Ammar yace "Shhhh Khairiyya just shutup, ba abun da Dr Umar zaiyi wa Zaynab, let me call her ma kiji", a take ya d'au wayar sa ya danna wa Zaynab kira ya saka a loudspeaker, Zaynab tana picking call d'in tace
"Hello Yaya Ammar, Monster na KIM", Khairiyya da sauri ta kar6a wayan tace
"Zaynab kina nan lafia, kina ina", Zaynab tace
"Kalau KIM, ina saloon ya jiki'', Khairiyya ta kalla jikinta tace a hankali ya jiki kuma,ta kasa recalling mei yafaru, ya akayi tazo asibiti, tace
"Da sauki Zaynab, zanzo gidan anjima ki mini biski da miyan kuka", Zaynab tayi dariya tace
"Toh KIM, ina jiranki sai kinzo", Ammar ya kar6a wayan a hannun Khairiyya ya katse wayan, ya kalle ta yace
"Yanxu kin yarda Zaynab tana nan kalau koh", ta d'aga kanta alaman Eh, Ammar yace
"Oya sleep now kinji", ta zumburo bakin ta tace
"Nifa ain't feeling sleepy"
Ammar yace "kedai try", da lallashi har bacci ya d'auke ta.......
Sunyi two days a asibitin, kullum Suraj da Ammar suna yini da ita a asibiti, Ammar shi yake kwana da ita Suraj sai dare yake barin asibitin, sosai take hira da Suraj dan koh kad'an bata rik'e sa a rai ba, itadai sai mamakin sa take, shi da yace ya fasa auren dan tanada HIV, koh dai yanxu yasan gaskian neh, haka take ta sake sake a rantaWashegari aka sallame su a asibiti, she was suprise da tafita a hospital d'in taga gaba d'aya ma ba a Nigeria take ba, sai tambayan Ammar take ya akayi suka kawo ta India, shi kuwa koh amsata baiyi ba, sanda suka dawo gidan ta takura mishi lalle sai ya fada mata, tace
"Mr Ego nifa I can't recall anything, the last thing I can remember shine kiran da Dr Umar ya mun wai na samei shi a Down Town", Ammar ya zauna a kujera yace
"Oya zauna KIM, ban lbr mei ya had'a ki da Dr Umar da har yana so yaga bayanki", Khairiyya ta zauna tsab ta basa lbrn had'uwar ta da Dr Umar, Ammar bud'e baki yayi yana kallon ta yace
"KIM abun naki har haka, stubbornness naki yayi yawa O-V-E-R, Allah sarki matar shi Allah jikan ta May Jannatul Firdaus be Her Final Abode", KIM tace
"Hmmm Ameen Ammar, ban ta6a tsaman abun zaikai ga haka ba, but fault nashi neh da ya ta6a ni da dirty phalanges nashi, I sooo much hate namiji ya ta6a Diamond skin nah, Mr Ego koh aure nayi haka zamu zauna da Miji nah ba ta6e ta6e", Ammar ya fashe da dariya yace
"Kai amma kin taka sa'a wollah, da saidai muji KIM tana da ciki koh an aura mata Zil ya koro ta yace ita um um um ce", sai ya kara fashewa da dariya, pillow ta d'auka ta fara dokan shi dashi tana cewa "
Allah ya isa Ammar, Toh aini ban kai wani abu ciki ba, i'm still a small gurl", Ammar yayi dariya yace
"Ban yarda ba, ko zamuyi practical neh, muga koh zaki d'auka koh dagasken ke yarinya ce bazaki iya d'auka wa ba", Khairiyya taja wani dogon tsoki tace Allah sawwaka wlhBayan sun nutsu ta juya ta kalla Ammar wanda shi already ya kura mata ido yana kallon ta with soo much tenderness in his eyes, KIM ta kashe masa ido d'aya tace
