Ni Macece Part 8

56 3 0
                                    

           🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟      NI MACECE 8   🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Tana jss 2 mahaifinta ya kwankwasa wani mummunar hatsari a hanyarshi ta dawowa daga zamfara dayaje wani taronsu na yan kasuwa, labarin hatsarin shi shine musababbin paralysis din ummanta har yayi arba'in a kasa bata san inda kanta yake ba shiyasa koda aka raba gadon aka mikawa samiha gadon su su dukkansu biyu wanda hatta gidan da suke ciki a cikin gadonta ya fadi kasancewar gidanjenshi su uku ne a katsina amma wanan shi yafi girma, saboda gigita da kuma kuruciya kasancewarta mai karancin shekaru tayi musu ajiyar sakaci. Abokin babanta na kut da kut wato alh saminu wanda aka fi sani da baban kassim ya dau nauyin ciwonta suka wuce turai da ita, a wanan term din duka samiha bata je skul ba Allah ma ya sota 1st term ne. Da kyar ta soma samun sauki likitan ya bada shawarar a dinga kawota gashin kashi, samiha tace ah ah sun yafe saboda shima baban kassim din nada ahalin shi masu bukatar shi bai kamata dukiyar shi a kansu zai kare ba, zata je ta hado gadon su sai su cigaba da treatin dinta a nija. Suna dawowa suka tarar an buggling musu shashin su, takardun gadon sunyi sama ne ko kasa oho. suka taru a daki suka ci kukansu tare su su kadai, babu halin a kai kara tunda an riga an raba sanan babu halin ace ga wanda ya dauka tunda basu da shaida sai suka hakura suka rungumi pls suka dau sorry. Suna ji suna gani aka korosu daga side din mamanta bene sama da kasa zuwa kasa guest house din saukan baki sanan ta kore masu aikin da ta nemar musu dukka tace akwai budurwa kamarta a gidan menene amfanin masu aiki dole ta dinga shigowa tana musu aiki......................................................................................................................................................Tun a lokacin samiha ta soma fuskantar kunci da kuma gararin rayuwa maraici mai ta da zaune tsaye ne, haka ata tashi tun assalatun farko, ta soma share share share ta mopping din gidn karan kap idan muguntar ya motsa harda shashinta zatayi kasancewar ta koma shashin ummanta wai wajen yafi kyau da kayatuwa ga kuma enuf space, ta gyara ko'inna tayi wanke wanke a lokacin an kira assalatun safe taje tayi ta dawo ta daura musu break fast ta dawo ta jera a dinning table, idan sunga dama su bata idan basu ga dama ba su hanata, ta fito sanan ta hura icce ta dora wa ita da mamanta ruwan wanka kasancewar tasa anzo an diconnecting musu water heater din bandakin su, ta tallafa mata da rarrafawa tayi mata sanan su dawo tazo ta kimtsa ta, ta koma tayi nata sanan ta soma musu gyare gyare wasu lokutan kuma idan taga zata makara ma skul sai ta bari sai ta dawo tukunna, idan gari ya waye sai ta tafi gidan alh saminu neman abunda itada mahaifiyarta zasu saka a baki ta dawo su karya sana ta dauko ruwan da mahaifiyarta take wa kanta tofi a ciki don samun waraka daga ubangiji domin shine gatan su idan ta gama ta bata ta shanye sana taje ta dauraye kwanukan da sukayi amfani dashi. Sai ta gama da ita ta tabbata bazata nemi komi ba sanan ta saka kayan makaranta ta wuce a cikin motar da alh ya bada a dinga kaita makaranta ita kadai a ciki. Sau tari zai cika motar da kayan abinci kala kala yasa a taho musu dashi, haka suna ji suna gani za'a shigo daki kwashe shi tass, umman na hawaye ita samiha kuma batada bakin magana, babu abinda zata aiktawa a wuce dasu idan ma muguntar nata na kusa bazasu tafi ba sai an nada mata na jaki tukunna sanna su fice dashi. Da abun ya ishe ta sai ta dinga taro mai kayar daga waje tsce yaje dashi gidan shi kokuma yay sadaka dashi amma kawo abincin da yake yi baya kara mata komi illa fitina kuma bata kaunar yanda suke zuwa har gaban idon mahaifiyarta ana dukanta saboda abinci amma dan Allah kada ya fadawa baban kassim saboda kar ranshi ya baci, daga lokacin akasarara mata ta fanin abinicin dukda saida ta kara shan dan banzan duka wai saboda an daina kawo abincin wai tana musu bukulun kayan jindadi, kuji fa? idan ba mugunta ba banda gadon uwarta da natan da suka danne wasu kudinne basu dashi na jindadi da more duniya?. Gashi duk abunda zasu mata bata kai karar wajen kowa sai wajen Allah saboda shine kadai zai iya magance mata matsalar da take fusknta gashi babu dangin iya bare na uba, eh mana saboda daga kakarta har dangin ta ida sunzogidan ko kallo bata ishe su ba, idan za'a kasheta a gabansu basu ko da tari ne saboda tsanar da sukayi wa uwarta ya shafeta. Alh yayi yayi dasu akan su koma cikin gidan shi da zama zasu fi jin dadi kokuma ya kama musu haya amma sunki, samiha tace ai abunma ai sai yayi yawa wai shege da hauka, sun kwace mun hakkina, suna bautar dani nida gidan ubana, ai idan na gudu tamkar na basu kyautar duk abubuwan da suka sata ne daga gareni saidai idan wuya na kisa sai ya kashe mu nida mamana idan yaso alhakinmu ya jibgu akan wuyar su........................................................

NI MACECEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora