CHAPTER TWENTY ONE

1K 24 0
                                    


    Khairiyya tasha gyaran jiki fiye dana lokacin, tayi kyau kamar ka saceta ka gudu, sai fara'a take, yau itace ranar da za'a d'aura mata aure da man of her dream....
     Ammar kuma Abba ya aiko masa kayan da zai saka, shadda neh fari kal wanda yasha zubi, da ganin shaddan nan ba karamin 6arnan kud'i aka masa ba, Ammar kallon shaddan yake kamar bazai saka ba, zuciyan sa neh yake tafarfasa, ya rasa mei yake masa dad'i, ya zauna a kasan carpet ya fashe da kuka, yana cewa
'"""""I love KIM, I love yhu sooo much, I love you to the square root of infinity, daman a rubuce yake ke ba matata bace, matar mutum kabarin sa, Allah baki zaman lafia a gidan ki KIM, you are my inspiration, there is no hesitation. You are everything to me"""'

Bubbuga kofan akeyi, da sauri ya tashi ya goge hawayen sa ya bud'e kofan, Abba neh da wheelchair nasa, yace
"Haba my son ka shirya mana mu fita, na baka 10mins dan Allah ka shirya", Ammar yayi murmushin dole yace
"Toh Abba gani nan fitowa In Shaa Allah", bayan minti talatin sai ga Ammar ya fito, zo kuga yadda yayi kyau kamar shineh angon, a wajen taron d'aurin auren ya had'u da Zilyadeen wanda shima yasha farar shaddan shi da babban riga, ya juya d'ayan gefen yaga General Suraj a.a, zuciyan sa sai tafasa yake, baisan lokacin da yatashi a taron ba ya silala yabar wajen, yana barin wajen ya shiga side nasa ya d'au key na mota, already daman motar sa yana waje kawai ya fita waje, ganin Motoci dayawa gaba d'aya ya cika anguwar ba yadda zaiyi ya fitar da motar sa ma yaja tsoki, da kyar ya fita bakin titi ya tsaida tricycle yace ya kaisa gida, yana sauka a gate ya shiga gidan su ya d'auka wani key mota ya fisga motar da karfi sai tafiya yake wanda shima kansa baisan ina zashi ba, zuciyan sa yana tafarfasa, hawaye na sauko wa kan kuncin sa..........

     *Bayan d'aurin Aure*

Alhamdulillah anci ansha, Eesha tace kai nana baza a barni a baya ba kinsan ni da kwad'ayi gwara na tashi na bawa ciki nah hakkin sa ina ganin su Kaji da pizza ai inaa, Masoyan Ammar tun suna taya sa bak'in ciki sukaga kayan dad'i ina suma suka baje sai bawa cikin su hakkin sa suke, nidai Nana na kasa cin komai ina tunanin halin da Ammar yake ciki

Da daddare misalin karfe bakwai na dare Amarya Khairiyya tasha wanka, ga kamshin humra da turaren wuta da yake tashi a jikin ta, Ummi ta zauna da yan uwanta suna mata wa'azi sosai, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba dan wa'azin ya shige ta sosai, bayan sun gama nasu Abba ma ya kira ta d'aki ya mata wa'azi akan yadda zata zauna da mijin ta lafia, sai kuka take ta rungume Abban ta tace
"Abba ka yafe mini, ka yafe mini Abba", Abba yayi murmushi yace
"Mamana kece ya kamata nace ki yafe mini, na miki babban laifi, kuma ban ta6a zama dake na for good three months ba kullum ina barin ki a babban gidan nan a hannun strangers, I am so sorry my child", Khairiyya sai kuka take, daga baya Abba yace shi zai kaita gidan ta
    Abba da Khairiyya neh a bayan mota, Khairiyya tana kuka Abba shi kuma sai dialling number Ammar yake, yana ta ringing amma baya d'aukan wayar, can ya kara dialling sai aka d'auka, Abba yace da tsawa
"Ammar yanxu yanxun nan inason ganin ka, kar ka wuce minti goma", shuru ba'a ce komai ba, Abba ya danna wayan a loudspeaker yace
"Ammar baka jina neh" daga can 6angaren wani murya neh yace
"Alhaji Ammar zamu kawo sa gida, ya d'anyi hatsari amma Allah baisa yaji ciwo ba", da sauri Khairiyya ta juya taga Abba zuciyan ta yana bugawa, kar6an wayan tayi a wajen Abba dan ta ganeh muryan daya d'auka wayar, tace
"Kamalu badd ina kuka samei shi, ina Ammar d'in"
"Hajia gashi nan kwance an masa alluran bacci amma nan da awa d'aya zai tashi, a jimtilo muka gansa"
"Ohk please Kamalu ka kawo shi gida"
"Toh hajia an gama", Abba ya juya ya kalle ta yace
"Kinsan su neh", ta d'aga kai, yace "ohk Allah sa baiji ciwo ba kamar yadda sukace", Khairiyya tace
"Ameen"

