Ni Macece Part 11

78 3 0
                                    


                  NI MACECE 11


A ranar da hutun shi ya kare ya koma a daren ranar ta sake kamota tace '' wato burin keda uwarki ku hadani da dana ko? to wallahi baki isa ba sanan wahalarki yanzu ya soma armashi a wajena muddin bazaki kwashe wanan tsumokaran naki dana uwarki ku bar gidan nan ba'' almakacinta sabuwa data siya ta dauko ta soma yanka mata suman kanta. Ko motsi batayi ba bare ma tayi kokarin hanata hasalima gyara zama tayi saboda dalilai biyu na daya koda ta hanata bazata hanu ba saima karin dukan azaban da zata sha, na biyu kuma bata kaunar taga gashin kanto ko kitso aka mata a gidan su alqassim sai ta zuba mata kasa a kan tace ta daura dankwali akan sai ta wuni a haka sanan ta kwaba toka akan tace ta kuskura ta wanke sai ta yanyanka ta to gashin duk ya yamutse dakyar idan ma babu kwarkwata akan gashi dama mai tsantsi, amosari garke guda ke kan ga uban kaikayi da yake mata so askewar tamkar samun sauki ne a gareta tunda ta rabu da wahalar gashin. Ta kama kyakyattawa tass harda ji mata rauni akan tayi kasancewarta mai fata mai laushi na kai, ta hankadeta bayan ta gama '' kizo ki tattare na nan ki share kiyi mopping dinshi tass kada naga suma koda ko dan kan kani ne a nan kokuma jikin ki ya gaya miki da daren nan, gobe ma idan kinso ki kara hadani da dana kiga next abunda zan miki sai ma yafi wanan yajin'', tana hawaye ta cika umarninta sana ta fice daga dakin. Ta shigo ta tarar da ummanta batayi barci ba sai famn rarraba idanu take taga inda zata bullo, tayi mata sassanyar murmushi domin kawar da damuwar ta tace '' umma karfe biyun dare amma bakiyi barci ba?'' ta yafitota da hannu '' ya zanyi barci samiha bayan bansan me ake miki a chan ba, fada mun abunda ya faru'' ta riko hannunta ''kome ma ya faru amma kisani umma tunda muna numfashi in shaa Allah komi zaiyi sauki watarana, umma bazan taba bari ki tozarta ba koma menene zanyi don kawai na ganki cikin rufin asiri so karki damu, abunda ta mun ita a ganinta ta cuceni ne bata san mafita ta samar mun ba, yanzu dai ina so ki kwanta muyi barci kinsan anjima inda aiki'' ba tare data kulata ba ta gyara mata kwanciya ta shiga bandaki kasancewar ruwan da dumi saida ta wake suman jikinta tsaf ta fito ta saka kaya cikin nishadi domin jin har wani iska iska take ji a cikin kai a zuciyarta tace ''Alhmdlh! daga yau nayi bankwana da soshe soshen kai, Allah nagode maka daka kawo mun mafita cikin sanyi'' sanan tabi lafiyar gado bayan da ta shafe su da aduo'i saidai muce asuba ta gari samiha. Haka rayuwarsu ta cigaba da gudana har ta rubuta jarrabawarta na shiga ss2 da ikon Allah kuma bata taba kuskure ba a makarantar shiyasa tazama abar tutiya a gare su ta zama tauraruwa mai haskaka su abunda ke konawa jamila da yarta zee rai kenan amma banda abun alfaharinta kuma yayan ta Abduljabbar. Tana rubuta final yr exams papers dinta na ss2 zuwa ss3 Allah yayiwa Abduljabbar rasuwa. Kukan da samiha tayi ko mahaifiyarshi batayi kwatankwacin shi ba, sau hudu tana suma ana farfado da ita saboda firgita tayi ba na wasa ba, da kyar mahaifiyarta ta shawo kan hankalinta da taimakon rubutun da take bata sanan ta samu sassauci a game da rayuwrta. Idon abdul rigakafi ce a gare ta gamida mahaifiyar shi amma yanzu tunda kasa ya rufe shi sai abun nema ya karu, wasu lokutan da dama sai su wuni babu komi a cikin su gashi samiha ko kwai bata iya dafawa ba. Lokacin da babanta ke nan a raye saidai ta hau kan kitchen cabinets din tana tayata hira kokuma ta yanka na yankawa, ta miko na mikowa ballantana tace zata sato daga store din main house din ta girka musu. Abun duniya duk ya isheta, idan itace to zata iya wuni churr bata ci komi ba don ita ba ma'abociyar ciye ciye bace amma ummata itace matsalarta. Tayi nazari iya nazari amma ta kasa samo mafita domin dole saida jari zata soma sana'a to a ina zata samu kuma wacce sana'a ce zatayi wanda bazai kawo mata mishkila ba a wajen maman zee? ranar da abun ya ishe ta tace ''umma dan Allah ki saurareni inaso muyi wani maganar fahimta ne dake'' ta karkatar da ganta zuwa ga kallon fuskar ta '' ina jinki samiha na'' taja gauron numfashi sanan tace ''ina so na soma aiki a garejin baban kassim'' alamar mamaki suka bayyana a fuskar ummanta tace ''gareji? samiha gareji fa kika ce?'' ''umma gareji nakenufi, bawai mistake nayi ba'' tayi shiru na wani dan lokaci sanan tace '' wanan al'amarin da rikitarwa yake, kin taba ji ko ganin mace tayi kanikanci? sanan banda haka shi baban kassim din me zaki ce mishi don ya amince kiyi aikin kanikanci?'' ta riko hannunta domin ta wanan hanyar ne fastest way to reach her heart tace '' umma na uncle da sauki, ko kuka na mishi zai amnce yanda bai kaunar ganin hawaye a idanuna dinnan. Zan ce mishi aikin automobile engineering zanyi a jami'a shiyasa nakeso na soma training tun yanzu don nan gaba kada ya bani wuya'' shiru kuma ta sakeyi '' pls umma, ki taimakeni ki amince kuma na iki alqawarin bazan taba baki kunya ba plssss'' ta karkatar da kanta gefe domin sakonta yaji dadin shiga jikin umanta, tayi ajiyar zuciya '' ina mutukar kaunar farincikinki yake ya''ta, amma cudanya da maza a wanan zamanin bafa karamin batu bane saboda wasu lokutan yana iya zama hatsari ga ya'mace, bazan hanaki ba saboda baki taba bani kunya ba sanan kinada naki burin saboda haka na amince amma kiyi kokarin kulawa da kyau dan wanan zamanin ya lalace'' cikin murmushin murna tace ''na miki alqawari i wnt eva give u d reason to cry, ki sa mun albara kawai'' ta fada tana mai kwanciy akan cinyanta, ta shafo kanta tana mai cewa '' a kullum cikinsa kike domin daga fitowar rana har saukar sa cikin saka miki shi nake, Allah yayiwa samiha na albarka'' ''amiin umma''.

NI MACECEWhere stories live. Discover now