NI MACECE 9
..Aunty salma tana yawan kawo musu ziyara da kuka suka rabuwa saboda tausayin halinda yar'uwarta da neice dinta ke ciki amma ya ta iya? mijinta ba mai karfin aljihu bane saidai godiyar Allah bare ta dauko mihi su su zama mishi liability. Itama kayan da tazo dashi bayan ta tafi za'a tsinta tass a wuce a barsu da fili, zee itace yar'so a gidan, kodata saka wata sutura a jikinta zee ta kyallaro ido ta ganni ya mata kyau to haka zata kwabe su ta kawo mata babu musu saboda tana gudun abunda zai janyo mata duka ba wai don tana tsoron bulala ba saidai don kada ran ummanta ya baci tayita mikewa akan gado tana so tazo ta kwaceta amma babu hali don jan ciki take wasu lokutan kafin ta motsa kasancewar tana iya zama kadan kadan da taimakon adua'a, to hakan dake faruwa na karyar mata da zuciya. A wajen mutum daya kwaia take jin sauki a gidan, yaya Abduljabbar saboda muddin yana nan babu mai mata wanan tsangwamar saboda ayoyi da hadisai na kala Alla kala Annabi shike sa har ta koreta daga gefenta muddin kuwa zee ne sai yayi mata dukan fitan rai har sai an kwaceta gashi maman na mugun sonshi tunda shine dan gaban goshinta shikuma yace ai ita samihar ba sa'ar ta bace saboda haka ta kiyaye shi kamar yanda take ganin kata mai gata haka samihar, komi lokaci ne. Ai muddin abdul na nan kumatunta har cikowa sukeyi gata mai doguwar fuska itada mahaifiyarta a lokacin za'a sarara masu, tana ss1 abdul kuma yana jami'a ranar zee ta zage mahaifiyarta tun tana hadiyewa har ta kasa saboda a duniya idan kanaso kaga bacin ran samiha to ka taba mata umanta, aikuwa ta rufe ido ta zage ta nada mata dan banzan duka, mahaifiyarta na dawowa babu jin ba'asi itada kanwarta da zee din suka nada mata itama dukan daga karshe ma suka kwabe mata wando suka zuba mata dakakkiyar yaji a kasanta sanan suka jata tsakar gida suka tunkude ta suka koma shashin su. Tana kururuwa tana rarrafawa har ta kai karkashin famfon tsakar gidan ta bude shi akanta kayan jikinta azaba yasakata yayyage su haihuwar uwarta ta kwanta a wajen maimakon taji sanyi saima karin azaba abunka da gari mai rana dole tanki ya dau dumi ruwan cikin shi ma haka, radadin dake karuwa a wajen shi ya sanya ta cigaba da ihu tana kuka tana kiran sunan Allah dana ummanta, daga baya ma karfinta ya kare to soma wata irin karar azaba, da kyar mahaifiyarta ta rarrafo zuwa inda take ta tallafo kanta tana kuka tana mai neman agaji. Dalilin kada akawo mata agaji shiyas ma aka aike maigadi, kamar daga sama sai ga abduljabbar,yanata horn amma shiru sai abun ya bashi mamaki domin shi shaida ne akan magadin gidansu baya da yawo sanan kuma bashi da nauyin barci, saukowan da zaiyi daga motar ya bude gate din yaji ihun umma daga sama yayi saurin shigowa, da sauri yayo kansu yana salati zanin dake jikin umman dukda ya jike shi ta cire ta dan daura wa samiha a jikinta sanan abdul ya kinkimeta a sume sai mota, ya harba titi a guje ya bar umma a tsakar gida tanata kuka da kyar da dagyalgyal ta samu ta rufe famfon sanan to ja jikinta zuwa kofar dakinta. Da kyar da siudin goshi aka samu aka shawo kan lamarin don taji wuya ba kadan ba, abdul kuka ya dingayi kamar karamin yaro daya tuna a halin daya sameta sai ya sake saka sabon kuka a bakin shi furtawa yakeyi babu kaukautawa'' mummy ki tsoraci haduwarki da ubangijinki'' yayi ta nanatawa kamar wanda ke naman yin haddar karatu a bisa dole, saida aka kwana sanan numfashinta ta dawo dadai wankin gabdan da aka mata da kuma alluran kashe zafi a hankali wajen ya soma sabewa daga kumburin dayayi, yaje ya sami likita bayan ya tabbatar mai da komi ya dawo normal yace bari yaje gida ya duba halin da mahaifiyar ta ke ciki. A kofar gida ya tarar da ita ta shimfida zani ta zauna akai tana karatun alqur'ani hannunta na rawa kasancewar bata gama warkewar da zata iya rike abu ba, idanunta sunyi luhu luhu sanan daga ganin yanda tayi furu furu da kuma kofar dakin zai tabbatar maka da a wajen ta kwana sana kayan jikinta ma haka tun na jiya, ina taga ta chanji bayan mai kula da ita tana asibiti rai a hanun Allah? Tunda ya kusanto ta ta soma ''abduljabbar ina samiha? ta mutu ko? gaya mun mana kada ka boye mun, mahaifinta mai tsananin sona ya tafi na dangana da rashin shi bare ita, abdul nace ka gaya mun '' tausayinta dana samiha suka taru a ranshi baisan sanda ya durkusa ya fashe da wata sabuwar kuka ba abubuwan daya gani jiya suka zamo mishi sabo fil a cikin ranshi, ganin yana kuka shi ya tabbatar mata da hassashen ta itama sai ta saka kuka ''samiha ya'ta Allah ya jikan ki yasa kin huta da matsalolin duniyar nan tamu da matsalolin da muke fuskanta ya hada fuskokin mu da alkhairi, na yafe miki har abada dukda baki kasance a cikin wacce ta taba aikata laifi ba a gareni saima faranta mun rai da kike burin aikatawa a kodayaushe, samiha Allah yasa karshena nima ya karaso kusa na huta da wana rayuwar'' da kyar ya lallashi zuciyar shi sanan yayi mata bayanin an shawo kan matsalar bari yayi wanka sai yazo suje tare ta ganta tace to. Yana shiga ya tarar da zee da kawarta suna rawa a falon basu ma ji shigowar shi ba saida ya wuce wajen jazz box din ya daga yayi rugu rugu dashi a kasan sanan ya wuce ko sake kallonsu baiyi ba, shashin mahaifiyar shi ya nufa.
YOU ARE READING
NI MACECE
AdventureIts about an orphan girl who lost her father at a young age nd had to fend fo herself and her paralysed mother. Just read and enjoy..