Gida neh tsararre a anguwar old GRA, gate d'in ma kad'ai abun kallo neh, danna key sukayi gate d'in ya bud'u, sai tafiya suke kamar ba gate suka shiga ba, ganin wani dankararren gate tayi, Abba neh ya mik'a wa Musa driver paper yace ga pin d'in ka sauka kayi unlocking gate d'in, Musa ya sauka ya latsa pin d'in sai murya a gate d'in "Password accepted", Abba ya danna remote gate d'in ya bud'u, wani designer gida neh, wanda ita kanta Khairiyya duk yawon ta a Nigeria bata ta6a ganin gida haka ba sai outside the country, sai tunani take daman ashe Zilyadeen shima ba baya baneh ta kud'i, sai sake sake take a ranta, da suka shiga gidan kuma ta bud'e baki hanci ido tana kallon gidan, Sai fad'a take a ranta Aljannan Duniya, duk tsarin gidan su a fad'in maiduguri sai taga ashe gidan su ba komai baneh, komai na cikin gidan is customize, tun daga kan ceilin har carpet, cushions komai, a cikin gidan wani 6angare daban aka kaita, jibgegen parlour, Abba ya shigar da ita wani d'aki yace
"Mamana nan shineh d'akin ki, kamar yadda kika mini alkawari zaki zauna da mijin ki lafia Toh ki cika alkwari", Abba ya kara mata sabon wa'azi ita kuwa sai kuka take, da Musa zai jasa a kujeran sa Khairiyya ta kama kujeran tana kuka tana cewa
"Dan Allah Abba karka tafi ka barni please Abba", da kyar Musa ya raba ta dashi, zube wa tayi a kasa tana kuka sosai, ga kanta wani tsarawan da yake mata, wata ce wanda baza ta haura hamsin ba tayi sallama, Khairiyya ta d'aga kanta ta amsa, matar tace
"Nice wanda zanna kula da masu aikin ki, nice ogan su hajia, mu zamu wuce side namu saida safiya hajia", Khairiyya tace "yawwa", sai mamaki take, tasan a kullum sukayi hira da Zil yakan ce mata shi a tsarin rayuwar shi baya son mai aiki gashi yanxu har masu aiki aka kawo mata, tun tana jiran ango har tagaji, can ta tashi ta fita a 6angaren ta, sai bin gidan take da kallo, gida neh ya tsaru iya tsaruwa, sai fad'a take toh ina 6angaren Rumaysa, dan ita side biyu Abba ya nuna mata yace mata wannan naki, ya nuna mata d'ayan yace wannan na mijin ki, but bai nuna mata side na Rumaysa ba
Dan Zil ya fad'a mata gida daya da Rumaysa zasu zauna, can ta gaji ta d'au number ta takira shi amma switch off, neman toilet tayi ta cire kayan jikin ta tayi wanka, tayi Sallah, bayan ta idar ta kwanta a kan gado zuciyan ta sai bugawa yake, ta rasa ganeh dalilin da yasa har yanxu Zil baizo ba, Allah sa dai lafia, ta latsa number Abba shima takira shi amma no answer

Can wajen Ammar bayan su Kamalu badd sun kaisa gida, Abba da kyar yasaka sa yayi sallah, bayan yayi sallah yaci abinci, Abba ya kira family doctor su yazo ya duba shi, aka bashi magani yasha, maganin pain reliever neh yana saka bacci sosai, bayan yasha Abba ya saka Musa driver dan ya kaisa gida, da kyar aka shigar da Ammar mota Musa driver yaja motar, to my own suprise gidan da aka kai KIM shi Musa driver yakaisa, ya bud'e gate d'in da pin ya shigar da shi

KHAIREEYYAH(Completed ✔)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang