NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.
SANADIN HADUWARMU
©Pharty BBWattpad @PhartyBB
22
Misalin karfe tara na safiyar Litinin, garin an tashi da tsananin sanyi kasancewar lokacin tsakiyar hunturene, ma'aikata da dama suna faman tafiya wajen aiki, yan kasuwa suna kok'arin tafiya wajen sana'arsu.
Zaune yake gefen Mahaifinsa kansa a k'asa, yafi minti goma yana son fad'a masa takamammem abinda ya kawosa wajensa amma yana tsoro ya zai kar'bi abin, ya zai fuskance sa ya gane nufinsa, taimako yake son yi ga rayuwarta, yasan abinda zai yi shi kad'aine zai dawo da farin cikinta, duk da, da wuya ta samu sauran farin cikin rayuwarta amma yana fatan samar mata shi nan gaba kad'an.
Kallonsa Mahaifinsan yake tin bayan da suka gaisa yasan bakin d'ansan da magana, murmushinsa na manya yayi yana dafa kan d'ansan.
"Ya akayi Sultaan, na kula tin zamanka akwai magana tattare da kai."
K'ara k'asa da kansa yayi cikin fad'uwar gaba da kyar ya iya bud'e baki yace.
"Abba dama..dama dai..."
"Dama dai menene, feel free and tell me."
"Abba dama na samu matar da zan aure, amma ban san ya zaka d'auki maganar tawa ba."
Murmushi Abbansan yayi a 'karo na biyu.
"Akan maganarnan shine kake jin kunyan fad'amin, in dai har yarinyar nada asali mai kyau da tarbiya ai shikenan Allah zaba mana abinda yafi alheri."
"Ameen ya Allah."
Cewar Sultaan k'asa-k'asa.
"Y'ar ina ce?"
Dum zuciyar Sultaan ya buga, dama yana tsammanin tambayarnan a ko wani lokaci.
"Abba bansan y'ar ina bace asalima boyemin asalinta take, ba wata bace Ummu A'ishat."
"Ummu y'ar aikin gidannan kake nufi."
"Eh ita Abba, Abba so nake in taimaki rayuwarta in sadata da farin ciki kamar yanda kowani 'Dan Adam ke buk'ata, tana buk'atar taimako, wanda ya kawota bai damu da ita ba."
Shuru Abbansan yayi shikam yasan bai isa ya hanasa ba, sannan bai isa yace ya aureta ba, in Allah yayi matarsa ne dole sai ya aureta in ko akasin haka to sai dai ya hakura.
"Kaje Office naka yanzu zuwa anjima da dare zan nemeka."
"To Abba nagode."
Fad'in Sultaan na tashi, da fitarsa sallama yama Maminsa ya wuce.
A office din ma ranar kasa duba marasa lafiya yayi har aka tashi addu'a yake tayi akan Yayan nasan, dan ya kula da take takensa akan Ummu amma duk tunaninsa ya kasa gano menene.
Da yamma karfe hudu ya baro Office isansa gida a wajen parking ya ga motar Sadeeq, bayan yai parking ya fito ya wuce babban falon gidan, Rahma ce da Mami sai Sadeeq a falon bayan sun gaisa ya wuce d'akinsa, wanka yayi ya canza kaya kan ya fito falon Rahma ta zubo masa abinci.
Abinci yaci kad'an ta d'auke saura, nan su kaci gaba da hiransu na 'yan uwa har Abbansu ya dawo, bayan sun gaisheshi ya wuce 'dakinsa, Mami tabi bayansa.
Kiran Sallar magribane ya fito dashi suka had'u dashi da y'ay'ansan suka wuce masallaci, bayan sun idar suka dawo a falon Abbansu suka yada zango, da sallama Abbansu ya bud'e gurin kafin ya fad'awa Sadeeq buk'atar Sultaan, inda suke so ya fad'a musu garin Ummu dan zuwa binciken Asalinta tinda shine silarta na zuwa gidan.
Shuru Sadeeq yayi da jin maganar Abbansa kansa a k'asa.
"Abba naji komai amma ina mai bada hakuri akan buk'atar Sultaan ba zai yu ba."
"Ko zaka fad'a mana dalili?"
Kallonsa Sadeeq ya kai kan Sultaan kafin ya watso masa tambaya.
"Shin ya halarta Mace ta auri maza biyu?"
