NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.
SANADIN HADUWARMU
©Pharty BB( 9 )
Da dare su Hauwaty suka dawo daga gidan Uncle nasu Baban Biebie, duk da Momyn Biebie tayi-tayi ta zauna mata tak'i ta biyo Hauwaty suka dawo, nan Rahma ta kwashe komai da Ya Sadeeq ya d'auka ta fad'a musu.
Wani uban tsalle Hauwaty tayi daga kwanciyar da take, dama duk cikinsu ta fisu rashin kunya, sai Biebie kuma girman kai da wulakanci, Rahma ko zigine da ita.
"Kan uba fatan bai tab'amin kaya ba?"
Cewar Hauwaty tana bud'e gefen kayanta.
"Bai tab'a ba, dan sun mata yawa ina ga shi yasa yak'i yace a bud'e."
"Tab Allah yaso kowa wace shegiyace da wallahi duk ranar data sa sai na cire mata na mata tsirara a gidannan sai dai ya kasheni."
"Ni ko shida ya d'auki hannu ya d'auka ya bata, shi zai 'dau hannu ya bani kudi na siya."
Fad'in Afnan tana kwanciya ko a jikinta dan tasan meta shirya masa.
Daren ranar ma dole yasa Rahma takai mata abinci, yace mata kuma in taci ta fito da plate din duka.
Kamar zata zubar haka ta d'auka abincin sai da ya daka mata tsawa.
"Kika zubar dashi zan taka ki a anan gurin, rik'e mai kyau."
Kuka ta kusa sawa ta d'auka ta kai mata ta kudura a ranta sai ta muzguna mata kamar yanda tasa yayanta yake takura mata.
Da misalin karfe tara da rabi da minti biyar na dare (9:35pm), Mamine da Sadeeq sai Hauwaty suna zaune saman dining.
"Abba ko kasan Biebie suna da bikin kawarta wani sati."
Mami ta fad'a tana kallonsa yana cin abincinsa.
"Ban sani ba."
"To yanzu ka sani gobe ka d'auketa kuje ta siya duk abinda take bukata."
"Zan bata dai kudi ta siya abinda take so, amma ba inda zan kaita danni ba driver nata bane."
"Ko baka zama yanzu ba gaba kad'an zaka zama."
"Me kika ce?"
Ya fad'a yana kallon Hauwaty da tayi magana k'asa-k'asa.
"Ni bance komai ba." Ta fad'a a tsorace dan tsammaninta bai ji abinda tace ba.
Gurinta yayi ganin ya nufota ta tashi zata gudu ya fincikota ya watsa mata mari.
"Yaushe na fara wasa dake ni sa'an kine."
"Kayi hakuri ni wallahi bance komai."
Mari zai sake kai mata Mami ta rik'o hannunsa.
"Ya zaka dinga dukarmin 'ya a gabana, karya tayi ne?"
Sakinta yayi ya haura sama ya rufe kofarsa da karfi, Mami ce ta lallashi Hauwaty kafin suka wuce d'akunansu.Washegari karfe takwas ya sauk'o yayi breakfast nasa ya wuce office nasa inda yake aiki.
Da karfe biyu da mintuna na rana ya baro wajen aikinsa ya dawo gida, kamar yanda ya saba yana dawowa d'akinsa yake wucewa yayi wanka ya canza kaya ya sauko cin abinci haka yauma, yana zaune kan dining, su Biebie suka fito cikin shirin fita sun sha bak'aken dogon riga, bayan sun ma Mami sallama zasu fita ya 'kira sunansu ta hanyar daka musu tsawa.
"Hauwa, Rahma da ke Biebie kuzo nan."
Dawowa su kayi suka zauna saman kujerun dining din, sai da ya gama cin abincinsa ya kallosu tare da buga tsaki.
"Ina zaku?"
Caraf Biebie tayi magana.
"Shopping kasan bikin k'awarmu Zee ya kusa."
"Allah ko."
"Eh ko zaka kaimu Yayanmu."
Wani kallo ya watsa mata kafin ya tashi, can ya dawo suna zaune yanda ya barsu, kud'in hannunsan dubu goma ya watsawa Biebie.
"Ga kudin da kika ro'keni kin san ni ban gaji roko ba."
Yana fad'ar haka ya fita a falon, bakin ciki da Biebie ta shiga baya misaltuwa duk da yanda take jinsa a ranta bata son wulakacin da Ya Sadeeq ke mata, a sanyaye ta kwashe kudin kafin suka fita Hauwaty tayi drivern nasu suka fita.
Ummu ko a ranar ta fara aiwatar da ayyukanta cikin gidan, tsakaninta dasu sai dai gaisuwa shima sai sunga dama, 'yan matan ko ba magana su sata wannan in tayi ba dai-dai ba sun dinga mata fad'a.Sati biyu da zuwanta ta fara kwarewa a aikin da take yi, duk tsawon kwanakin bata 'karasa Sadeeq a ido ba, safe zata farka in tayi sallah tayi wanka da brush kamar yanda Ya Sadeeq yace tana yi, inta idar da Sallah ta fito ta shiga kitchen ta taya Iyamee mai aikinsu dan aikace-aikace in sun gama ta wanke kwanukan da suka 'bata ta goge kitchen din sai ta wuce 'dakin yan matan ta gyara ta share ta goge ta wanke band'akin, tasha wuya kafin ta kware da aikin.
