Ni Macece Part 2

79 4 0
                                    


                                                   🌠🌠🌠🌠🌠🌠 2 🌠🌠🌠🌠🌠🌠

Tuka kekenta takeyi a cikn nishadi saboda a rayuwa matsalarta bai wuce dayaba zuwa biyu amma muddin cikin ummanta a koshe yake to duk matsalolin da zasu biyo baya masu sauki ne. Akofar wani gida ta tsaya ta jinginat da keken ta kulle da makulli yanda ba mai iya tukawa sanan ta kutsa kanta ciki da sallama, a tsakar gida ta tarar da ita tana wanke wanke ta durkusa har kasa ta gaishe ta matar tace ''samiha barkanki da zuwa,tun dazu naketa zuba ido ko zanganki amma shiru ko lafiya'' ''maman khalid wlh lafiya amma ba lau ba , tunda asuba na fita neman ruwa ba nina dawo ba sai bayan azahar a samu wanda na kawo gida yau ko karyawa banyi ba sai kusan karfe biyu'' ta rike haba''haba dai samiha, duk ruwan gidan ku amma kice mun babu ruwa samiha wani ruwan kuma ko ba famfo kike magana ba'' ta dan yamutsa fuska '' shifa, ba'ayi biyan kudin gyara bane ai bare a gyara, ni sauri ma nake dama lekowa nayi na sanar dake banyi zobo d kunun ayan ba sai gobe in shaa Allah kadi kiyita zuba ido kiji shiru'' '' shikenan nima abun ya dameni don baki cika makara a kawo shi ba, Allah ya kaimu to idan kinje ki gaida mamanki'' ta juya '' zata ji'' ta fice ta dau hanyar wajen aikinta. Tana idowa daidai kofar garejin ta sauko dga keken ta soma turawa a hannu har ta shiga,tana hango alh saminu akan benci yana amsa waya ta sha jinin jikinta sabda tasan sai ya tuhumeta akan dalilin makararta gashi ita ba gwana bane ta fannin kary. Har kasa ta durkusa ta gaishe shi, katse wayar yayi yana amsa mata murmushi murmushi akan fuskar shi''ya'ta kin wuni lfya'' ''lfya kalau abba'' ''madallah, yauwa garin har yau kika makara kamar haka ba kamar lokutan da kika saba isowa ba'' saida tayi dan jim sanan tace'' ruwa na tafi nemowa tunda sauba a garuwa sai dazu na samu saboda layin dayayi yawa'' baki bude yaketa kallonta dama tasan sai anyi hakan shiyasa ta sake gyara tsungunen ta ''samiha garuwa fa kikace kuma a gidan ruwa? ina mai ruwan da nake biyan shi yna kawo muku har gidan tun bayan da kikace mun tap dinku ya lalace?'' ta hadiye yawu da kyar ''yaje ganin gida ne bai dawo ba kuma na gidan ya kare ne babu koda na abinci shiyasa na fita nema'' ya girgiza kanshi cikin takaicin abinda ta fada ''yanzu samiha nan da gidana bazaki taho na saka almajirai su kawo muku dag gidana ba shine kika gwammaci ki tafi da kanki har gidan ruwa da kuma garuwa? haba samiha har nawa kike da zaki iya tura garuwa saboda Allah ke a ganinki kin kyauta mun tsakaninki da Allah?'' kanta a kasa ta soma bashi hakuri ''kayi hakuri abba nasan nayi kuskure amma a lokacin sai ya dinga mun kaman baka gida ne shiyasa banje ba'' ya sake tubure fuska ''idan bana gida ke baki isa ba kenan kije kice musu su baki ruwan ba kenan injini kokum kikira ni a waya'' ta rasa tudun dafawa ''abba dan Allah ka gafarceni nayi kuskure kayi hakuri in shaa ALLAH bazan sake ba'' saidaa yadan ja numfashi sana yace '' shikenan tunda kinyi nadama ya wuce amma kada ki sake ki maimaita hakan. ya ummanki da jiki nata?'' ''tana nan lafiya kuma jikinta Alhmdlh da sauki'' ''madallah, to ya batun maganar karatu da mukayi dake kikace mun zakiyi nazari a kai'' nan da nan annurin fuskarta ya gushe ita harta ma manta da maganar da sukayi din don dat tuna data hango shi da bata karaso ba saita jira har ya tafi amma sanin kanta ne muddin ya jira bai ganta ba hankalinshi tashi zaiyi ''nifa abba....'' sai kuma tayi shiru'' ehen.... cigaba mana kefa mene?'' ''nidai abba dan Allah a hakura kawai da maganar karatun nan dan Allah,babu abunda nida umma muka nema muka rasa duk ka dau dawainiyar mu. dan Allah kayi hakuri a bar maganar nan'' ya kalleta a tsanake'' nifa na rasa irin ki fa samiha, gaki da kwakwalwa da basira meyasa bakison karatun? nifa ban taba ganin wanda ake binta da admission din jami'a take gudun shi ba sai ke. inada buri ssai akan karatunki samiha saboda banaso na banbantaki da ya'yan cikina shiyasa na dage akan kiyi karatunnan'' ''nidai abba kayi dai hakuri a bar maganar jami'an nan kwata kwata wllh banson shi dan Allah abba ka mun uzuri kuma ka gafarceni idan na bata maka rai'' ya dade yna kallonta sanan yace ''to kiyi maza ki fito da miji tunda bakya son jami'an'' ta dago kanta a dan razane don bata zata option din da zai kawo ba kenan..........

  

NI MACECEWhere stories live. Discover now