Ni Macece Part 4

66 3 0
                                    


                                                            🌠🌠🌠🌠🌠     NI MACECE 4🌠🌠🌠🌠

WACECE SAMIHA? BARI MU GANI

Alh Abdulazeez Salihu haifafen dan garin shinkafi ne a garin katsina iyaye da kakanni. su uku ne a wajen iyayen shi kuma shine babba sai habiba sanan fatima auta. Dukkansu suna aure a cikin garin katsina da yayansu Tunda ya gama jamia ya fada a kasuwanci gadan gadan kuma cikin hukuncin ubangiji Allah ya albarkace harkartashi lokaci guda aka soma damawa dashi a cikin manyan yan kasuwan garin kt. Ya gina wa iyayenshi gidanna gani a fada agarin kt ya mayar dasu,ya tabbatar basu nemi wani abu sun rasa ba. Kannenshi duk shi ya aurar dasu ya dauke dawainiyar aurensu karankap yanda naira biyar din iyaye shi bazaiyi ciwon kai ba. Ya gina lafiyayyen gida a cikin garin funtua saboda shagunan shi sunfi yawa a cikin garin sanan yanayin garin yafi cikin kt sanyi da dadin ni'ima sanan bai cika son zama a wajen iyayen shi ba saboda yawan uzuzzura mishi da sukeyi akan maganar aure wanda shi a ganin shi a lokacin bacin lokacine saboda yawancin yanmatan da suke bibiyar shi saboda arzikin shine kokuma tashen shi. Ya fito wurin aiki tsautsayi yasa shi buge wata yar buzuwa da take ta faman bara da motar shi, tuni ya wuce da ita asibiti. HankLinshi duk ya tashi yar'uwar ta sai faman kuka take tayi da kyar akashawo kan lamarin. Likita ya dubata banda targade da tayi a kafa sai dan kurjewar da tayi a gefen cikinata haka ya biya kudin asibiti ya wuce dasu gidan su,kallo daya zakayi wa dakin ka fahimce suna fama da wahala. Ya dube yar'uwar yace''ku jirani barin naje na nemo mai gyar ya gyara mata idan ma zamu kaitane sai muje'' tace ''toh''. Aka dauko mai gyara ya rike ta duk ta hada zufa saboda ciwo donma tanda dauriya batayi kuka ba ta cusa dan kwalinta a bakinta don kada sautin ihunta ya fito. ya sallame me gyara sanan ya dawo ya tarar da kanwar tana mata fifita tana nishi sama sama duk tausayinsu ya mamaye shi ya dube kanwar ''uhm,. yama sunan naku?'' kanwar tace ''sunana salma, itakuma asiya'' ya jinjina kai ''to ya kamata dai ki dan duba mata wani abu da zata sak a cikin cikinta don ta samu ta hadiye magani'' amma daya sake nazari sai yace ''kodashike jirani ma ina zuwa ''ya fice yayi musu shopping din light foods n provisions dasu quaker oats nd co ya kawo musu. Yayar baki bude kawai tayi tana kallo ana shigar dasu dakin................................................................................................................................................... Saida ya gama ajiyesu saan tace ''haba bawan Allah ai dawainiyar sai yayi yawa, ka bugeni amma tsoron Allah bai barka ka gudu ba ka biya mun kudin asibiti sanan kuma yanzu harda kayan abinci?'' yayi murmushi mai kayatawa '' kada ki damu ai ni na saka kaina so ki bar damun kanki'' ya dubi agogon hanunshi ya danja tsaki ya dubeta ''inada meeting dana makara kuma na bar dumbin mutane suna jirana bari na tafi zan dawo gobe da yardar Allah naga jikin naki, ki huta lafiya'' ''na gode kuma Allah ya kaimu'' a daidai bakin kufan dakin ya ajiye mata rafar kudi na dari biyu guda biyu sanan yayi saurin ficewa kada su mayar mishi dashi, yay wa kanwarta sallama atsakar gida tanata faman hura icce zata daura musu abinci tayi mishi godiya sanan ya fice. A ranar dai kawai dai saboda barci ya kasance barawo shiyasa kawai ya samu damar sace shi amm tunanin baiwar Allanan ya hanashi sakat. Yayi sallama ya tarar da kanwarta salma tana wanke wanke ta gaishe shi ya amsa mata sanan tayi mishi jagora cikin dakin su, tayi mishi marraba ya zauna suka gaisa ya tambayeta jikinta tace da sauki sana sukayi shiru ya dubi salma yace ''yan'mata ya akayi bakije makaranta ba yau ko duk jikin sister din nakin ne sila?'' ta kalleshi ta kalli yar'uwar nata sanan ta sunne kanta tayi shiru, sai ya dawo da hankalinshi wajen asiya yace ''to tunda nayi mata tambaya ta kalleki tayi shiru, watakila sai ke ki ban amsa'' tayi murmushi mai ciwo sana tace ''dukkanmu saina arabiya na boko iyakacin mu praimary shima din a gdan marayu mukayi shi kafin mu fito sabod yanayn rashi, mu biyu ne kadai a wajenn muka asance buzaye sai naga kaman bamu dace ba a wajen shiyasa na daukota na mayar da ita yar'uwata saboda dukkanmu bamu san kowa ba amman Alhmdlh koda da rana daya Allabai taba hanamu da ci ko sha ba saidai abunda bamu rasa ba'' ya zura mata idanunshi kawai tausayin su ke dawainiya dashi a zuciya yace '' yanzu rayuwa kuke ku biyu a gidan nan? tayaya har kuke rayuwa kuci ku sha duk kuma ku biya haya'' '' aikatau mukeyi dukkanmu mu hada albashin mu, a hanun matar da muka fada da muka fito ita ta rike mu tsakaninta da Allah har Allah yayi mata rasuwa to danta ne bayan anyi rabon gado yaji tausayin mu ya bar mana gidan yace babu abunda zaiyi dashi mu zauna har rayuwa tayi man sauki, barar da kaga inayi a titi saboda korar mu da akayi a gidan da muke aikine, anyi wa kanwata kazafi shiasa na kasa jurewa shiyasa muka bar msu gidan su, yanzu abun kaiwa baki na neman fin karfin mu'' ya girgiza kanshi duk jikinshi yyi sanyi, yayi shuru yana nazari sanan yace ''yanzu idan nace ina sonki zan aureki mu zauna harda kanwarki tsakani daa Allah zaki amince?''..........................................................................................................................................

NI MACECEWhere stories live. Discover now