Bangaren ci da sha ba laifi da zaran sun gama girki Iyamee zata dib'a mata taje 'dakinta taci.*****
Yau (Weekend) hutun karshen mako, tin daren jiya ciwon baya ya sata gaba motsi ka'dan tayi ya dinga ciwo, bayan ta idar da Sallar asuba dakyar ta kwanta akan abin sallar dan bayan ciwo yake sosai.
Karfe tara da mintuna taji ana buga kofar kamar za'a balla, dakyar ta iya tashi abinda ta gani a jikinta shiya mutukar tsoratata dai-dai lokacin an turo kofar da karfi, Rahma ne da Biebie, cikin matsifa Biebie tace.
"Kina ji ana kiranki ki kama mutane shuru dan iskanci ubanwa zai gyara mana d'akin."
Tana kare mata kallo, kallon mai cike da wulakanci.
"Ke Sister kalli fa 'kazanta anan."
Fad'in Rahma na nuna leman da yake bin 'kafar Ummu.
"Mtsw 'Kazanta ma d'aya ko biyu, zomu fita kar ta sani amai."
Da sauri suka fita, Ummu ko kuka tasa ganin abin wancan watan ya dawo mata jan jikinta tayi ta shiga band'aki ta gyara jikinta ta wanke kayan da bata ta fito ta sake kwanciya tana kuka.
Jin bud'e kofa yasa ta kalli kofar da sauri tsammaninta duk sune suka dawo, tsaye yake yana kallonta, kanta ta d'auke ya 'karaso 'dakin ya zauna gefen katifan a hankali yace.
"Meke damunki?"
Bata kallesa ba tace.
"Ciwon baya."
Kallonta yayi da kyau.
"Dama in za kiyi period haka yake miki?"
Shuru tayi dan bata gane me yake nufi ba.
"Sorry ina nufin in za kiyi Al'ada haka yake miki."
Tusa kanta tayi cikin filo cike da tsananin kunya ta kasa magana.
"Tambayarki nake."
"Sau biyu nayi inda wannan."
Ta fad'a cike da kunya, kallonta yayi da kyau cike da mamaki.
"Shekarunki nawa?"
"Sha hudu." Ta bashi amsa takaice.
Shuru yayi can ya tashi ya fita, bai dad'e da fita ba, Iyamee ta shigo da breakfast nata da kaya a leda, sai da tasa taci ta bata magani ta koya mata yanda zata gyara jikinta ta tambayeta ko ta iya wankan tsarki, shuru tayi ta girgiza kanta dan ita batama san me wankan tsarki ba, shuru Iyamee tayi cike da mamaki dan musulmi bai iya wankan tsarki ba.Kwana hudu tayi ta gama, maganin da tasha yasa ciwon bayan ya daina mata, taci gaba ayyukanta cikin kwanakin Iyamee ta koya mata wankan tsarki in ta gama, haka kuwa akayi bayan ta gama tayi kamar yadda ta koya mata.
Tin ranar daya shigo ya mata ya jiki bai k'ara shigowa ba basu k'ara haduwa ba.Wata ranar Asabar yan matan suna gida Biebie da Rahma Hauwaty sunyi tafiya da Mami, kasancewar suna hutun karshen zango (Second Semester).
Da yamma tana kitchen tana wanke kwanukan da Biebie ta b'ata ita da kawayenta taga an shigo kitchen din Biebie ce ta shigo ta d'auki cup zata had'a cornflask, kamar tsautsayi taji abu ya fad'o saman kafarta, Ummu ce ta d'auko food flask zata ajiye tsantsin omon hannunta yasa ya sabule, kafin ta d'ago daga sunkuyen da tayi ta d'auki flask din daga saman kafar Biebie, taji an kwasheta da mari dafe kuncinta tayi dan marin ya shigeta.
Cikin kuka tace.
"Kiyi hakuri ban sani ba wallahi."
"Rufemin baki wawiya kawai."
Shuru tayi taja gefe ta tsaya tana share hawayenta.
"Fitarmin a kitchen k'azama kawai."
Fad'in Biebie tana nuna mata hanyar kofa.
Cikin sauri tana shirin fita gib tayi karo da Rahma, wani marin ta saukar mata a fuska itama wanda yafi na Biebie zafi.
"Baki da hankaline ko tsabar raini ke damunki zaki bigeni bakya kallo.."
Bata k'arasa taji sukar marin daya gigitata, d'ago kai tayi yana tsaye yana kallonta ransa a mutukar 'bace.
Fizgota yayi ya tura kitchen ya shiga ya kulle, belt na jikinsa ya cire ya had'ata ita da Biebie ya zane ciki da waje dan duk abinda sukewa Ummu gidan yana kula kawai yana kawar da kaine dan kar a fahimci wani abu.
Tsaf ya zanesu dama Mami bata nan duk bugun duniyarnan da Ummu take yi ya bud'e kofar yaki sai da ya gama ya fita tana durkushe tana kuka hannunta yaja ya nufi d'akinsa da ita tana turjewa.PhartyBb.wordpress.com
أنت تقرأ
SANADIN HA'DUWARMU
عاطفيةLabarin matashiyar budurwa Ummu A'isha, labari mai cike da tsantsar tausayi da rashin gata, soyayya da rashin taimako.... Abubakar Sadeeq wanda ya taimaki rayuwar Ummu bayan wahalhalu da tasha, ya ba ta dukkan taimako kafin ya watsar da lamuranta. ...