Ni Macece Part 5

72 3 0
                                    


                                                           🌠🌠🌠🌠🌠  NI MACECE. 5🌠🌠🌠🌠🌠


...Cikin mamaki dukkansu suka kalleshi sai tace'' amman wasa kake ko'' ''maganata har cikin zuciyata take zaki aureni/'' tayi murmushin takaici ''idan taimakona kake sonyi kawai ka taimakeni amma karya da kalaman so bafa karamin abu bane'' ''nifa wlh har cikin raina naji ina kaunar ki kuma nake son aurenki, ki duba cikin idanuna kinga alamun wasa a tattare dani? da zallan taimakone ai akwai hanyoyi dayawa da zan iya taimaki mik dashi ba saina kawo batun aure ba amma sonkin da na kamu dashi farat daya shine sanadin dayasa nakeso nayi rayuwa ta din din din dake. Abunda nake ji a game dake wlh Allah daya kenan ban tabajin makamacin irin shi akan wata ya'mace ba sai akanki don banma taba soyayya ba tunda nake saidai a soni saboda haka kin amnce zaki aure ni?'' shiru tayi jikinta yayi sanyi alamar tana nazarin maganganunshi a cikin kwakwalwarta, salma a hankali ta mike ta bar musu dakin domin maganar ya girme ta,cikin muryar karaya tace '' naji batunka, yanzu ace na amince zan aureka kai a ganinka mai kwalisa iyaynka zasu barka ka aureni a wanan halin da nake ciki?'' yayi dan jim sanan yace ''ke musulma ce dats for starters sana ina sonki wana kadai ya isa mahaifina ya amince da bukatata amma bazanyi miki karya ba matsalar ta fanin mahaifiyata ne,saboda akwai wacce ta dade tana so na aura ina ki amma kar ki damu nidai bukatata ke daikawai naki amincewa ne kawai ki bar mun matsalar gidan mu naje na ji dashi'' ta ja gauron numfashi sna tace '' shikenan na amince zan aureka kaje kayi maganin matsalar gidan ku'' yayi murmushi sana yayi hamdala ''nagode asiya! nagode ssai, yanzu bari naje da zafi zafi nasan inda dare yayi mana'' suka rabu cikin farinciki. Tunda suka gaisa yayi shiru ya kasa magana saboda fargaba, tace ''yaya dai dan baba daga alamu akwai magana kuma mai nauyi a gabanka'' ya hadiya da kayar ya kalleta ''umma kun dade kunata so nayi aure ko?'' ta gyada kai '' hakane, da matsala ne" '' eh to na samu ne shine nazo na sanar dake'' ta soma washe hakora da nuna tsananin fafrin cikinta ga labarin daya kawo mata'' ai tund ka shigo naga kanata wani nuku nuku nasan da walakin, kai! nayi mutukar farin ciki dukda naso ka auri nana amma bata baci ba sai ta hakura, yanzu a ina yarinyar take kuma yar wani unguwa ce/'' ya soma sosa keyar sa saboda a wajen matar ta kade mijin wato inda matsalar kenan '' uhm.. uh... wai dama a funtua take, marainiya ce ita da kanwarta kuma buzuwa''. Wani kallon data watsa mishi saida yaji hantar cikin shi ta kada dama gashi baima karya ba kafin ya fito hakan ne ya taimakawa cikin ya kara hautsinewa, tace ''mene kce? ban jika ba dan mamaita naji'' abunda yake tsoro shike shirin faruwa ''umma ina sonta dan Allah kada kiki amincewa da bukatata wallahi umma suna cikin matsanacin rayuwa'' tayi mishi dakuwa '' ungo kaji gidan ku. kana haukane kokuma giyar arzikin da kake shane ke neman yaudarar ka? har ka isa kayi tattaki kazo gareni tafe da wadanan maganganun/ ah ah ba matsi ba Allah yasa ma a cikin rami suke rayuwa maganar banza kawai''. Ya sulale kasa ya durkusa mata akan gwiwoowinshi biyu yace ''pls umma kada ki mun haka, wanan shine karon farko dana fara jin wani abu a zuciyata akan wata wanan kuma shine karon farko dana shirya rayuwa da wata umma kada ki watsa mun kasa a idanuna, wallahi da zaki saurareni da sai na kawo miki ita har nan don ku gana wallahi am serious u'll get to like her'' ta harareshi gami da yin kwafa ''wa? ka kawota ina? chapdi ! to bana bukata kuma saurareni nan idan har nema izini nane ya kawo ka nan to ban amince ba kuma bada yawuna ba sanan muddin kana son zaman lafiyarka dani to kuwa kada ka kuskura ka sake kawo mun zancenta, nadai gaya maka'' ta mike tayi ficewarta daki ta barshi nan zaune a kasa zufa keta faman tsartsafowa daga ta koinna a jikinshi saboda tashin hankali, ranshi a jagule ya mike ya fice daga gidan gabaki daya daman wanan shine plan A tunda baiyi aiki ba zai koma plan B .........................................................................................................................................................

NI MACECEWhere stories live. Discover now