NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
SANADIN HA'DUWARMU
©Pharty BB( 12 )
Wani wawan fisga taji an ma hijab din jikinta ta baya, a tsorace ta juyo kan ta bud'e baki tayi magana taji saukar tagwayen mari masu rai da lafiya, kafin tayi kwakkwaran motsi taji an rufeta da duka, dukanta 'yan matan suke tako ina tana durkushe tasa hannunta tana karewa tare da basu hakuri duk da bata san laifinta ba.
Mami ko fa'da take tana k'ara yi.
"Ku dake y'ar banza, Karuwa ce, a cikin gidana zaki nunamin karuwanci, dama nasan tsintacciyar mage bata mage, yau sai kin fita a gidan nan."
Sai da su Biebie su kaga Ummu taji jiki kafin suka kyaleta, Mami taja hannunta tayi bakin get da ita sam sai tabar mata gida.
"Musa bud'emin kofar nan."
Wanda aka 'kira da Musa yana shirin bud'e get aka danna hon, lekawa yayi ganin mai yin hon din ya sashi wangale get din gaba daya ya shigo da motarsa, bai 'karasa wajen fakin ba yai fakin ya fito da sauri ya nufi wajen su Mami cikin tsananin mamaki.
"Mami lafiya?"
Wani kallo Mami ta watsa masa.
"Ina lafiya ka kawomin karuwa har gida."
Dum yaji maganar ta shigesa.
"Mami karuwa kuma?"
"Kamata mu kayi tana shiga d'akin Isa mai wanki, inba karuwa wace 'ya macece zata shiga 'dakin namiji baligi."
Cewar Biebie cikin sauri.
Kallonsa ya maida kan Ummu da take durkushe tana kuka, takawa yayi ya isa gurinta, zata matsa yasa kafa ya take kafarta, tsananin zafin da taji na shigarta ya sata sakin wani kuka tama kasa magana.
"Sadeeq fitarmin ita a gida."
Fad'in Mami tana kallonsa.
Yanda yasa mata ido yana kallo sai kuka take, shi yasashi sa hannu ya d'agota ya nufi cikin gida da ita, shan gabansa Mami tayi cikin tsananin mamaki.
"Ina zaka kamun ita?"
Kallon Mami yayi a nutse.
"Mami AMANATA CE, sai na tabbatar da gaskiya kafin in yanke hukunci."
"Sadeeq kanka d'aya kuwa."
Murmushi karfin hali yayi.
"Mamina lafiyana lau, tambaya kawai zan mata."
Yana fad'ar haka yayi cikin gida bai tsaya a babban falon gidan ba ya wuce d'akinsa da ita, rufe kofar yayi har dasa key kafin ya zaunarta gefen gado yaja stool ya zauna saitinta yasa mata ido yana kallon yanda take kuka, tsaki yaja cikin fad'a-fad'a yace.
"Rufemin baki karna bugesa."
Tsit tayi sai hawaye dake zuba tana sa bayan hannunta tana sharewa.
Kallo ya kare mata tsaf shikam yasan ya d'aukowa kansa jaraba, tin shigowarta rayuwarsa yake samun matsala.
"Abinda su Mami suka fad'a gaskiyane kin shiga d'akin Isa?"
Shuru tayi kafin a hankali ta d'aga masa kanta, ido ya zaro cikin tsoro da kaduwa ya tamabayeta.
"Dagaske, me ya kai ki?"
"Anti Biebie ce ta aikeni."
"What?"
A tsorace taja baya jin tsawar da yayi kamar zai daketa.
"Me ta aikeki yi wajensa."
Shuru tayi kafin ta kwashe komai ta fad'a masa tin daga tana wanke-wanke Biebie ta kirata ta ta sata aiki da karb'an sauran Omo nata da tayi a gurin Isa.
Shuru yayi tabbas wannan abin sharrin Biebie ne kuma zai yi maganinta in banda neman ta kullawa yarinya sharri me na karban guntun Omo da sabulu wajen mai wanki duk Sabulu da Omon gidannan, ransa in yayi dubu ya baci.
Kallonta yayi kafin ya tashi yace.
"Biyoni."
