NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION
SANADIN HADUWAR MU!!!
©Pharty BB(4)
Ummu ko sai daf da magriba ta farfad'o, ganinta sabon d'aki dakyar ta iya tuna mai ya kawota, kuka tasa musu nan matar mai gari tayi ta bata hakuri har ta samu tayi shuru sai ajiyar zuciya take, ita kam tasan gatanta ya 'kare.
Kwanan Baffah biyu da rasuwa har lokacin Ummu na gidan mai gari, da yamman ranar Abulle ta turo Laure ta k'irata, badan ta so ba ta musu sallama suka tafi gida, gidan ba mutane sosai sai 'kalilan y'an unguwa da k'anwar Abulle da abokiyar Abulle mai suna Lami.
Da sallama suka shiga gidan har 'kasa ta durkusa ta gaishesu ta wuce d'akinsu, bayan tafiyarta Lami ta kalli Abulle tace.
"Ke aminiyar ya za kiyi da wannan yarinyar wai?"
"Yako zan yi da ita banda muci gaba da zama da ita ko ba komai tana min tallah da ayyukan gida."
"Cabdi kina nufin ki zauna kici gaba da ciyar da katuwa, ita ba zata tashi ta tayaki nema ba."
"Lami kenan duka duka sha hudu take kuma wannan kauyen me zata taimakin dashi."
Shuru lami tayi can tace.
"Ta fara al'ada?"
"Ah a bata fara ba, lafiya kike min wannan danyar tambayan?"
Cewar Abulle tana ma Lami wani kallo.
"Ina da babban shawara gareki duk lokacin data fara ki sanar dani, insha Allah da wannan yarinyar har Makkah za kije Abu, kai nima sai kin kaini."
"Allah aminiyar."
"Dagaske ke kam Allah kaimu lokacin."
Babin hira suka bude a gidan makokin dako sadakar uku ba'ayi ba.Bayan kwana hudu da rasuwan Baffa aka had' akayi sadakan bakwai, washe gari Abulle ta fara sana'arta na kosai da rana tasa Ummu ta dafa shinkafa da wake ta fita dashi talla, haka da yamma ta kulla gyada ta bata ta fita dashi, da dare ma ta k'ara d'aura mata ta kai dandali.
Haka rayuwar ya kasancewa Ummu banda bautawa Abulle da yaranta bata da aikin yi, Saurayin Dije ko ya sata gaba bata isa ta fita ba yana gadinta sai ya bita ko ina, ita ko da zaran ta gansa take sauri kuma bata bin gun daba mutane, dan taji labarinsa gurin Laure ba imani ba tsoron Allah yake danne yaran kauyen k'anana yake musu fyade, bata tab'a barinsa su hadu ba, ko a dandali in ya zauna kusa da ita tashi take ko taki basa fuska haka zai zo ya zauna, tana taka tsantsan da rayuwarta, dan rashin gata da maraicinta, tasan komai ya mata ba mai tsaya mata.
Bayan Shekara d'aya, abubuwa da dama sun faru, lokacin Ummu alamun budurci ya zauna mata sosai duk da wahala da talaucin da bautan da take ciki bai hana dirinta fitowa ba, Dije ko lokacin sau biyu itada Abulle suke zubar da ciki in Dije tayosa a waje, ta zama tantiriyar y'ar iska mazan kauyen har tsakar gida wani lokacin har d'akin da suke zasu shigo suyi abinda suke so da ita su fita, Abulle sai dai ta shige d'aki in sun tafi ta fito.
Ummu ko abinda yafi mata dadi bata wuni gidan in ta fita tin karfe sha d'aya tallar Shinkafarta sai karfe biyu ta dawo tayi sallah ta 'dauki gyadarta in ta dawo da yamma ta musu ayyukan gidan da dare ta 'dau sauran gyadarta taje dandali.
******
Yau Jumma'a tin dare ciwon mara yasa Ummu a gaba tayi kuka har kanta ya fara ciwo, bata samu bacci ba har asuba wani wahalallen bacci ya d'auketa, cikin bacci taji an kwara mata ruwa mai tsananin sanyi, a firgice ta farka tana ja baya kayan jikinta yayi jakab.
Abulle ce tsaye a kanta.
"Shegiya kin san karfe nawa kika tsaya kina bacci, wazai karb'omin nikan kosan da dibo ruwan."
Cikin muryar kuka ga muryan baya fita dan kukan da tasha da da dare muryan duk ya toshe.
"Dadah kiyi hakuri jiya kwana nayi banyi bacci ba, banda lafiya."
"Asibitine a kanki, zaki tashi ko saina jibgeki."
Cikin sauri ta fara ko'karin tashi bashiri ta sake k'ara ta koma.
"Dadah na kasa tashi."
"Mike in ganki."
Da kyar ta iya tashi dan kafarta kasa d'aukarta yayi, ji tayi abi na bin kafarta da sauri takai dubanta ga inda Abulle take gani, jinine ya bata mata kaya, ido ta zaro tana kallo.
