NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
SANADIN HA'DUWAR MU
©Pharty BB(2)
Ajiyar zuciya ya sauke bayan doguwar tunanin daya fad'a tare da share hawayen fuskarsa daya sauko, fita yai a dakin yayi kofar gida dai-dai lokacin Samha da Laure sun iso gidan da gudu ko wacce da Allonta a hannunta, har kasa suka durkusa suka gaishe da mahaifinsu kafin suyi cikin gida, d'akin iyayensu suka shiga, nan Ummu tayi turus ta tsaya ganin Innarta bata kwance inda ta saba ganinta, hijab nata ta cire ta yar ta fita waje gurin mahaifinta, da gudu tayi gurinsa tana tambayarsa.
"Baffah ina Innata?"
Hannunta ya rik'o ya zaunarta kusa da shi can yace.
"Ummuna kinsan wacce tazo ranar."
Da sauri ta daga masa kanta.
"Yaushe?"
"Kwanaki biyu da suka wuce."
"Addah Salamatu, Addan Innata."
"Ya akayi ki kasan Addar tane?"
"Innah na fad'amin tana da yayu da kanne kuma naga suna kama da Innah ta."
"To kiyi hakuri yau tazo ta d'auki Innarki sun tafi garinsu dan ayi mata magani ta samu lafiya, watarana zamuje kinji."
"To Baffa har zuwa yaushe?"
"Wani lokaci, jeki gida zanje wajen maigari."
Tashi tayi ta shiga cikin gida, hanyar dakinsu tayi da karfi taji ance Ke!!
Cikin sauri ta juyo, Abulle ce tsaye gefenta Dije, da sauri tazo ta durkusa jikinta na rawa tace.
"Gani Dada."
Wani kallo ta watsa mata.
"Tashi maza ki hura wutancan ki d'aura tukunya kizo kiyi tankad'e."
Da sauri ta tashi ta harhad'a itacen batama iya ba ta kyerta ashana har d'an yatsarta ya kone, dakyar ta hura wutan ta cika tukunyar da ruwa ta daura ta rufe, gurin da taga an ajiye tankad'en garin masar taje ta d'auka ta zauna tana tankad'ewa duk yazama biski dan inda wannan sau uku ana tankad'esa asamu kad'an na girkawa, yauma kam dakyar ta samu ta cire na tuwon yau ta ajiye a gurin ta tashi tabar gurin ta shige d'akinsu, bincike ta fara a d'akins har ta gano inda Innarta ta ajiye wani sarkanta na murjani, d'auka tayi ta boye cikin ghana most go dinta inda nanne tsummokaren kayanta suke ciki.
Kwanciya tayi ta fara kuka a hankali dan yunwar da take ji, tin d'umamen safe data ci bata k'arasa komai a bakin ta ba gashi har karfe biyar tayi, sai da tasha kukanta ta koshi kafin ta tashi ta fita lokacin Abulle ta gama abinci harta kashe garwashin tana son zuwa rokonta tana tsoro haka ta hakura ta d'auki tulunta ta nufi rafi.
A hankali take tafiya dan yunwar da take ji haka ta d'ibo ruwanta ta dawo kafin ta gama magriba tayi, alwala tayi tai sallah ta zauna bakin kofa taji ko Abulle zata kirata ta karbi abincinta shuru, ganin shurun yayi yawa ga yunwa na cinta yasa ta leka wajen ba kowa a filin gidan, kofar dakin Abulle taje kamar mai jin tsoro tace.
"Dadah."
"Na'am uban me kike nema da daren nan."
"Dadah yunwa nake ji banga tuwona ba."
Dariya Abulle tayi.
"To dan kaniyarki dama darajar uwarki da ubanki yasa nake baki yanzu ko kinga uwarkin tabar gidan, ubankin baya nan saiki nemi abinda za kici dan ni Zainabu Abu baki kai na miki tuwo kina zaune sannan ki bude ciki kici ba, gafara ki ban guri."