Fita yayi a d'akin tana binsa har falon Mami, zaune ya gansu suna kallo hankalinsu kwance, yana zuwa wajen Biebie bai yi wata wata ba ya kwashe Biebie da mari wanda ya sata sakin ihu har Mami ta fito daga bedroom nata, zai sake kai mata wani yaji ance.
"Kul Sadeeq." Daga bakin kofar falo.
Juyawa yayi ya kalli mai maganan, Mahaifinsune, 'karasowa yayi cikin falon yana zama a d'aya daga kujerun falon, Biebie ko tashi tayi zata bar falon cikin kuka ita dasu Rahma taji muryan Abbansu na cewa.
"Dawo nan Biebie, kai ma Sadeeq zauna, Halima(Mami) kema zauna magana za muyi."
Gaba d'aya guri suka samu suka zauna, kallon Sadeeq Abba yayi yana cewa.
"Mai ta maka kake mata irin dukannan? baka san bakyau dukan mace ba."
Kansa a katsa ya kwashe komai ya fad'awa Abba kamar yanda Ummu ta fad'a masa da yanayin da yazo ya samesu.
"Wacece kuma Ummu a gidannan?" Cewar Abba yana dube-dube.
"Wata tsintacciyar ya kawo mana."
Fad'in Mami cikin sauri.
"Ina take?" Abba ya tambaya.
D'ago kai Sadeeq yayi ya kalli kofar falon bata nan bata cikin falon.
"Abba bari in kirata." Cewar Sadeeq na kok'arin tashi.
"Jeka 'kirata."
Tashi yayi ya fita ya sauk'a falon k'asa ya nufi d'akinta, tana zaune tana kuka jin an shigo 'dakinta ya sata d'ago idonta da suka yi ja dan kuka.
"Biyoni, kuma ki tsaya ki k'i shiga ki juya sai na 'bata miki rai."
Fita yayi ta tashi tabi bayansa har falon da sallama ya shiga ya zauna itama ta shigo cikin sallama ta rakub'e ta zauna.
Kallonta Abba yayi.
"Kece Ummu?"
Kanta ta d'aga cikin sauri.
"Me had'inki da Biebie, ma'ana mai ya had'aku da ita har ya kai Sadeeq ya mareta a kanki."
Shuru tayi kafin ta kwashe komai ta fad'a, gaba daya falon shuru aka yi cikin sauri Biebie tace.
"Abba wallahi sharri tamin."
"Rufemin baki." Ya fad'a a tsawace, dan yasan Biebie da raina mutum musamman na 'kasa da ita.
Shuru tayi tana ta hararan Ummu da kanta ke k'asa.
Nan Abba yayi musu fad'a sosai kafin ya sallamesu ya dakatar da Sadeeq, fad'a ya masa sosai akan saurin yanke hukunci, nan kuma ya nemi sanin wacece Ummu?
Sadeeq bai boyewa Abbansa komai ba ya fad'a masa sai dai ya boye masa da aure tsakaninsu, Abba ya tausayawa rayuwar Ummu, sun dan dade suna hira da Sadeeq kafin ya sallamesa ya wuce d'akinsa.Can d'akin Mami kam kuka Biebie tasa sam sai tabar gidan akan y'ar aiki za'a mareta dan anga ita ba y'ar gidan bace, ai itama tana da nata iyayen da 'kannai, gidansu zata tafi, dakyar Mami ta iya lallashinta tare da mata alkawari ta 'kara hakuri nan da shekaru biyu ta gama makarantarta ayi bikinsu ko baya so sai anyi, ballema lokacin tana sa ran tayi duk wani ko'karinta na 'ya mace taga ta jawo hankalinsa, sannan ta fita harkan y'ar aikin nan, da wannan ta samu ta hakura.
Sadaukarwa ga ummu Aisha(Ummi Safwaan).
PhartyBb.wordpress.com
YOU ARE READING
SANADIN HA'DUWARMU
RomanceLabarin matashiyar budurwa Ummu A'isha, labari mai cike da tsantsar tausayi da rashin gata, soyayya da rashin taimako.... Abubakar Sadeeq wanda ya taimaki rayuwar Ummu bayan wahalhalu da tasha, ya ba ta dukkan taimako kafin ya watsar da lamuranta. ...