Yarinyan Alhaji Ibrahim Muhammad fu'ad, sunan ta Khairiyya cewar Mami, Munay ta zare ido tace
"Dan Allah Mami, na d'auka wata talakace ai, toh yanxu yazamuyi"
Mami tace da hankali "beauty (sunan da take kiranta) the best solution kawai muje wajen malamin nan", Munay ta 6ata rai tace
"Mami kin sandai ba abun da natsana a rayuwata duk iskanci na kamar zuwa wajen malami da boka koh, ki kawo wani shawaran amma ba wannan ba Cox gaskia bazan yarda da wannan shawaran ba", Mami ta tureta tace
"Mtswww kefa banza ce, ana nuna miki hanya kina bijire wa, ashe dai ba Sonshi kike ba", Munay tana shan kamshi tace
"Gaskia maganar gaskia tsakani da Allah ba wani sonsa nake ba, kawai dai inaso ana nuna ni ace ga matar *GENERAL SURAJ*, (yanxu dan an kara masa matsayi), shineh kawai Mami ana nunani ana cewa ga Matar sa, kin ganeh ai, kinsan ni Mami inason karya da respect, ina bala'in son kayan karya, duk wani cewa ina mutuwar sonsa fa I don't really mean it, ina mutuwar son matsayin sa neh not shi d'in", Mami tace
"Lalle beauty Toh ai shineh so d'in", Munay ta girgiza kanta tace
"Mami nasan So, wanna baya cikin signs na So, a rayuwa ta mutum d'aya na So kuma kinsan wayeshi, tunda ya rasu ban kara jin irin feelings ma wani d'a namiji ba", Mami tayi dariya tace
"Lalle munay the beauty, tunda bakison aikin boka da malami yanxu mei abunyi", Munay ta tashi a kujera tace
"Yawwa yar gari, yanxu kike magana, kinsan mei Mami I will think of a solution, zan samo mana mafita ba boka ba malam, just give me a day, cikin kwana d'aya sai mu shirya aikin da yafi na boka koh malam", Mami tayi shewa tace
"I trust you munay the beauty, Allah bar mini ke", Munay tace Ameen*Wanene Suraj*
Captain Suraj a.a wanda a yanxu General Suraj a.a, Asalin sunan shi Suraj Adam Abubakar, Yaron Mallam Adam Abubakar
Mallam Adam Abubakar ma'aikaci neh a UBA BANK, yan asalin garin maiduguri/kunduga baribari gaba da baya, sai matar sa malama Safiya ita yar asalin garin gombe, mutanen kirki neh sosai, Mallam Adam su biyu neh iyayen su suka haifa, shi da Alhaji Muhammad (mahaifin munay), iyayen su sun rasu tun suna kanana, haka suka tashi suna sana'ar hannu suna makaranta, bayan Shi Adam yagama ya samu aiki a bank yadauka nauyin kanin sa Muhammad a lokacin ya aura Safiya, bayan Muhammad shima ya gama marantan sa aka turasa service (NYSC) a Kano, a Kano ya had'u da Saude har suka fara soyayya, Muhammad yana da hankali sosai da sanin yakamata but amma Saude mace ce mai son duniya, tafifita duniya akan komai
Bayan shekara d'aya da aure Safiya da Adam ta samu ciki, bayan wata tara ta haifa d'an ta aka rad'a masa suna SURAJ, Suraj yana shekaru uku Muhammad shima ya aure Saude, Allah bai bata haihuwa ba sai bayan shekaru goma, inda ta haifa yarta aka rad'a mata Suna Munay......
Suraj yana shakaru goma sha hud'u mahaifan sa Mallam Adam da malama Safiya suka rasu a plane crash, inda Adam zaikai Safiya asibiti India dan tana da matsala da kidney nata za'a mata kidney transfer.. Toh tunda rasuwar mahaifan sa ya koma hannun kanin babanshi da zama wato Alhaji Muhammad (Abu ) ya rike sa tamkar d'an cikin sa shi ya haife sa, Saude (Mami) itama ta rikesa daidai balaifi, watarana ta musguna masa watara ta masa abun arziki, Suraj yana matukar kaunar su sosai kamar su suka haife sa, shi baima san Mami tana musguna mishi ba ya d'auka discipline neh take koya masa.. Yana bala'in kaunar su and he always abide by their rules, idan sunce bari toh har abada ya bari kenan, Mami tana yinsa dan ita a tunaninta ta juya masa kwakwalwa neh, a tunanin ta aikin bokan na ci batasan tsantsan biyayya baneh, Mami na matukar son yar ta Munay ta aura Suraj dan tasan koh bayan ransu zai kula da ita and most especially yana da kud'i... Munay kuma tun da tasan kanta basu ta6a zama tare sunyi hira ba danshi mostly baya zama a gidan ma, tun tana primary yaje school na soldiers, amma yana matukar burgeta, Munay yarinya ce mai Son girma, yarinya ce mai Son karya, Farko BSC Nursing suka bata a Unimaid ta canza zuwa environmental biology wai ya mata wahala she can't stress herself............................... *wannan kenan*.............
Da misalin karfe takwas na dare bayan isha'i Suraj yazo gidan su Khairiyya, bayan sun d'an ta6a hira da Khairiyya yace
"Please ki sanar da Abba iyayena zasuzo next week akan maganar auren mu ", Khairiyya tayi murmushi tace
"Ba komai Allah nuna mana", amma can kasan zuciyan ta ita kad'ai tasan yadda take feeling
ESTÁS LEYENDO
KHAIREEYYAH(Completed ✔)
Novela JuvenilKhaireeyyah is a story of a beautiful, charismatic, rich,stubborn gurl... she got everything she ever want in this world, everything she desires.... But there is one thing that makes her life miserable.....LONELINESS!!!!! And this Loneliness turned...