" Im pretty ryt, Mallam karka cinye ni da kallo, what exactly ya samei ni neh da kuka kawo ni India", Ammar ya bata lbrn tsab abun da ya samei ta but bai fad'a mata An cire Kidney shi d'aya an dasa mata ba, shidai kawai yace tayi accident kuma taji ciwo sosai shiyasa aka kawo ta har India......Da daddare Suraj yazo gidan suka sha hiran su as normal, ita sai mamakin sa take, tana son tambayar sa koh yanxu yasan the truth amma ta kasa tambayan sa, haka suka sha hira Ammar yana gefe sai danne dannen waya yake, Suraj yaso Ammar ya baso wuri amma Ammar ya zauna daram yana facing nasu duk maganan da suke a kunnen sa
Bayan kwana Uku jirgin su ya d'aga zuwa Nigeria, a Abuja suka sauka, daga nan Washegari suka hau jirgi zuwa maiduguri, Suraj ya wuce gida Ammar da Khairiyya kuma suka wuce nasu gidan, gidan su Ammar
Suna shiga da gudu Zaynab ta rungume Khairiyya tace
"Welcome Sis, ya jiki", Khairiyya ma ta rungume ta sosai tace
"Alhamdulillah Zee Ustaziyas, nifa naji sauki banjin abu yana damu nah", Ummi ma tafito suka gaisa da Khairiyya tana tambayar ta yajiki, Khairiyya tace itafa ta warke a daina tambayan ta yajiki, Zaynab ta kaita d'akin ta already Ammar ya sa an gyara shi komai sabo daga kan gado har carpets, kayan ta ma a wanke a goge. Toilet tashiga ta watsa Ruwa tayi alwala tafito tayi sallah, bayan ta idar ta d'au Al Qur'anin ta tafara bi
Ummi da Zainab a parlour suna kallon Aljazeera, Khairiyya tafito a dakin ta dtace
"Gaskia Ummi nifa jininah yaki News, zan shiga wajen Ammar muyi hira", Zaynab tace
"Toh Mrs Ammar sai kin fito", Khairiyya ta harare ta dan bataso tayi magana a gaban Ummi ta tashi ta tafi, Sallama tayi Ammar ya amsa kan ta tusa kai tashiga ciki, Hoton tane daman a hannun sa yana kallo jin muryan ta ya tusa hoton a karkashin pillow, bayan ta shigo ta nema waje ta zauna tace
"Mr Ego wai ni ina waya ta neh"
"Wayar ki d'aya tazama condem lokacin da kema kika kusan zama condem, d'ayar kuma na je na kar6o miki wajen su Haule"
"Heges Haule nasan taci kasuwa da waya ta, Toh yanxu ina the phone", yana drawer cewar Ammar, da sauri ta tashi ta bud'e drawer ta d'au wayar ta kirar Samsung S6 edge, wayan Ammar da yake chargy ta cire tayi plugging nata yana gani baice kala ba, bayan ta kunna taga Emergency, kusan minti goma Emergency, tace
"Wai ni Ammar ba network neh", Ammar ya duba wayan sa yace
"Akwai mana", ta tura bakin ta tace
"Toh ya ni Emergency yake nuna mini"
"Maybe sunyi blocking", ya fad'a mata, da sauri ta juya ta kalle sa tace
"Blocking in what reason zasuyi blocking SIM nah", Ammar baisan lokacin da yace
"KIM Ten months ba wasa baneh fa", yana danne danne a wayar sa baisan ma ya fad'a ba, zaro idon ta tayi tace
"Ten months, wata goma kenan fa, kana nufin Ten good months bani da lafia"
Kallon ta shima yake yace
"Sorry to say gaskian kenan", da gudu tafita a d'akin taje parlour ta durkusa gaban Zaynab tace
z"Ustaz zee yauwa muna musu da Ammar, wata nawa nayi neh a India", Zaynab tace
"Mtsww kodai baku rabuwa da shirme, wata goma mana"
"Ki rantse Zaynab, nidai ban yarda ba", Zaynab taja tsoki tace kar Allah sa ki yarda
YOU ARE READING
KHAIREEYYAH(Completed ✔)
Teen FictionKhaireeyyah is a story of a beautiful, charismatic, rich,stubborn gurl... she got everything she ever want in this world, everything she desires.... But there is one thing that makes her life miserable.....LONELINESS!!!!! And this Loneliness turned...