Girgiza kansa Sultaan yayi cikin dakewa yace.
"Ah a."
"Good, sannan shin ya halarta Namiji ya auri matar aure."
Nan kam girgiza kai Sultaan ya sake yi dan ya kasa furta ko kalma d'aya.
"In kasan har haka bazai tab'a faruwa to ba zai faru ba, dan Ummu da kake ikirarin zaka aureta, matar aurece akwai igiyar aure uku a kanta."
Gaba d'aya shuru falon yayi Abbane yayi karfin halin magana.
"Sadeeq auren waye akanta?"
"Abba kayi hauri bisa boyema da nayi, nayi hakanne badan komai ba sai dan gudun ban san ya Mami zata d'auki auren ba, nima kaina bada son raina aka d'aura auren ba sai dan tana bukartar tsananin taimako a lokacin...."
Nan ya kwashe labarin farkon SANADIN HA'DUWARSU ya fad'a musu bai boye musu komai ba hatta da zamanta gidan magajiya.
Daga Abba har Sultaan sun tausayawa rayuwar Ummu da irin rashin gata da take fama dashi, Sultaan ji yake zuciyarsa tayi zafi da jin irin rayuwar da tayi da wanda yanzu take ciki na rashin halin ko in kula da Yayansan yake mata, hakan kuma yake ikiraran 'kiranta matarsa.
Tashi yayi ransa a bace yana cewa.
"Abba nagode dama duk tunani bai taba nunamin da ita din matar aure bace, duk da wani hali da wasu abubuwa da Ya Sadeeq ke nunawa akanta ban taba zaton haka bane, amma ya sani k'ani na auran matar Yayansa idan har ba abinda ya shiga tsakinsu."
Tashi Sadeeq yayi a fusace yana watsawa Sultaan wani kallo.
"Me kake nufi?"
Shima Sultaan cikin b'acin rai yace.
"Abinda kaji shi nake nufi, kasa yarinya gaba ka rabata da 'yan uwanta da kowa nata akan kana tak'ama da cewa ka taimaki rayuwarta, to ka sani ni Aliyu Sultaan sai Ummu ta zamo matata in dai ina numfashi."
Yana gama fad'ar haka yabar falon, Sadeeq zai bi bayansa Abba ya dakatar dashi.
"Zonan Sadeeq."
Baya ya dawo ya zauna yana huci.
"Kar kuban kunya mana duk zamanku da shak'uwarku mace na shirin shiga tsakaninku, nasan Sultaan b'acin rai ya sashi haka amma nanda wani lokaci zai sauk'o, abu na karshe jibi ka shirya kai da Ummu za muje garinsu dan yin bincike a kanta."
Ajiyar zuciya Sadeeq ya sauke.
"Allah kaimu Abba."
"Ameeen, zaka iya tafiya."
Fita yayi a falon ko sallama bai ma Mami ba yaja motarsa yabar gidan, a ransa ya kudiri a aniyar d'an tazarar da ya rage Sultaan ya samu Ummu sai ya kawar dashi a daren yau, tinda dashi yake ikirarin sai ya aureta, wanda faruwar hakan yasan zai sa aure ya haramta tsakaninsu sai ko bayan ransa.
Yana isa gida bayan yayi parking motarsa ya fito ya nufi falon, a nan ya tarar da Biebie na kallo gabanta Laptop nata ne, rufewa tayi ta isa wajen ta rumgumesa.
"Wellcome home My Dear."
Kanta ya shafa yana k'irk'iran murmushin dole.
"Ya gida."
"Lafiya lau, muje kayi wanka in kawo maka abinci."
Kai ya d'aga bata bai jin zai iya magana, da shigarsu d'akin wanka yayi ya shirya da taikamon Biebie, kafin su fito ta kawo masa abinci, lomarsa ta farko ya gane d'and'anon abincin bana Biebie bane, kad'an yaci ya ture sauran ta d'auke ta dawo ta shige jikinsa.
A haka suka d'anyi kallo suka wuce d'akunan baccinsu, wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta wuce d'akinsa, kwanciya su kayi shikam kasawa yayi sai da ya tabbatar tayi bacci kafin ya lullubeta da bargo ya fita yaja mata kofar.
