CHAPTER FOUR

752 25 0
                                    

      Bayan tayi addu'a ta kwanta, wayar tane yafara ringing, wata number tagani wanda bata sanshi ba kuma ba number Nigeria ba, Khairiyya tace koh Abba neh, d'auka wa tayi tace "hello"
   Can 6angaren akace Baby nah yakike, muryan mace mei dad'in gaske wanda ya tabbatar mini dana mahaifiyar taneh, Khairiyya tanajin muryan Ammi tawani 6ata rai, tace
"Ammi yanxu kuma kina wani country"
Ammi tace "Baby nah ina Sri lanka but very soon zan dawo Nigeria"
"Ahh Ammi idan kinso karki dawo fa, dan nasan koh kin shigo nigeria wajen mijin ki zaki tsaya so banda problem ki dawo koh karki all thesame to me, yanxu zanyi hanging off call d'in dan bacci nakeji bye" Khairiyya ta katse wayan, bakin ciki neh ya cikata, baccin ma kasawa tayi, tashiwa tayi ta d'auka Roci sachet d'aya ta tsosa tsab ta kora da codein, kan ace kwabo har bacci yayi awon gaba da ita....... Ammi kiran ta takeyi har kusan 3missed call amma Khairiyya ta saka wayan a silent bataji kiran ba

