Khairiyya tace "what,am i dreaming or what, Ammar idan mafarki nake please ka tashe ni, Captain Suraj kaine a gari lalle kam yau za'ayi ruwan sama da kankara"tana wage hakora, Suraj ya d'au kujera yazauna agaban gadon,kallon ta yake, ta kara masa kyau sosai gashi duk bakin ciki ya cikasa, waye haka yake kama mata gashi da ribbon yace
"Sai yau KIM, jiya na dawo daga kasar da aka turani course, sai yau nashigo Maiduguri, ina shigo wa naje gidana na kunna TV nagan hoton ki an saka missing, shine nafito neman ki", Khairiyya ta zare ido ta bud'e baki with soo much suprise on her face tace
"Yaya Suraj hoto nah a TV kuma missing", tana fad'an haka ta juya wajen Ammar tana kallon sa, tsab tasan shi ya aikata, Khairiyya tace
"Yaya Ammar haba dai, basai kajira gari ta waye ba, kawai ka kama kasaka hoto nah a Tele6ijin gaskia baka kyauta mini ba", Shiko Ammar koh kulata baiyi ba yana gama d'aure mata gashin ta ya nema gyale ya rufe mata gashin ta dashi, duk bakin ciki da kishi ya rufe sa anga gashin KIM nasa, Khairiyya taga bashida niyan kulata tace wa Suraj
"You are so nice, thanks for the care, naji dad'i sosai, gaskia gwara da kadawo cox nayi missing naka sosai", zo kuga dad'i a wajen Suraj, yana wage hakora yace
"Nazo nima sabida ke, I miss you more, da naga hoton ki missing har hankali na ya d'aga, I don't wanna loose you", Khairiyya tayi murmushin jin dad'i, ita tana kaunar duk mai sonta, tace "Nagode Captain Suraj Allah bar kauna", sanda cikin Ammar yayi kululuu da jin maganar ta, ranshi yayi mummunar 6aciwa, Sallama akayi, suka amsa tukun aka bud'e d'akin
Zilyadeen, mummy, Hajja da Rumaysa neh suka shigo d'akin, Zilyadeen sanda yaji zuciyan sa ta buga (nidai nana nace OMG kamar ina kallon Clash of the titans )
Khairiyya kam zuciyan tane yake bugawa, koh dai shine yayan Rumaysa da ya buge ta, Suka gaisa dasu mummy, mummy tace
"Khairiyya ga mutuminki da ya buge ki", zuciyan ta ya tsanan ta da bugawa, Muryan shi naji yace
"Khairiyya ya jiki", da voice nasa mai narkar da zuciyan ta, Khairiyya tace
"Dasauki", da tsiririn muryan wanda Ammar baisan ta dashi ba, atake ya juya ya kalle ta, tana da zak'in murya amma yadda ta amsa shi daban neh, sai wani kunya kunya takeji, ana hira bata magana sai murmushi, Suraj kam yana jin dad'i Khairiyya ta canza hali baisan da biyu baneh
Ammar ya kira Ummi yace suna asibiti, Ummi tace toh yanxu zatazo, ba'afi minti goma sha biyar ba sai ga Ummi da Zainab
Ummi da mummy kallon juna suka fara, Ummi ta nuna ta da yatsa tace sis Ramaadah kece wannan, Mummy ta rungume ta tace nice Aysher, mummy tace lalle yanxu shekaru nawa da rabuwa, tun muna secondary school, ikon Allah kenan (mummy da Ummi sunyi makaranta d'aya da suke yara GGSS BAMA da ke cikin borno)
Ummi tace ai Khairiyya yata ce, mummy tace Allah sarki ikon Allah kenan,Mummy tace sai hakuri fa, Ummi tace abu Allah ya qaddara zai faru, ai ba komai, duk suka gaigaisa, haka dai d'akin yacika dam mummy da Ummi suna hiran makarantar su,ana shan dariya, Rumaysa tana satan kallon Zilyadeen, Ammar da Suraj suna satan kallon Khairiyya, Zilyadeen ya kalla Rumaysa ya kalla Khairiyya, idan Khairiyya ta had'a ido da Zilyadeen sai ta sunkuyar da kai tana murmushi, idan ta had'a ido da Suraj sai ta kashe masa ido d'aya, idan ta had'a ido da Ammar sai ta murkud'a masa baki tayi nuni da hannun ta irin ya da zafin kallo haka.....
Haka nan dai Nurses suka kore su sutafi saidai suzo karfe hud'u visiting hours, Ammar yace zai zauna, Ummi ta harare sa tace
"Kajika fa, nidai zan zauna", Hajja tace sam ita bata yarda ba, Ita zata zauna da Khairiyya responsibility nasu neh, haka Hajja ta dage, Rumaysa ma tace toh zasu zauna tare da Hajja, Ummi tace baza ayi haka ba, Zainab zata zauna da Hajja, akayi shawara akan Zainab da Hajja zasu na kula da Khairiyya
Haka duk suka fita a d'akin akabar Hajja, Khairiyya da Zainab... daga nan Khairiyya tayi bacci su Hajja da Zainab kuma suna ta hira Zainab tana ta shan dariya....
Bayan su Zilyadeen sun koma gida, Mummy tayi gaba ta barsu, rike hijabin Rumaysa yayi yace
"Haba my future wife, jiya na wahala baki kwana a gidan ba, yau kuma wai zaki kara zama, koh muryan ki bakiso naji neh, bakisan nayi missing naki ba", Rumaysa ta wani rufe fuska da hannun ta tace
"Inaso mana Nurul hayat, nima nayi missing naka", tana gama fad'an haka tayi gudu tabar sa awajen yana wage hakora, yace "Rumaysa ina matukar kaunar ki, I love you sooo love, tun ranar da kika zo duniya nafara sonki kuma bazan ta6a iya daina sonki ba, I love you to the square root of infinity", yana gama fad'an haka ya tuna da Khairiyya, yaji kansa ya d'au zafi gaba d'aya, ya furta
"Khairiyyahhhhh, meisa nake tunanin ki neh, I think of you every moment, whyyyy".... masu karatu yaci ace zuwa yanxu kunsan wacece Khairiyya, wanene Zilyadeen da kuma Suraj, toh lemme start with Zil, zan fara da Zilyadeen
YOU ARE READING
KHAIREEYYAH(Completed ✔)
Teen FictionKhaireeyyah is a story of a beautiful, charismatic, rich,stubborn gurl... she got everything she ever want in this world, everything she desires.... But there is one thing that makes her life miserable.....LONELINESS!!!!! And this Loneliness turned...