Chapter 09-10

244 13 0
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of reader's._*

*_Follow me on wattpad @ Fkahmad._

In dedication to Maryam Adamu. Happy birthday dear friend wish you Allah's khair and blessing, have fun its your day!😘

09 - 10

      Daddy bai shigo gida ba sai bayan isha'i. Bayan ya ci abincin sa ya huta sannan Mommy ta d'auko zancan Mahmoud.

     Tunda ta fara maganar kasa kunne yayi ya zuba mata ido yana sauraron ta har ta idda maganar.

     Sauke numfashi yayi sannan yace "kin gama?" Kallon sa tayi da mamaki a fuskar ta tace "kaman ya nagama kuma kana sounding like never serious", ya kara ce da ita  "nace kin gama?" Shiru tayi ta rasa ma abun fad'a sai ido da ta zuba masa, shi kuwa crossing na k'afar sa yayi ya jingina a jikin kujera ya yace "idan kin gama da wannan zancan shirme na ke da d'an ki sai ki bani waje na huta".

    Mummy da bata tab'a tsammanin hakan daga garesa ba har yanzu ta kasa daina masa kallon mamaki.

    Baki ta bud'e zata yi magana "amma Alhaji..", cikin zafin rai ya d'aga mata hannu tare da fad'in " dakata Asma'u, idan wannan maganar ce nagama ta, wani uba ne zai d'auki innocent 'yar sa ya danka wa irresponsible person like Mahmoud, for God's sake ke kanki kin sani d'anki ba mijin aure bane, je ki gaya masa randa yayi hankali ya daina shaye shayen banza da yake sannan yazo mun da maganar aure in ba haka ba kuma kuje can ku k'ara ta", ya mike ya nufi d'akin sa.

   Baki ta sake wangalan tana kallon sa da mamaki har ya gama ya tashi.

    "Turkashi! Lallai ko da sake Alhaji, ya zanyi na tun kari Mahmoud da wannan bayanin?" Ji tayi anyi shot da stool d'in dake bayan ta cup na glass dake kai ya fad'i ya tarwatse, a tsorace ta juya Mahmoud ne da ya d'aga kujerar dinning d'aya zai kwad'a akan center table d'in parlour'n Mummy ta saki k'ara tare da dakatar dashi amma ina har ya saukar da shi kan glass table d'in tas tatatas sai k'arar fashe war sa da ake ji.

     Mummy tace "wai me kake yi haka ne? Ka bari ya isa haka", da zafin rai yake maganar " ki k'yale ni Mum naji duk abunda Daddy ya fad'a, me yasa zai mun haka bayan ina son Siyamah, d'azun nan najeni gai da Abban ta ya jaddada mun idan am not ready akwai wanda zai had'a ta da, I can't bear losing Siyamah", ya fad'a yana goge guntun kwalla da ta fito mar ya shige d'akin sa.

    Zama yayi kan gado ya d'auki wayar sa ya shiga kallon hotunan Siyamah a wani folder da ya ware mata na musamman. Wani hotan ta da tayi da hijabi tana smiling ga dimples d'inta sun fito, shafa kan hoton yayi muryan sa na rawa yace "Why? Why? Daddy inason Siyamah" sai kuma ya fashe da kuka.

     Jannat da Salma ne suka fito a lectures zasu library dan yin wani research Salma tace "Friend naga tun ranar da naje gidan ku nace miki ina son yayan ki kiyi hooking d'ina dashi baki ce komai ba", Jannat tayi murmishi sannan tace " Salma toh ai ke d'inne baki da dama, gobe in kinga wanda ya fisa kyau sai ki juya mar baya, ni kuma ina gudun abunda zai min ne ranar da zaki rabu dashi", "kar ki damu bazan rabu dashi ba wannan karan dashi zan zauna babu ruwa na da kowa", " hmm ni dai gaskiya ban yarda da ke ba".

  "Toh shikenan ko number'r sa ce ki bani bazan nuna ke kika ban ba", " ke anya kuwa? Bari zan baki ba yanzu ba tukunna dan yanzu hankalin sa na kan wata", "shikenan dai ni idan zan samu no problem".

    Mummy da Daddy na zaune a parlour tana lallab'a shi da ya amince da maganar auren Mahmoud amma ina Daddy ya kafa ya tsare.

     Sallama suka ji daga bakin kofar ansa wa sukayi Daddy ya taso da murmishi ya mika wa mutumin hannu tare da cewa " Engr. Ahmad Kayi wuyan gani fa", shima mutumin da murmishi ya tunkaro sa sukayi musabaha yace "wallahi ayyuka ne suka mun yawa a office". Mummy da ita ma murmishin take suka gaisa da Engr. sannan tace " gaskiya rabon ka da gidan nan zai wuci kwana goma", "amin afuwa Hajiya aiki ne suka mun yawa sai yau na samu daman kawo muku ziyarar", " yayi kyau toh bari na kawo ma ruwa", Mummy ta tashi. Call ne ya shiga wayar Daddy shima yayi excusing kansa ya tashi.

    Mummy ta ajiye mar ruwan sannan ta zauna tare da cewa "ya su Hajiya Kaltum da Mufeedah a Maiduguri dan ya kwan biyu bamu gaisa ba", "suna nan kalau ita Mufeedah ma tagama SSCE'n ta last week tace zata zo hutu nan ta muku har wata", "haba kace y'ar tamu angirma masha Allah, za tayi kaman shekara nawa yanzu?" "Eh shekaran ta 18 yanzu dan dai Mamar ta bata bari ansa ta makarantar da wuri bane da tuntuni taga ma ai",  " yanzu dai ka kyau ta da zata zo mana dan rabon ta da zuwa hutu nan ai ta jima tun tana y'ar k'arama".

   Daddy ne ya shigo ya katse su "kamar naji kunce y'ar tawa zata zo hutu nan koh", " eh wallahi ta dame ni sai tazo", "ai ya fi kam dan ko shekara biyu da suka wuce da naje ni Maiduguri sai da tace zata bini ka hana ta", dariya sukayi Mummy tace " toh bari na shiga ciki" ta basu waje.


Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now