NI MACECE 12
Ranar da taje wa alh saminu da maganar sai yama shashantar da maganar a matsayin wasa ''mace da kanikanci? imposible!'' da ta matsa mishi akan eh taji ta gani a hakan take so sai yace to yaji taje gida zaiyi nazari, anan ya watsar da zancen nata. Sati daya shiru ta sake komawa mishi nan ma yace yana dai kan nazari, a takaice dai zuwanta hudu amma duk bai gama nazarin tashi ba tace shikenan idan yasan wata ai bai san wata ba, a na biyar dinne tayi mashi zama yan bori a kasa ta sakar mai kuka a office dinshi tace Allah bazata tafi koi'inna ba sai ya gama dukanin nazarin da zaiyi ya bata sakamakon shi, yace ''samiha, nifa banga dalilin da zakije wani aikin kanikanci ba kina mace, shekarunki fa ko 16 basu kai ba, banda ma wanan me kika rasa eyeh! idan kudi kike bukata fada mun ko nawa ne zan baki don na yarda dake fiye da ya'yan cikina amma maganar kanikanci kima cire shi a gefe ki jngine don babu shi'', tayi tayi dashi ama yace shi sam baima san zancen ba sai ta kyale shi. Washe gari daya je duba su kafin ya wuce kawa sai ya ganta ta zage haikan haikan kanikanci zatayi, a nan ya sallama mata don lamari ya zarce tunani shi yace ai idan mutum yace zai hadiye gatari sai ka sakar mai kotar don yaji dadin kwana a tsaye. Abu kaman wasa karamar magana ta zama babba, samiha ta soma aikin kanikan haikan haikan, abokan aikinta wato manya kamanta salisu, sha'aban, bashir da isma'il tuni suka saba da ita harda sauran kananan masu koyon aikin saboda zagewar da takeyi sanan sam bata wasa da aikintaa, saka kai tayi ssai har ta saba. Suma da farko abun ya zamo musu wasa amma da sukaga babu wasa a lamarinta sai kowanne ya soma koya mata feild of perfection dinshi, gata da saurin shiga rai saboda rashi girman kanta da kuma daraja na gaba da ita da takeyi don dukkansu tana basu respect dinsu daidai su, suna wasa amma sama sama bata barin gonar wani ya wuce iri saboda alqawarin data ma ummanta yana nan daram dam dam a kanta sanan bata dauki sanin da tama ogansu a matsayin komi ba hasalima bata taba sanar dasu ba, shi da kanshi yazo ya fada musu bayan yayi musu gargadi mai tsanani akan su kiyayeta, ba rashin wadata bane ya kawota ba saboda haka kada wani a cikinsu yayi gigin raina ta domin ita ya'ce a wajen shi akasin haka na nufin yin waje road da koma wanene daga nan suka lakaba mata suna''mai karfi''. Bayan sati biyu ranar asabar kasancewar weekend tana tafiya tun safe,ta dawo gida da rana a gajiye tazo kawowa ummanta abincin rana don ba laifi yanzu kam tana dan samu kasancewarta sabon star domin kowa yaji al'amarin sai yazo don kawai ya kashe kwarkwatar idanunsa sanan ayi mata jinjina da kyauta mai tsoka gashi hnunta yafi kwari a ta fannin engine sanan ta saka kanta ssai akan aikin, ga cika alqawari muddin ta hanunta kabi sanan bata tsananta kudi ssai akai tunda ita bayi take saboda tanada wani dogon buri akanshi tunda bata rasa gida da kuma kudin makaranta ba ah ah tanayi ne saboda kawai ta samu na kudin asibitin mamanta sanan ta samu na kashewa. Tana turo gate din me zata gani? Mahaifiyarta ta gani zaune a tsakar gida zee da kanwar mamanta sun zagayeta sunata surfa mata uban zagi data kasa gane na menene ga hawaye na ta bin kuncin ta, wani bacin rai ne yayi mta dirar mikiya a zuciya, ta nufesu tana maifadan '' keh! zee me mahaifiyata ta muku kuka janyota tun daga daki kuka kawota nan kuna zaginta?'', kanwar jamila mai suna karima tace '' ai komi ma tayi tunda har tayi mistake din auren babanku harta haifo ki tana mai hada kishin ya'ya da yayata. Wai kamar ki har kin isa ki soma zuwa wajen sana'a babu izini don tsabagen samun guri ko?'' zee ta cafe ''sana'a ko karuwanci amma dai anji haushi wai mace da kanikanci? kuma wai har ke a matsayinki na mahaifiyarta kika kasa tsawatar mata don dadin da take kawowa miki kuke ci ko?'' tana magana tana mai dungurar wa umma da kai. Da zuciya ta debe ta, a guje tayi kofar dakinsu ta rarumo sandar da suke tokare dakin dashi dadare saboda kada wani abu ya shiga kasan tayi kansu dashi, ita kanwar nata kasancewarta matsoraciya ai a guje ta arta shashin su zee ko ta tsaya kkam a wajen a zatonta kuri kawai takeyi, tayo kanta da bugu ba ji ba gani ji kake tim tititim, umma naa dakatar da ita amma inaa...... tayi nisa bata ji kira. Ihunta ne ya ankarar dasu a cikin gidan suka fito a guje kawo mayata dauki suna dosota ta biyo su dashi suma haba ai sai hanyar gate babu ko waiwayo suka fice gate din ita kuma ta dawo tana nishi, a lokacin ta tuno zee da take nishi a tsakar gida ta nufota duk ta jigata ko motsi ta kasa yi abunaka da yar gatan da ba'a duka ta nuno ta da yatsa '' don uban wani ya sake koda kuskuren taba mun ummata ya gani idan banyi azancin aika dashi barahu ba, banza kawai, shasha sha, baki ji junya ba wai ke a hakanki? duk abunda zakuyi bazku tsaya dashi a kaina ba sai kun hadada uwata ko? to na sake kama wani wlh gamuwar mu bazatayi kyau ba'' ta tsatsar da yawu a gefenta sanan tayi tsaki '' wlh da wani bare be sai na kusan raba shi da numfashi sa a hakan ma na ragar mikine saboda akwai dangantakar jini mai kaurin zaren dinki a tsakanin mu saboda haka kikiyayeni'' tana kaiwa aya ta juya ta taimakawa ummanata suka shiga cikin gida.
YOU ARE READING
NI MACECE
AdventureIts about an orphan girl who lost her father at a young age nd had to fend fo herself and her paralysed mother. Just read and enjoy..