      Washegari da safe misalin karfe takwas Khairiyya tana kwance a kasa akan sallaya tana bacci, Haule ce ta bud'e kofan d'akin tayi sallama, tashin Khairiyya take tace
"Hajiya ki tashi kiyi shirin makaranta kinga kinyi latti"
   Khairiyya cikin muryan bacci tace "Haule bazan kara zuwa school ba sai ranar da zafara waec dan saura sati d'aya ma mufara so please kibarni nayi bacci nah"
Haule ta tashi tabar mata d'akin, Khairiyya bata tashi a bacci ba sai kusan karfe sha d'aya, shiga toilet tayi tayi brush, dinning ta wuce dan cin breakfast, Lanzania da Fish sauce neh a food flask, ta6e baki tayi tace ba'saban ba yau Dije tayi abun kirki, zama tayi ta narka sanda taji cikin ta yayi nak tukun ta ture plate din
Kiran Dije tayi, Dije tazo ta durkusa tace "Hajiya gani nan"
"Dije Lanzanian nan ya naji shi wani iri but ba laifi dai ya d'an yi dad'i you try a little, lunch inason ki mini pancakes da pinkcles kinji, and kuma ki cewa Haule na ajiye albashin ku gaba d'aya ta raba muku"
"Toh Hajiya mungode Allah kara bud'e" Khairiyya tace "Ameen"
Tashiwa tayi ta wuce d'akin ta tayi wanka tasaka atampa super wax dark blue wanda yake da touches pink d'inkin riga da skirt wanda ya matukar amsan jikin ta da fatar ta, d'aukar wayar ta tayi taga 25missed calls wanda almost all na Sabir neh da na Abba guda biyar sai na Suraj guda d'aya da wanda Ammi tamata daren jiya guda Uku, dialling number Abba tayi, yana picking yace
"My daughter where have you been inata kiranki bakya picking yanxu ina airport inada wani meeting a Spain but I will call you immediately idan na iso"
   Khairiyya tace "Ohk Abba safe journey"
Number Kamalu badd take kira amma baya d'auka wa, tun ranar da abun Corper da  sojoji yafaru bata kara ji takansu ba, gashi tun jiya take kiransa baya d'auka wa, mtsww yanxu Kamalu badd baya d'aukan waya ta koh ya zanyi da Sabir neh oho, can tace Wow I got an Idea, number Suraj tayi dialling, a take yayi picking, Khairiyya tace
"Hello Yaa Suraj naga missed call naka Wlhy so sorry bana kusa da wayan neh"
Suraj yace "ba komai Kim, daman i just wanna say good morning neh"
"Ayyah thanks alot, u remembered abun da nace maka jiya, if you are free mu fita"
Suraj yace "Sure why not, ba abun da nakeyi now, nazo neh yanxu"
"Umm no why not mu bari sai da yamma around 4 haka, cox yanxu akwai rana"
Suraj yace "Ohk toh shikenan sai anjima, I will come en pick you up around 4pm" Khairiyya tace ohk toh shikenan bye, ta katse wayan....
     Gaban madubi ta zauna ta tsara kwalliya, cos taje Tara makeup school ta iya kwalliya ba karya, ni Nana nace Wow cos Allah yamata kyau, ta d'aura d'an kwalin kayan ta yafa gyale a kafad'a, key na motar ta da woyoyin ta ta zuba a jakan ta MK mai kyau, Motar Abba ta d'auka S-Cross wanda a Nigeria gabaki d'aya mutaneh uku neh suke hawwan kalar motar, fisgan motan tayi sai Uni-Town,  Wani babban restaurant neh, parking motar ta tayi a parking slot, bayan ta shiga ta siya su ice cream da meatpie, komawa tayi parking slot dan ta d'au motarta, mei zata gani, wata mota ce kirar Benz007 ta rufe mata hanya yadda baza ta iya fitar da motar ta ba, dogon tsoki taja tace mtsww yanxu ina zanga wannan mei motar na masa magana ya fitar da motar shi, ai wannan iskanci da rashin hankali neh, kujera ta zauna a waje tana shan iska tana shan ice cream nata, idonta  kyar na wajen motarta tana jira taga wanda ya tare mata hanya, can ta hango Sabir da wani saurayi kyakkyawan gaske sun nufo wajen motar da alama Benz din nasu neh, Khairiyya tace
"Wow seems like I know this face somewhere, the face looks familiar, tabbas kaman nasan Guy da yake tare da Sabir, mtsww banson surutu nasan yanxu ina Sabir zai rikeni da surutunshi, he's a goddamn Talkative, if not wlhy da ba Sabir baneh dasai naci musu mutunci, yanxu ma dan banason yawan surutun Sabir neh
Sai satan kallon Yaron da suke tare da Sabir take, amma brain nata ya kasa recalling inda tasan Yaron, can wajen su Sabir kuwa sai cewa yake
"Wow Yaya Zilyadeen kaga motan nan kuwa, S-Cross neh fa wanda nake ganin tallan shi a show na ride, gaskia motar tayi" yana fad'a yana shafa motar
   Zilyadeen yace "kaidai tunda muka shigo nan maganar motar nan kakeyi, sai kayi addu'a Allah baka arziki mai Albarka, sai kaga kasiya wanda yafi wannan ma"
  "Kai inaa yaya ni koh wannan ma ya isheni bana neman wanda yafi wannan, kasan mei yaya, kamar inajin kamshin turaren wata sabuwar babe danayi Kim" cewar Sabir
Zilyadeen yace "Toh yanxu kuma wacce kasamu sunan ta Kim, lalle kam kaidai da son matan ka gwara ka rage"
"Kai yaya wannan fa daban ce, ta had'u iyakan had'uwa, zanso ka ganta yaya tayi wlhy, mss hot nake kiranta amma asalin sunan ta Khairiyya"
Zilyadeen yanajin Sabir ya ambato Khairiyya atake kalan fuskan shi ya canza, mode na face nasa yakoma wani iri, dan yanxu Khairiyya yana d'aya daga cikin sunayen da ya tsana a rayuwar sa, yace
"Idan zaka shiga mota kashiga, idan baza ka shigaba naja motata nayi gaba" Sabir yashiga mota Zilyadeen yaja suka bar haraban Uni-Town restaurant, duk maganganun da sukeyi Khairiyya idonta nakan Zilyadeen, he's sooo damn cute and kaman nasan shi awani wajen, Toh where??? Yaa Rabbi ina nasan fuskan nan, haka ta gama sake saken ta tad'au motar ta sai gida, tana zuwa gida ta mikawa su Haule ice cream da meatpie  itama takai sauran d'akin ta tasaka a fridge, tayi alwala tayi sallah, tana idarwa tace "Gosh the world is moving so fast, lemme make it slow"
D'aukar Benelyn da wasu kwayoyi tayi tasha, batafi seconds biyu ba bacci mai nauyi ya d'auke ta, itace bata tashiba sanda Haule tazo tana bubbugata, tace
"Hajiya ki tashi kinyi bak'o fa"
Atake Khairiyya ta tashi tace
"Haba Haule har yazo, yanxu karfe nawa neh"
"Karfe hud'u da rabi"
Khairiyya taja dogon tsoki, amm Hajia sorry yanxu 4:30, Khairiyya batasan lokacin da ta tashi ba tashiga toilet tayi wanka da alwala, tana fitowa tayi sallan Asr, powder ta shafa da lipglose, Wata English wear ta saka doguwar riga light purple, ta d'auka Vail (gyale) tayi rolling, ta d'au wayar ta, dubawa tayi taga 11missed calls, biyu na Suraj suran na Sabir, kiran Sabir tayi, yana picking yace
"Haba Kimhot inata kiranki bakya picking, har bp na ya hau wlh"
Khairiyya tace "Haba durling, yanxu ina tare da yayana kuma yana so ku had'u, kazo ka samei mu a BARWEE mana"
Sabir yace "Haba mss hot, Toh yanxun nan zan shirya nazo, sai nazo kinji bye"
Itama tace bye ta katse wayan
    "Wayyo Allah nah, Allah sa wannan Captain Suraj d'in da Uniform yazo, ai koh ba uniform nasan yana yawo da gun koh pistol,  ohhhh Sabir we gonna catch some fun today"

KHAIREEYYAH(Completed ✔)Where stories live. Discover now