Mei yayi zafi Rumaysa, tunda bakison Khairiyya ai shikenan, share hawayen ki bazan aure ta ba har sai da yardan ki, har sai ranar da kika furta da bakin ki ehh kin amince, sai ranar da zaki zo gabana kice "Nural Hayat na amince Khairiyya ta zama abokiyar zama nah"....
Rumaysa tace "har duniya ta nad'e bazan ta6a amincewa ba, keep it at the back of your mind yaya Zil, bazan ta6a yarda ka aura Khairiyya ba, kar kace idan ka aure ni shikenan sai yadda kayi dani, ka sani koh da igiyan auren ka yana nan cas uku a kaina a ranar da ka auro Khairiyya toh zan bar maka gidan ka, ka sani yaya Zil, ka saka a ranka, lemme say it one more time keep it at the back of your mind bazan ta6a amince wa ba....
Zilyadenn Yace "naji future wife, zanyi yadda kike so kinji, bazan aura Khairiyya ba tunda baki son ta", tace da ya fiye maka alkhairi, yace yanxu Toh tashi ki samu su Abba kice kin janye maganar yanxu zaki aure ni kinji, tana murmushi tace "toh"
Bayan kwana uku Khairiyya hannun ta ya warke zata fara shiga cikin makaranta dan anyi nesa sosai a lectures, duk tayi sanyi ba kamar da ba,Riga da skirt less ta saka da Hijab dogo har kasa brown colour da dogon takalmin ta da jaka shima brown, yau daga powder sai powder koh kajal bata saka a idon ta ba, daidai zata fita ta ja motarta sai ga Ammar shima zai fita, yace ahh Khairiyya bara na kaiki Makarantan mana, Khairiyya tace
"Ammar you don't have to worry, I can drive"
"Are you sure Khairiyya, kibari na kaiki, umarni nake baki so just shut up your mouth", ta shiga motar sa yaja suka bar haraban gidan, suna cikin tafiya kowa yayi shuru Ammar yace
"Khairiyya zanyi tafiya, zanje na samu su Abba a U.S sai na wuce wajen aiki nah ana nema nah, zan kai like wata shida In Shaa Allah kan na dawo, incase idan anyi auren ki bana nan zan tura miki gift don't worry kinji", sai ga hawaye shar a idon Khairiyya tace
"Ammar har wata shida, Toh ai ni kuma koh zanyi aure saidai mijin ya jiraka har ka dawo, dan bazan yi aure baka nan ba", Ammar yace
"Shikenan My KIM, zanyi attending auren ki In Shaa Allah, share hawayen ki", tana murmushi tace
"Mr Ego sunan nan KIM fa kai ka rad'a mini kuma gashi ya bini, dan nima inason sunan", yayi dariya yace
"Gashi kuwa sunan ya biki, Instagram celeb ba, KIM can you remember lokacin da nake Mexico muna competition wayake da highest followers a Instagram, but nafiki followers, matan Nigeria da son karya, sunga fine boy gashi kuma suna ganina cikin snow kullum da tsadaddun jackets kawai suta following d'ina", Khairiyya ta fashe da dariya tace
"Mr Ego wlhy nafika followers, nifa macece, yanxu ma haka inada 56K followers"
"Ni kuma inada 58K followers"cewar Ammar, Khairiyya tace ita sam bata yarda ba karya yake mata, sanda yayi parking mota a gefe suka d'auka wayan sa suka duba, kuma ehh hakan neh ya fita followers, tace
"Kaii mata dai sunji kunya, da sunga namiji ya had'u ga kud'i kuma suna ganin hotunan shi a kasar waje sai su rikice gaba d'aya suta following", Ammar yayi dariya sosai yace
"Yau ke da bakin ki kike ce na had'u, wayyo naji dad'i"
"Kar ma kaji dad'i Mallam, ironically nake nufi, opposite idan baka san meaning na ironically ba" yace mata "whatever gurl", haka ya ja motar ya shigar da ita har cikin school, ta bud'e motar ta fita kenan Ammar shima ya fita a Motar yaje daf kusa da ita yace
"Khairiyya jirgi na zai tashi karfe sha d'aya, but karkiji komai zan dawo soon, nasan Abba yana zuwa maganar auren ki za'ayi, I am very happy for you KIM, I must say that you're so very lucky, wanda kike kauna shima yana kaunar ki, baki son masu wani, the one you love also love's you back, Allah kara had'a zuciyan ku KIM, Allah barku tare, Allah sa alkhairi neh, I can't hide to you, bazan 6oye miki ba, I must have to say this, *I'M GONNA MISS YOU ALOT KIM*, DO TAKE CARE OF YOURSELF, GOODBYE
Yana gama fad'an haka ya shiga motar sa da sauri ya fisga motar da gudu yabar wajen, ta kasa gaba ta kasa baya sai zubar da hawayen da takeyi, tace da karfi kamar mahaukaciya _I will Miss you more Mr Ego, m gonna miss you more more more more, more than words can say_, kowa ya juya a wajen yana kallon ta, cire handkerchief tayi a Jakarta ta share hawayen ta, ta d'au wayar ta takira Teema, Teema batayi picking call d'in ba, tsoki taja, motar Zilyadeen neh ya tsaya a gaban ta, bud'e mata kofa yayi yace tashiga, ba musu tashiga motar ta gaishe shi ya amsa fuska asake, yace
"Yajiki, da alama kamar kin warke", eh na warke ta amsa mishi
Zilyadeen yace "Khairiyya akwai very important magana da nake so muyi dake, but muje office nawa sai muyi maganan acan " Khairiyya ji tayi zuciyan ta ya buga tace "ohk bakomai"
Bayan yayi parking motar a parking space na staff suka wuce office nasa direct, bayan sun shiga ya bata drinks tasha suka d'an ta6a hira sama sama, Zilyadeen ya gyara zama yace
"Khairiyya maganan da nake so mu tattauna akan Rumaysa neh, Rumaysa taki ta amince, bansan ya abun zai kasance ba But karki damu Khairiyya inda raina zan aure ki, inda raina Khairiyya matar Zilyadeen ce, Inda Raina zamu kasance tare har karshen rayuwar mu..... *(ZIL-KHAIR)*, Khairiyya tace Allah za6a mana mafi alkhairi, karka ji komai yaya zil, koh da Rumaysa bata amince ba zan iya hakura
"Shhhhh Khairiyya karki kara fad'an haka, koh da ke zaki iya hakura ni bazan iya hakura ba, yanxu naji nafara sonki, So na hakika"
Khairiyya tayi murmushi tace "ni zan tafi, inada da lectures bye", yana kiran ta amma koh tsayawa batayi ba tafita a office d'in
YOU ARE READING
KHAIREEYYAH(Completed ✔)
Teen FictionKhaireeyyah is a story of a beautiful, charismatic, rich,stubborn gurl... she got everything she ever want in this world, everything she desires.... But there is one thing that makes her life miserable.....LONELINESS!!!!! And this Loneliness turned...