CHAPTER THIRTEEN

922 24 1
                                    

[

        A ranar Khairiyya tana cikin kunci Rumaysa kuma tana cikin farin ciki, Anyi aure lafia, ba'ayi wani events ba sabida ango Zilyadeen bayaso, daga walima sai walima shima dan Rumaysa ta nace dole sai anyi, a daren Ranar akakai amarya gidan ta, gida neh madaidaici da d'aki uku parlour biyu,kitchen biyu,  komai na gidan unique cos mostly kayan ordering akayi daga turai.....
    Misalin karfe goma na dare Zilyadeen yashigo cikin d'akin Rumaysa da leda a hannu, ya zauna kusa da ita yace Amarya bata laifi koh ta kashe d'an masu gida, itadai Rumaysa fuskan ta rufe da gyale sai sautin kukan ta kawai akeji, dakyar ya lalashe ta taci kaza da drinks daya kawo, bayan sun gama ci ya sakata wanka da alwala shima yayi, bayan nan sukayi sallah suka gode wa Allah daya nuna musu wannan ranar, daga nan Zilyadeen ya fara canza salo, dole Rumaysa tabada kai bori yahau, a daren ranar ya mata alkawari kala kala, daban daban dan Rumaysa tafitar dashi a hankalin sa, a cikin alkawarin harda Ni Mijin mace d'aya neh Rumaysa, bai saurara mata ba har sanda bakin ta ya mutu dan kuka sai sauke numfashi kawai take, nidai nace ya'isa haka naja Eesha muka bar musu d'akin.....

    Washegari da safe Khairiyya da Zaynab suka je gidan Alhaji Ibrahim Muhammad fu'ad , khairiyya tana shiga cikin gidan taga ko'ina kura, ranta idan yayi dubu ya 6aci, ihun kiran sunan Haule, Indo da Dije tafara, sai gasu nan a gaban ta, ta watsa musu kallo tace
"Wannan wani irin iskanci neh, wato dan kunga bana gidan shineh kuka bar gidan haka, daga ku kalla TV sai ku dafa abinci kuci koh" duk dai basu tsaman Khairiyya zata musu zuwan bazata ba, ihu tayi tace
"Ina tambayar ku kuka mini shuru, lalle ku d'in nan, Toh yanxu ku d'au tsintsiya ku share da mopping gidan nan tas, daga kan d'aki na har na Abba, toilets na gidan nan gaba d'aya  ku wanke su tas, idan gidan nan banga yana kyale yana shinning batoh a bakin aikin ku,ku tashi ku bani waje", duk suka tashi a take suka bar wajen, Zaynab tace
"Haba Khairiyya wannan fa bai kamata ba, baki ganin sun girme kine"
"Dan sun girme ni sai mei, ina biyan su nake, kinsan nawa nake biyan su every month kuwa mtswww", Khairiyya da Zaynab suma suka canza kaya riga da wando suka zage suna aiki, su Haule sai mamaki suke yau hajiya Khairiyya dakanta tana aiki, ikon God

A gurguje pls

    _International Airport Maiduguri_

    Ranar monday da misalin karfe hud'u na yamma Khairiyya nagani da Ummi da kuma Zainab acikin airport, sai duba agogo suke duk hankalin su a jagule, Khairiyya sai aikin jan tsoki take, karan jirgin da taji kamar zai toshe mata brain yadawo da ita daga tunanin da tafad'a, ba'afi minti talatin ba wani dogo farin mutum mai kyaun gaske wanda a kalla bazai wuce arba'in da takwas ba tare da Uncle Hisham dukkan su rike da akwati a hannu, Khairiyya da gudu taje ta rungume mutumin tace Abba nah I miss you so much tana kuka, shima ya rungume ta yace I missed you more my baby, haka ta kankamei shi shi sanda Ummi tace
"Haba Khairiyya ai kya bari yasha iska" duk sukayi dariya, Uncle Hisham yace
"KIM kinga Abban ki shine koh gaisuwan nan babu", Khairiyya tace "so sorry uncle", yayi dariya yace nidai kam nayi fushi Gaskia.... Gidan Uncle Hisham suka wuce, bayan sunyi wanka sun ci abinci sun huta Abba yace zai tafi gidan sa, Uncle Hisham yayi yayi dashi ya tsaya amma yace shi sam a gidan sa yake son kwana, haka Abba da Khairiyya suka shiga mota suka dawo gida, masu aiki sai zuwa kwasan gaisuwa suke, yau maigidan Oga ya dawo gida after two years, Abba da Khairiyya sunkai karfe biyun dare suna hira, Abba yace
"Baby nah yanxu fa karfe biyu kiyi sallah ki kwanta bacci koh", Khairiyya tace eh kaima bara na barka ka huta, gudnyt Abba nah. ... yace gudnyt babynah

       Sati d'aya shar ana cin Amarci, tun ranar da aka d'aura masa aure da Rumaysa bai kira Khairiyya ba, Khairiyya ranta yayi mugun 6aci takira sa ranar auren sa ta masa congrat amma baiyi picking call d'in ba kuma bai kirata ba tace wato dan yayi aure shineh harya manta dani, lalle kam zanyi maganin sa
Suraj kuma tun ranar da Abba yazo kullum yana sintirin zuwa gidan, haka har suka saba da Abba sosai har zama suke suyi hira, Abba yana kaunar yaron sosai idan Suraj yayi kwana biyu baizo gidan ba har Abba yana kiransa a waya yaji koh lafia, sosai suka saba dashi, yanxu ma Khairiyya ta sake da Suraj sosai, duk mai kaunar Abban ta toh itama tana kaunar sa...... Ammar har yau bai kirata ba, ta kar6a number wayansa a wajen zaynab idan takira sa baya picking call d'in, Ammar yayi mugun 6ata mata rai, wani dogon tsoki taja tace Ammar zanyi maganin ka, Khairiyya zaka wulakanta koh, d'au wayar ta tayi ta turawa Ammar text message kamar haka
_mtswwwwwwww GO TO HELL, JERK_

KHAIREEYYAH(Completed ✔)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora