Ni Macece Part 10

55 3 0
                                    


                                      NI MACECE 10


Tana falonta tana kallon wani arab film, yana shigowa ta kalleshi sama da kasa sanan ta tabe baki tace ''oh! ashe dagaske ne ka dawo ka tafi da wanchan tsinanniyar yarinyar asibiti tun kafin ma ka shigo ka gaisheni a ganinka ka kyauta? kumafa harda kwana ko waya ma baka buga mun ba yaushe kuma muka soma yar' haka da kai?" Wani malalacin kallo ya wurga mata a zuciyarshi yana mai aiyanawa inama inama maman samiha ita ta haife shi '' a lokuta da dama mummy idan kika aikata wadansu abubuwa sai na dinga tunanin anya kuwa kinada imani? saboda Allah mum she's just 14 amma see what ur making her go tru. Yarinyar nan kin zalince su itada mahaifiyarta amma babu wanda ya kai karar ki a cikin su shine kike neman ki salwanta rayuwar ta da azaba? mum kiji tsoron gamuwarki da ubangijinki, hakkin gado ma kadai ya ishe ki tashin hankali saboda Allah baya.....'' bata barshi ya karasa ba ta daka mishi tsawar daya saka shi kawo ayar dole tace '' ya isheka haka abdul,ya isheka nace! rashin kunya zaka mun iyeh saboda wanchan stupid girl din da worthless uwarta? laifinane da uwarta ta gamu da lalura kokuma laifinane da uwartata batada dangi? har ka isa kazo gabana a matsayina na mahaifiyarka kana gaya mun maganganu son ranka?.to tun wuri ka natsu tun kan na bata maka rai mara wayo kawai idan kuma ita asiyan ce uwartaka sai na sani'' bai san sanda ya soma hawaye ba saboda takaicin abubuwan da take fada shi ya dau hanyar gabas ita ta doshi yamma tayi mishi fahimta abai bai wanda shi yasani duk don kare kanta daga fada ne '' mummy its enuf mana nasan kin fahimce nufina ur just tryng to turn it up on mi saboda bakya so na tuhumeki da abunda kika aikata ne no na sani , inaso ki fahimceni koda sau daya ne a rayuwa, just once! mum they're suffering already ki barsu suji da rayuwar da suka tsince kansu a ciki dont add up to their sorrows pls mummy kidaina abubuwan da kike musu. Inada imanin zan daina zuwa gidan nan idan anyi hutu muddin bazaki daina aikata irin wadanan ababen ba, na gwammace na zauna a gidaa a chan har hutu ya kare akan na dinga zuwa nan neman sassauci ina cin karo da tashin hankali'' bai saurareta ba ya fice da sauri, bai wa zee magana ba kunnenta kawai ya ja zuwa waje, kawarta da suke rawa tare tuni ta fice ganin abunda yayi wa abun kidansu. A tsakar gidan suka tsaya '' yau kin gaisheni? bama wanan ba sau nawa na sha gargadinki akan batun saka mana waka a gida saikace gidan party'' tana kara tace '' yaya dan Allah kayi hakuri daga yau bazan sake ba'' saida ya murda kunnen sanan ya saketa '' wuce mota ki jirani gani nan zuwa'' ta juya zata tafi sai a lokacin ma ya lura da suturar jikinta ai cikin zafin nama ya janyo ta ya kwada mata wadansu marruka guda biyu hagu da dama masu rai da lafiya, tsabar shiganta da mari yayi yasa ta soma zubar da jini ta hanci, ta bude baki zata saka ihu ya mangare bakin da bayan hanun shi yana mai zare mata ido yace ''yi mun shiru kafin na kara miki wani jinin, dan uwarki ba hanaki sakawa samiha kayanta ba? bakida suturu ne a daki kokuma dukkanin wadanan awkatunan da suke jera a cikin dakin ki tsummokara ne a cikin su? waima shin da sunan ki na siya? next tym ki kara saka mata kaya koda mistake ne na ganki da mai kama dashi sai na kusan sumar dake a gidan nan idan yaso kisa mummy ta tsine mun na bi duniya na lalace hankalin dukkanku ya kwanta mai shegen kunen kashi kawai'' ya dunkule mata wani rankwashi mai tai da lafiya saida ta tsungunna saboda zafi, hanun abdul bashi da kyau gashi babu halin tayi ihu a kara mata duka, ya daka mata tsawa tuni ta wuce wajen mota jikinta na rawa shikuwa yaje ya ciccibe umma zuwa mota sanan suka wuce asibiti. Zee na zumbure zumbure haka ta taimakawa samiha wajen saka mata sutura a jiki sanan ta zauna a wajen har ta farka ta bata abinci saboda umma ta kasa hannunta na rawa shikuwa tsabar tausayinta ne ya hanashi iya bata domin gani yake duk inda ya taba a jikinta ciwo ne. Haka ta karaci jinyarta a asibiti aka sallamosu da taimakon Abdul bai bari alh saminu yaji ba don gudun kada yaji sanadin da hakan ta faru.

NI MACECEWhere stories live. Discover now