🌠🌠🌠🌠🌠 NI MACECE. 6 🌠🌠🌠🌠🌠
Abu kaman wasa karamar magana ta zama babba duk hanyar da zai iya shawo kanta amma abun ya faskara atafur taki amincewa dayaga wankin hula na neman kaishi dare kawai sai ya kaimaganar wajen baba ba don ranshi yaso ba domin yaso ace iata ta soma amincewa sana ya kai kunen baban. Ya zauna ya korawa mahaifinshi bayanin abubda ya faru da kuma halin daya tsince kanshi a ciki, yace kar ya damu zaije unguwar su yayi bncike muddin babu mugn shaida akansu to zai amince da auren, ya fice yana godiya. Akayi bincike a tarar da komi lfya lau kawai sa baban ya amince da auren, maman tace bata san zancen ba yan'uwan ma suka bi bayan ta akan ya hakura kawai ya nema wat amma ya kafe atafur sai ita, da kyar da wa'azi da lallashi ta amince da auren amma tace ita da sonta ar abada tunda ta zamo silar da danta mai tsananin byayya a gareta ya bijire wa umarninta. Akayi aure lami kalau amarya ta tare a cikin tafkekiyar gidanta tre da kanwarta, suka shimfida rayuwar shakuwa da tsantsar kaunar junan su. Ya daukewa salma dawainiyar sabon islamik school di daya sakata na shekaru uku don dukkansu sun nuna sunfi son na arabiyyan nan na boko kam ya fice musu a kai. Tana final year dinta wani dan zari'a yace yana sonta ta amince amma saida aka fada mishi ko ita wacece gudun zancen duniya da baya buya ya kuma amince kasancewar yana sonta, tana kammalaw aka daura musu aure suka wauce zaria da zama. Shekararsu biyar babu ko batan wata bare bari, tunfa maman na jurewa har tsanar da take mata ya motsa ta daga mishi hankali akan lallai aje asibiti a bincika wanene mara lafiyar, saida baban ya taka mata burki sanan ta natsu ta sake dauko batun karin aure baba ma yace muddin zata saka shi auren dole tofa itama saita shirya tare zasu karo tuni ta natsu amma duk da haka ba dama tazo gidan saita jefata da mu gun kalamai, habiba da fatima ma haka suka bi bayan mahaifiyarsu a wajensu ma bata jindadi tayi kuka ta more amma saboda kawaici da zurfin ciki bata taba samun shi da maganar ba saida wanda idanunshi suga ganar mishi. A cikin shekara ta shidan ne Allah yayi wa mahaifinshi rasuwa , ai bai kai wata uku a kabari ba tshon tsana ta mosa ta sake ruro mishi da wutar tashin hankali akan lalle lalle sai ya kara aure sabod a san matsalar dag ina yake. Saboda samar wa kanshi lafi harma da matar shi da aka baiwa dukkanin laifin wai ai ta mallakeshi ta kanainayeshi tana cin dukiya taki ta haihu kuma taki bari shi ya kara aure yace mata ya bata zabi ta zabar mishi duk wacce tayi mishi in shaa Allah zata sameshi mai bin umurninta da gaggawa,ai kuwa kamar jira take da azama ta samo mishi yar kanwarta dake cikin daura da zama mai suna jamila. Ranar kawo amarya saboda yada magana da suke mata kulle kofanta tayi a cikin shashinta taki fitowa gudun kada a fada mata abunda zata kasa jurewa.................................................................................................................................................Amma duk da hakan bata tsira ba domin kuwa ta sha gori da habaici harta godewa Allah don sun san tna ciki sai su dinga magana cikin daga murya, babu irin takale takalen da baa mata ba don kawai ta fito ta tanka a gwabza amma saita ma kunna alQurani a rediyonta tana saurar tana binshi a hankali zuciyarta ya soma sanyi damuwar dake ranta kashi mafi yawa dake addabarta ya soma washewa. Amarya ta tare da nata fi'ili da jinkai da kutungwila ita ai ga yar'uwar shi kuma yar dangi yar asali saida ya taka mata burki tukunna yanuna mata itafa auren biyayya ce wanan kum auren tsantsr so saboda haka ta iya takunta ta bar ganin dangantakar su muddin ta ce zata matsa wa matar shi to lalle zata koma gidan su ya auro dubbai bayan ita kuma ko sisi a arzikin shi bata girgiza ba.
Ganin daula zai wuce ta a barta da babu ai tuni ta natsu sai dan abunda ba'a rasa ba saboda hausawa sun ce mai hali baya fasawa saidai ya dan rage wasu abubuwan, tashin farko Allah ya bata ciki, wai! zo kuga iyayi da shagwaba har sakawa tayi a kawo mata mai aiki wai bazata iya da aiyukan gidan ba sanan ga juna biyu, shidai binta kwai yake da ido da kuma to don kawai su zauna da uwarshi lafiya.
YOU ARE READING
NI MACECE
AdventureIts about an orphan girl who lost her father at a young age nd had to fend fo herself and her paralysed mother. Just read and enjoy..