Kuka Ummu tasa haka ta tashi taje gurin girkin nasu ba komai sai tukunyan da suka yi tuwon shima an jikashi da ruwa, d'aki ta koma ta fara kuka can taji motsi lekawa tayi da sauri taga Baffan tane, fita tayi taje gurinsa ta rik'o hannunsa cikin muryar kuka tace.
"Baffa yunwa nake ji Dadah bata ban tuwo ba."
Hannunta yaja ya d'auki tabarman kaba ya shimfida ya zaunarta ya shiga d'akin Abulle sun baje itada yayanta sai hira suke.
"Kawo min abincina waje yau."
Ya fad'a yana fita a d'akin, kwanon tuwonsa ta d'auka ta fita waje dashi yana zaune kusa da Ummu, ajiyewa tayi ta koma d'akinta, bayan tafiyarta ya jawo kwanon ya bud'e ya tura gaban Ummu yace.
"Kici Badd'o."
Bata jira ya k'arasa ta matso ta rike kwanon kamar za'a kwace mata ta fara durawa a cikinta, sai da taci tayi kat tace.
"Baffah kai fa."
Murmushi yayi yace.
"Ni naci abinci a waje kawo sauran in cinye."
Tura masa tayi ta tashi ta wanke hannunta ta dawo ta zauna kusa dashi yana cin guntun abincin data rage, kwanciya tayi tin tana amsa masa har bacci ya d'auketa a gurin, bai koshi ba ya k'ara da ruwa ya d'agata ya kaita d'aki ya fito ya wuce d'akin Abulle tana zaune, kallonsu yayi.
"Dije yau baza kuje gidan Lami din ba?"
Bai k'arasa ba caraf Abulle ta cafke.
"Ai d'ayan d'akin zasu koma tinda ita Muniran ba ranar dawowarta."
Shuru yayi can yace.
"To shikenan."
A daren suka jida kayansu suka koma d'akin Munira kan gadon Dije ta haye taba Laure katifarta wanda duk ta tsomare, ta sauko da Ummu k'asa tayi kwanciyarta, shikam Baffah bai so haka ba haka suka kwana.BATAGARAWA
Washegarin da suka iso aka taru gaba d'aya Dangin a fada har Babbar yayar Munira ta iso da take Katsina, nan suka tattauna tsakaninsu suka yanke shawarar babban yayansu dake Kaduna zai tafi da ita da Addah Habiba da batada aure dan kula da Munira duk da matarsa tana nan, da haka su Addah Salamatu ta harhad'a musu abinda za suyi amfani dashi a ranar suka 'dauki hanya.Munira itace y'a ta biyar gurin iyayayenta, Babanta shine sarkin kauyen Batagarawa dake karkashin k'aramar hukumar jihar katsina, yaransa shida, biyu maza, mata hudu, Babba shine Kawu Saminu sai Kawu Idrisa, Kawu Saminu yanada mata da yara biyu Mukhtar da Aminu, yana zaune cikin Kaduna, sai Kawu Idrisa yanada mata da yara hudu shikuma a Funtua yake, sai Adda Halima tana aure a Kaduna sai Adda Salamatu tana aure a Daura sai Munira sai Habiba, Adda Halima duk cikinsu mijinta yafi kudi da wadata dan duk cikinsu ta fita daban bata son shiga cikinsu haka kuma tinda yaranta suka fara girma ta fara d'auke kafarta, sai ita Munira SANADIN HAD'UWARTA da Baffah ya aureta ya kaita kauyensu wanda aurensu ba k'aramar gwaggwar maya aka shaba kafin danginta su amince.
Wannan kenan!!!PhartyBb.Wordpress.com
YOU ARE READING
SANADIN HA'DUWARMU
RomanceLabarin matashiyar budurwa Ummu A'isha, labari mai cike da tsantsar tausayi da rashin gata, soyayya da rashin taimako.... Abubakar Sadeeq wanda ya taimaki rayuwar Ummu bayan wahalhalu da tasha, ya ba ta dukkan taimako kafin ya watsar da lamuranta. ...