Chapter 01-02

719 24 3
                                    


*_PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S (P.M.L)_*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of the readers.

01 - 02

_KADUNA INTERNATIONAL AIRPORT._

     Saukansu daga jirgin sama kenan, wasu matasa biyu ne ke tafe d'ayan yayi sallama da abokin nasa yayi hanyar wata motar da driver ke jiran sa.

     Shi kuma d'ayan yana cikin shigarsa na bakin wando da farin long sleeved shirt da bakin tie a wuyan sa, yana rike da bakin suit din rigar a hannun sa d'ayan hannun kuma na d'auke da brief case dinsa sai faman smiling yake.    
       
      Wasu 'yammata biyu da na miji daya ne suka yi ta kansa, matan suka ce "Oyoyo Ya Mahmud" suka rungume sa, shi na mijin kuma yace "Welcome Bro" yayi hugging d'insa shima.

      Sai yanzu ya bud'e bakin sa da cewa "ya banga da wanda kuka zo tare ba, wa ya kawo ku?" Dariya suka yi, k'aramar tasu Airah tace "laaa  yaya ba kasan ya Musty ya fara driving bane", zaro idonsa yayi waje yace "Wow! Don't tell me, ashe lil Bro angirma".

      Da annashuwa suka iso wajen motar duk suka shige suka nufi gida suna ta yiwa yayan nasu tambayoyi akan kasar US da ya kammala karatun sa ya dawo.

      Suna shiga Mummy ce tayi saurin fito wa ta same su tana " Welcome my son" Mahmud yayi saurin shige mata jiki tayi hugging d'an ta tace "I really miss you dear", shima yace " miss you too Mum, but am finally back home now".

      Muryan Dad suka ji yayi gyaran murya ya iso su yana murmishi yace kai kullum Mum d'inka kasani ko? Kuma ita kad'ai kake missing".

       Jannat ko kamar jira take Daddy yayi magana tayi saurin cewa "Daddy kaman kasani, har Mummy manta damu take idan yaya ya dawo", "k'yale sa... ai ni ina nan kar ku damu".

     Shikam Mahmud kasa cewa komai ma yayi sai smiling da yake yace "am sorry Dad I also miss you", duk dariya suka fashe dashi Mum tace "ok yanzu je kayi wanka ka dawo ga lunch d'inka kan dinning table".

  
      Can da daddare bayan Mahmud ya huta da gajiyan sa yana kwance kan gadon sa wayan sa yayi ringing ya d'aga.

" Hello, Sweety kinji ni shiru ko ban kira ki ba am sorry", "No Mahmud, you don't have to apologize nasan kana sauke gajiya ne banyi fushi ba". Tayi maganar ne cikin fara'ar ta suka ci gaba da soyayyar su.

       Bayan ya gama wayar da budurwar sa Siyamah sai yayi dailing number abokin sa da suka zo tare daga kasar US. " Maza yane, bacci nake fa ka ta dani", "toh ai gara kai ka samu baccin ma ni gashi na kasa saboda da rashin shan beer na kwana daya", dariya Nasir ya masa yace "gaskiya gobe ya kamata mu nema kar tamaka illa, kadai daure kayi baccin", " hakan zanyi kawai sai da safe". Ya katse wayar.

      Washe gari da safe bayan ya kintsa ya fito yin breakfast nashi.

  Mummy ya tarar wajen dinning d'in tana zaune ya kara so wajen da smile d'insa yayi pecking goshin ta, Mum tace "a'a Son sai yanzu ka fito?" "Eh Mummy kinsan a kwai gajiya ne bai jima ba na tashi daga baccin", murmishi tayi tace "nima nasani ai shi yasa ban shiga tada kai ba".

   Kujera ya ja ya zauna Mum tayi serving d'insa yace "Mum ina Dad da kuma sauran yaran?" Mum tace "duk sun fita, Dad naku nada meeting a office sai kuma Jannah da Musty suna da lecture'n safe Airah kuma taje School".

  "Ok, ke kad'ai suka bari a gidan", " toh ai nasaba dan ma yau kana nan", "tab ai nima fitan zanyi, zanje zagaya Friends d'ina", "gaskiya ya kamata kam". Daga nan ya kammala break d'insa yayi sallama da Mum ya fice.

    Da motar Mummy ya fita direct gidan su Nasir ya fara zuwa yayi parking a kofar gidan ya k'ira shi a waya ya fito ya shige motar suka nufi beer house.

     Sunsha giyar sunyi tatul amma banda Nasir dashi bai bugu sosai kaman Mahmud ba dan shi controlling sosai.

  Saida suka zauna a wajen na wasu hours sannan yad'an sauka akan su suka bar wajen. Mahmud yaso tafiya da wasu gida amma yana gudun fad'an Daddy.

     Daga nan kuma yaje yayi dropping Nasir a gida sannan ya wuce gida shima.
     
Ya fito daga motar kenan sai ga Daddy ma ya fito daga nasa motar ashe yariga sa zuwa amma bai sauka ba dan sauraron wani announcement da ake yi a Radio'n cikin motar.

     Mahmud bai kula da Daddy ba zai wuce ya shige cikin gidar Daddy ya tsaya kallon sa up and down da kuma yanayin tafiyar sa. Atake ya gane abunda ya saba yi ne yaje yayi. Tsawa ya daka mar ta hanyar kiran sunan sa ya juya kallon Dad d'in nasa.



Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now