Ni Macece Part 7

65 4 0
                                    


                                                         🌠🌠🌠🌠🌠   NI MACECE 7🌠🌠🌠🌠🌠

Shekararta daya a gidan ta sunkuta danta lafiyayye kuma kyakyawa bulbul dashi, ya dauko ta sak kasancewar ita ba baya ba ta fannin kyau amma yatsu da tsayin na baban shi ya dauko, sati na zagayowa aka sanya mishi sunan Abduljabbar. Daga nan kuma fa hali sai abunda ya karu saboda hata daukan dan idan asiya tayi sai an dunkule magana an yar mata wai ita bahaushiya bata san itama asiyan a garin hausan ta girma ba saikace jakar kano amma sai ta kyaleta kaman bata fahimce komi ba ta tura mata aniyarta abunda kuma ke kona mata rai kenan, Abduljabbar nada shekaru biyu cikin wata shidan dake jikinta ya bare, ta sake daukan wani ya bare , ta sake wani shima ya zube a takaice barinta hudu bayan danta na fari. Kawai sai ta hau ihu da kuruwa wai ai asiya mayya ce, bata haihuwa ta bada mahaifarta ita kuma da Allah ya bata shine take so ta hada da nata ta cinye to wlh bata isa ba, tana gama jinyarta a aisibiti tana isowa sai gata da yan sanda wai a kama mata ita a tsare, yan sanda kuma suka tasa keyarta sai cell saida ma ta kwana sanan labarin ya kai kunnen maigida kasancewar baya gari a lokacin da abun ya faru. Atake ya dau hanyar katsina cikin tashin hankali, yana isowa tun daga waje yake kwala mata kira ta fito tana iyayi don bata zata ya ji labarin ba yana isowa ya dauke ta da wasu tagwayen maruruka saida taga gilmawar taurari bai ma bari ta dawo hayyacinta ba ya shaketa ya hadata da bango tana ta kakarin fitar numfashi ya zare mata idanun shi yace ''na rantse da ubangijin da numfashina ke gudana da izinin sa, muddin baki fada mun inda kika kai mun matata ba saina kasheki na kashe banza kuma inki dauruwa'' idanunta sun firfito saboda zabar shaka bata jira yakashe tan ba tayi mishi bayanin da yake bukata cikin sarkewar numfashi, yayi wurgi da ita akan tiles bayan ya kwada mata mari ta ukun sanan ya fice da sauri ga police station din. Ya tarar tayi amai a cikin cell din ta gama jigata duk ta zube tashi daya, da azama ya fito da ita sai asibiti aka soma bata kulawar gaggawa, aunin farko sakamako yanuna tana dauke da juna biyu. Ya dinga murna kaman zai hadiyeta, ya rasa inda zai saka ranshi sabooda farinciki don ko a lokacin cikin abdul baiyi doki makamacin wana ba. Sai bayan kwkaanaki biyu aka sallameta daga asibitin, yanda yake nan da nan da ita saida haushi ya saka jamila tayi yaji wai ita da take da ciki ko kallo bata ishe shi ba amma da yake matar so ce ji yanda yake bata kulawa, ai yaki zuwa biko da kanta data ji wuya ta ci miyan kuka da gabza ai da kanta ta dawo saboda guduwa ma yayi daga garin yace wani taro saboda takurar da maman ta dinga mishi akan ya maida ta. Haka dai ta dinga hantarar ta akan wai kan ta samu ita tayi fiye da hudu sanan koda ta haihu danta ne babba a gidan don haka dole dashi za'a dinga damawa, ita asiya dai tsakanin su saidai kallo saboda idan da sabo tama saba da halinta shiyasa baduka abu bane idan tayi ke damunta ba. Cikinnta nada wata goma ta sunkuto yarta kyakywa son kowa kin wanda ya rasa, sak mamanta amma idanun da faratan da kuma tsayin duk na babanta yana ta tsokanarta wai dukkansu suna mishi wayo ba'a so a haifa me kama dashi duk suna mishi rufe ido.......................................................................................................................................................Ranar suna yarinya taci sunan samiha amma abun takaici ko yar'uwar shi guda daya babu a wajen taron dukkansu saidai su dinga bada silly excuses kawai iykaci wadanda sukazo daga kanwarta da ya'yanta uku sai abokan arziki da suke zaune lafiya, yaci alwashin sai ya kira kowacce yaci mata mutumci ta fashe mishi da kuka tace muddin ya kuskura ya doshe wani dan'uwan shi a wnan maganar to a bakin auren shi da ita zata tsallaka ta barshi da yar'shi ta koma tsohon rayuwarta, haka kawai zai kara mata jafa'i? a hakan ya suka kare da su ballantana an sake tunzura su, badon yaso ba ya hakura ya kyale a zuciyar shi ya aiyyana a bakin kudaden da sukace ya basu su chanja furnitures dinsu don kishiyar ubansu. Yarinya ta girma cikn so da kulawan iyayenta gata nan dama sambarka ga saurin shiga rai sana akwai surutu bana wasa ba shiyasa kowa ke jin dadin zama da ita,very lively girl the apple of her parents nd Abduljabbar's eyes. tanada shekara daya jamila ta haifo yarta mahaifinta sak itama ba laifi anyi dokin haihuwarta don maigida ya samu me kama dashi ita kuma daga kan samiha bata sake koda batan wata bane. Sau biyu aba mata double promotion a pri schl shiyasa tayi saurin gamawa ta shiga sec schl mai kyau amma day saboda bata son nesa da ummanta

NI MACECEWhere stories live. Discover now