🌠🌠🌠🌠🌠🌠🌠NI MACECE 3🌠🌠🌠🌠🌠🌠
Taja gauron numfashi ''aure fa abba'' ''eh daidai kunnuwanki suka ji aure nace.. Ai tunda naga kinyi kicin kicin da fuska nasan bazaki amince da batuna ba tunda ba tun yau muka soma maganar karatu dake ba kuma bazan iya ajiyeki a gabana haka ina kallo ba bayan amana kike a wajena saboda haka kizaba daya ki dauka a cikinsu ina sauraronki''. Gabanta bai daina faduwa ba, babu abunda ke fadowa a ranta sai ''uwata! uwata! uwata! ina zankai uwata? wa zai kula mun da uwata kamar yanda ni nake kulawa da ita? ai akan auren ma ai gwara karatun amma waye zai cigaba da fita neman kudin da zai cigaba da kula da ita? abba na kokari amma bazai iya daukan nauyinta ba don jini jini ne sana ga iyalan shi, wa zai lura mun da ita idan bana kusa da ita? shin menene mafita?. shiru kawai tayi mishi saboda ita a rayuwa bata iya wa babba musu ba koda ranta baya so haka zatayi shiru kawai tana saurae sai hawaye yanda koma wanene zai fahimmce cewa its a very difficult situation. Ganin tana hawaye sai yace'' asha! asha! hawaye kike saboda maganar danayi? haba samiha, nifa bazan tabayi miki auren dole ba hasalima bazan taba son abunda zai bata iki rai ba amma cigabanki nakeso shiyas anake kwadaita miki makaranta domin daukanki nake tamkar ya'ta ta cikina, mahaifinki bashida buri saina karatunki har ya rasu saboda kwanyarki mai saurin daukan abu ne da kuma saurin fahimta to meyasa kike neman dakushe tarin basirar da Allah swt ya baki?'' tace ''abba dan Allah kay hakuri saboda bana musu da kai bana ma so na koya amma ko daya a cikinsu ban shirya yi ba, ka kyaleni da wanan aikin da nakeyi zuwa nan gaba tukunna dan Allah abba'' kallonta kawai yakeyi yama rasa abunda zai fada mata, hawayenta na kashe mishi jiki domin gani yake duk ranar data zubar da hawaye to na maraici ne saboda banda mutuwa mai tada zaune tsaye to da a yanzu ana iya kirgenta a daya zuwa biyun ya'ya masu gata bama a garin funtua ba kadai har a duk fadin katsina. Yayi ajiyar zuciya sanan yace shikenan samiha tunda abunda kike so kenan na hakura da dukkansu amma a kodayaushe kikashirya ni mai bin bayan ki ne saboda ke ya'ce a gareni, tashi ki wuce'' ta share hawayenta tana mai hamdala a cikin zuciyarta dayasa ya fahimceta cikin ruwn sanyi ba tare da rayuka sun baci ba, saboda a rayuwarta batada burin kowa sai na mahaifiyarta domin babu mai iya jure dawainiya da ita kamar yanda ita takeyi. Tayi mishi godiya ta wuce cikin garejin, isma'il da sha'aban ta tarar akan wata mota suna gyara, sha'aban yace ''mai karfi ya akayine kika makara ko kin soma koyana african time ne?'' tayi dan karamin tsaki '' aiyukan gida ne suka sha mun ai gashi abba ma na neman ya kara mun tension'' salisu daya karaso yana jinsu yace 'me kua ya gaya miki?'' '' tun maganar karatun nan da mukayi dashine fa ya sake dauko mun, to wai dana ki amincewa shine wai nayi aure kawai'' ido waje salisu yace ''aure kuma? to ke wani amsa kika bashi?'' ''ai ba amsa sai kuka, da kanshi ya hakura ya zuba mun ido'' isma'il yace '' to mai karfi meyasa bazaki yarda da koda jami'ar bane wai? kinfa cika rigima bayan kinsan u dont fit in here sai karrambanin tsiya'' ta harareshi '' to naki na fit din, naje jami'a na kai ummana ina bayan kasan yanda nake da ita ga jikinta baya bada notice kafin ya tashi idan ina lecture ta kirani sai na kyaleta ta mutu kenan? chapdi! saidai ayi asarar kudin makarantar domin uwata ta fiye mun komi so kama bar maganar nan kawai don ba option baneits a decision'' tayi wucewarta zuwa office din da aka ware mata ta chanja kayanjikinta zuwa wani brown overall irin na bakanikai banbancin nata da nasu shine kala don nata brown nasu kuma blue, ta dora karamin hijab dinta akai shima brown daidai kafadarta tayi maza ta fito ta kama aiki saboda a rayuwarta bata kaunar ta ganta zaune waje daya shiru a ganinta malalaci ne kadai ke haka wanda baisan darajar lokuta ba ...............................................................................................................
YOU ARE READING
NI MACECE
AdventureIts about an orphan girl who lost her father at a young age nd had to fend fo herself and her paralysed mother. Just read and enjoy..