D'akin Ummu ya shiga wutan d'akin a kashe sai hasken farin wata daya hasko d'akin kad'an, can kan gado ya hangota tana bacci, lallab'awa yayi gurin gadon ya zauna ta inda fuskarta yake.
Ido ya zuba mata, tabbas yasan yaci amanar daya d'auka ya kasa taimaka mata, ya rabata da kowa nata dan ya taimaka mata amma ya kasa, bawai bashi da halin taimakon bane kawai shi kansa ya rasa mai yasa ya kasa aiwatar da hakan.
Hannu yasa saman fuskarta ya gyara kitsonta na kalaba daya rufe mata gefen fuska, kyakkyawar fuskarta ya sawa ido, boy'ayyen kyau gareta wanda ba lalle in ka kalleta sau d'aya ka gane hakan ba, sai ka saka mata ido sosai.
"Ayeeshat."
Ya k'ira sunanta yana d'an shafa fuskar, motsi tayi tana gyara kwanciyarta, cikin bacci taji ana shafa fuskarta ta farka a zubure tana kok'arin sauk'a a gadon ya rik'ota, ihu za tasa ya toshe bakinta da hannunsa.
"Ke nine."
Ya fad'a yana rik'eta da kyau, duk da ta ganesa kok'arin kwace jikinta take, yaki sakinta ya k'ara rik'eta da kyau, kuka tasa masa dan tinda suke da ita bai tab'a mata haka ba.
Cikin kuka tace.
"Dan Allah ka barni Ya Sadeeq."
Ko kulata bai yiba ya kwantarta ya kwanto jikinta yana rik'e da ita yaja musu blanket. Wasanni ya fara da jikinta a haka ya samu ya rabata da kayan jikinta. Ummu sai kuka take ganin wani sabon al'amari tsakaninta da Yaah Sadeeq, duk yadda ta so hana shi da kwatar kanta tana ji yana mata abubuwan da suka fi ƙarfinta.
Yaah Sadeeq kam bai san tana yi ba ya faɗa duniya sabuwa, sosai yake juyata son ransa, yarinya ƙarama da ta nema fitarsa hayyacinsa da abubuwan morewa na jikinta.
Daren ranar duk kok'arin Ummu da kuka da roko da magiya ba wanda ba ta ma Sadeeq ba, amma ko a jikinsa haka yabi da ita ya nema hanyar sa ya shiga da ƙyar don kamewa gurin, ya maida Ummu cikakkiyar mace, da kyar kafin ya saketa lokacin banda ajiyar zuciya ba abinda take yi dan ta jik'ata ba kad'an ba.
Wahallalen baccine ya d'auketa shiko ya tashi ya bar d'akin, d'akinsa ya shiga sai da ya tsarkake jikinsa kafin ya iya kwanciya shi ma baccin ya d'aukesa cike da farin cikin yanayin da ya samu Ummu cikakkiyar budurwa a matse gam.Washegari da safe karfe tara Biebie ta fito, ganin falon yanda ta barshi jiya shiya b'ata mata rai ta wuce kitchen nan ma ba a gyare ba balle har taga ta d'aura breakfast.
Cikin masifa ta fito ta nufi d'akin da Ummu take, banka kofar d'akin tayi ta shiga, kan gadon da take kwance ta isa wajen ta daka mata duka a baya.
"Shegiya tashi, uban wa zai miki aikin gidan kinzo kin wani baje kina bacci."
Cikin hawaye Ummu ta mik'e gaba daya ji take ta tsani rayuwarta, ta tsani Sadeeq da kowa nasa, ya cuceta yaci amanarta.
"Tashi ki fita ki gyaramin gida kafin naci mutuncinki."
Da kyar da azaba Ummu ta mike ji tayi kafafunta sun kasa d'aukarta ta koma ta zauna.
Nan fa Biebie tasha jinin jikinta ganin abinda idon ya kai kallo, me zata gani? Me yake shirin faruwa? Me yarinyarnan take nufi?Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummu Safwaan)
PhartyBb.WordPress.com
KAMU SEDANG MEMBACA
SANADIN HA'DUWARMU
RomansaLabarin matashiyar budurwa Ummu A'isha, labari mai cike da tsantsar tausayi da rashin gata, soyayya da rashin taimako.... Abubakar Sadeeq wanda ya taimaki rayuwar Ummu bayan wahalhalu da tasha, ya ba ta dukkan taimako kafin ya watsar da lamuranta. ...