugawa fit fit fit da karfi saboda gajiya amma bata fasa ba saima himma data kara. Ranar garin funtua a kanta ya kare saboda yau ba karamin layi ta tarar ba a gidan debo ruwa kuma kasancewarta mace a wajen shiyasa akaso a raina mata wayo shiyasa ta tube rigar mutumci ta ara na rashin kunya da zuciya sanan suka shafa mata lafiya. Tanaisowa gaban wani tangamemen gate ta dakata a wajen tana haki, zufa har cikin tafin hannayenta ta shiga dokawa malam habu kira akan ya bude mata gate. Ya leko da sauri dayaga ita ce sai a nan ya koma ya turo mata gate din yanda ruwan zai wuce yanata faman yi mata sannu yana sa mata albarka, ba bata lokaci ta tura har dai dai bakin kofar su ta tsayar sanan ta soma saukar da jerry cans din da suke cike taf har bakin su da ruwa tana jera su a kasa har ta saukar da dukkansu guda goma cif sanan ta shiga daukawa zuwa cikin dakin. Ummanta na zzune akan taburma a falon tana bare dafaffiyar gyada tana ci tace''Samiha na sannu da dawowa yar albarka sannu kinji'' gyada kai kawai ta dingayi har ta cika bandakin taf da ruwa, yaci guda biyar ta dawo kitchen ta juye saura hudun sanan ta tsaya tana mayar da numfashi kirjinta har rawa yake ta duba ummanta tace '' umma duk na cika ko'inna kuma akwai saura guda daya,tunda mugayen nan sun hana mu ruwan bari na ba malam habu sauran nasan zai isheshi zuwa gobe idan sun ga dama su biya kudin'' umman tace ''da kuwa kin kyauta dan kuwa na san yana bukata'' ta fito ta dauko guda dayan ta nufi dakin zamn shi, yana hangota yayi saurin tahowa ya karbeta dashi tace '' gashinan malm habu kayi maneji zuwa gobe idan an gyara kokuma idan bab idi ya dawo daga kauyen su sai ya kawo mana kasan bai dawo ba har yanzu'' ''nagode samiha, nagode ssai Allah yayi mik albarka yayi miki fifikon alkhairi yasa ki gama da duniya lafiya'' idan da sabo yaci ace ta sab da adu'an amma a kodayaushe yayi mata adu'an nan sai taji idanunta sun cicciko da hawaye domin na yanzun ma har sun soma gangarowa saboda tunawa da takeyi da mahaifinta da kasa ya dade da hadiyewa sanadiyyar shike mata ire iren wadanan adu'oin a kodayaushe koda kuwa ruwane kadai ta kawo mishi wato mafi kankantar aika sai ya fada mata hakan. Ta amsa mishi da amin sanan ta juya zataje ta dauko garuwan ta mayar wa wanda ta hayo a wajensa, zee dake zaune a cikin hut house din shakatawa ta dan daga murya yanda zata ji tace ''aikin banza kikeyi whalalliya kawai sai fi'ili da son neman suna kuma a haka zaki kare da yin aiyukan maza'' bata tanka mata ba saida ta dauko garuwan tadan turo shi kadan alamar zata fice sai ta tsaya a daidai inda itama zee zata iya hangota itama ta daga muryarta yanda bama ita zee din kadai ba harda uwartan zasu jita tace''idan ba tsoro ba wata shegiya yar shegiya zuri'ar shegu tazo gabana ta mun maganar baza kokuma ta daga mun yatsa idan ban goga mata hakoranta dana uwar tata a interlog din gidan nan ba shegiya uwata ta haifoni. Nayi rugu rugu da ita son raina yanda sai anje anyi jinyarta a baban asibiti kamar na bara'', tayi gaba abunta bata ko waiwayeta ba, itama zee kwafa tayi tana dan gunguninta ta wuce cikin gida. Gidan abinci ta wuce ta karbo musu abincin rana, saboda wahalar ruwa tunda asuba ta fito gida neman ruwa ba ita ta dawo ba sai bayan azahar saboda kada ta bar ummanta da yunwa gashi batada kafafu sai ta siyo gyada ta aika yaro ya kawo mata akan tayi hakuri dashi har ta dawo ta nemo musu abunda zasu ci. Ta dawo suka ci ta kwashe kwanukan da sukayi amfani dashi ta dauraye ta ajiye kowanne a mazaunin shi sanan ta kai musu ruwan wanka bayi, ta taya ummanta ccire kayan jikinta sanan ta kaita bayi tayi mata wanka ta rikota da kyar kaman yanda ta saba tana dingisawa ta zaunar da ita a bakin gado, ta shafa mata mai ta sanya mata kaya sanan itama taje tayi wankarata tazo ta shirya ta juye ruwan zafin dake tafasaa heater a flask din tea ta ajiye a gefen gado ta dauko mata kofi da dukkan abunda zata bukata ta ajiye mata agefenta sana tace ''to umma ni na tafi wajen aiki, ga kayan tea nan idan kinji yunwa kuma ban dawo da sauri ba sai kiyi amfani dashi har na dawo. kiyi hakuri kinji umma'' umman tace ''babu damuwa ya'ta kije kawai saikin dawo, Allah ya tsare ki kula da kanki kinji'' ''ba komi umma ki yarda dani kinji'' ta fito ta kullo kofan ta waje dama ta sakala mukullin a jikin wani tsuma ta daure a hanunta,ta kunce kekenta daga mazaunin sa ta dale sanan ta wuce abunta malam habu yace a dawo lafiya..................................................................................................................................................    

NI MACECEWhere stories live. Discover now