"Na shiga uku." shine abinda ta fa'da a ranta.
Abulle kam murmushin mugunta tayi tace.
"Ina zuwa."
Fita tayi ta tafi gidan kawarta Lami nan ta labarta mata abinda suka dade suna jira, gyalenta ta figo a saman igiya suka nufi gidan Abulle har d'akin su, tana durkushe tana kuka.
Dagota Lami tayi tana cewa.
"Ke banza bar kuka ko wace mace haka take yi muje ki gyara miki jikinki."
Da taimakon Lami ta gyara jikinta ta nuna mata yadda za tayi tana canza kunzugunta suka fito, lakacin Abulle ta gyara inda Ummu ta b'ata dan yau ba maganar kosai.
Zaunarta Lami tayi ta jika mata kanwa tasha dan samun sau'kin ciwon ciki ta kwanta suka fito suka nufi d'akin Abulle.
"Ke Lami yau Allah ya kawomu Badd'o ta fara Al'ada sai ki fad'amin abin kike shirin aikatawa."
"Aminyata kenan kin cika sauri."
"To ba dole ba ina nan ina zaman jiran shekara 'daya."
"To bud'e kunnenki kiji da kyau, birni zamu turata karuwanci kinsan kawata wacce muka taso tare Magajiya, dalilin yin kudinta kenan daga nan kauyen aka 'dauketa aka kaita birni karuwanci tayi kudi iyayenta sunyi kudi, yanzu ita take d'aukan yara daga kauye ta kaisu gidanta dan haka kema zan mata magana mu tura mata Badd'o."
Tin da ta fara magana ta sake baki take kallonta har ta dasa aya.
"Ke Abu magana fa nake miki kar dai duk bayaninnan dana miki baki jiba."
"Naji mana, amma Lami yarinyarnan zata iya mana abinda muke so."
"Zata iya mana waye zai kalleta yace shekaranta goma sha biyar."
"To Lami ku had'a da Dije mana kinga nan ma sana'arta kenan kuma a banza suke kwasarta amma in birninne ai za'a biyata."
"To shikenan ki lura da ita nan da ta gama sai su shirya kayansu, zan ma Magajiya magana dama wancan watan tazo tace zata dawo nan da sati 'daya."
"To to shikenan, wai ni Abu zanyi kudi."
"Har Makkah za kije."
Bayan sun gama kulle kullensu Lami ta fito ta nufi gidanta tana ma Abulle dariya, dan itama tasha alwashin saita samu kudi fiye dana Abu ta hanyar Ummu, da haka ta shige gidanta.Kwana uku tayi ta gama, cikin kwanakin a takure tayi sa gani take duk kauyen ansan abinda take yi, ta k'ara zama shuru shuru, kuma tana ko'karin ta saftace jikinta.
Yau tin safe bayan ta gama tallarta tayi na gyand'a ta da yamma tana zaune a 'dakinsu ta kula abin tin daren jiya ya d'auke tana son ta fad'awa Abulle tana kunya da tsoron me zata 'dauketa, sallaman Abullen ne ya sata tashi.
Tana daga tsaye tana kallonta sai yanzu ta hango abinda Lami take hange daga Ummu duk 'yan matan kauyensu dakyar asamu me kyan dirinta gata da karacin shekaru amma sai uban diri kamar 'yar sha takwas.
"Ke tambayarki zanyi, Al'adar takin bata dauke bane har yau."
Kanta k'asa cikin kunya tace.
"Tin daren jiya ya d'auke."
"Shegiya shine baki fad'amin ba, to tashi had'a kayanki kaf birni zan turaki ke da Dije muma mu samu muyi arzikin kanmu."
"Birni kuma Dadah."
"Eh ko ban isa ba."
"Dadah ni banason zuwa y'/an iska sunyi yawa ki barni na zauna nan abina."
"Kinci gidanku sai kinje in yaso su cinyeki tashi maza karna bubbugeki."
Tashi tayi tana kuka ta had'a kayanta Abulle ta bata daya cikin na Laure mai d'an kyau wanda za tasa gobe.
Daren ranar kasa bacci Ummu tayi tana ta tunanin kome za suje yi birni? Aikatau, shine amsar data tsayar a ranta, ta tsani aikatau dan tana jin labarin gurin y'an matan kauyensu duk yarinyar da aka kai aikatau ko yaron mai gidan ya lalatasu ko maigidan da kansa, ko wasu daban, addu'a tayi tasa a ranta duk inda take Allah zai kareta dan shi kad'aine gatanta.Washe gari....
Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummi Safwaan)
PhartyBB.WordPress.com
أنت تقرأ
SANADIN HA'DUWARMU
عاطفيةLabarin matashiyar budurwa Ummu A'isha, labari mai cike da tsantsar tausayi da rashin gata, soyayya da rashin taimako.... Abubakar Sadeeq wanda ya taimaki rayuwar Ummu bayan wahalhalu da tasha, ya ba ta dukkan taimako kafin ya watsar da lamuranta. ...