Chapter 07-08

236 16 2
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
💝

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate, we touch the hearts of reader's.

07 - 08

Nan ya tarar da Mummy ma na kokarin fita ita ma, jin muryar sa da tayi ya kira sunan ta ne yasa ta tsora ta dan ita a tunanin ta ya jima da bacci shine tafito da saurin ta ta bud'e mar kar asirin ta ya tonu dan abun da take gudu kenan.

Ce mata yayi ki tsaya anan bari na karasa, haka ta tsaya dan ba yadda ta iya.

Jin wani wawan bugu da ya kaima gate d'in ne ko da me ya buga oho yasa Airah ta fito da gudu ta fad'a kan Mummy, Jannat ma tana biye da ita ta labe a jikin bango dan tsoro duk basu san meke faruwa ba.

Musty kuwa tun bugun farko shima ya farka dan baiyi nisa a bacci ba ya tashi yana lekar kofar ta window sai addu'a yake shararawa dan banda Mummy babu wanda yasan Mahmoud ne.

Daddy ya k'arasa ya leka wajen ta wani hole dake jikin gate d'in sai fuskar Mahmoud yayi arba da dan saboda full light na motar a kunne take shi yasa har ya gane shi ne.

Wani bakin ciki ne ya lullub'e Daddy sai ya ji tsanar d'an nasa a ransa, a fusace ya kai hannun sa ya bud'e sakatar ya juya kawai ya nufi cikin gida dan ko maganar ma ya kasa ya mar.

Mummy da ta gansa a hargitse ya bi ta gefen ta ya wuce jikin ta yayi sanyi itama ta kama hannun Airah suka je d'aki Jannat ma ta bisu.

Shiko Mahmoud ana bud'e wa ya samu ya lallab'a ya shigar da motar da k'yar dan har yanzu a mayen sa yake. D'akin sa ya wuce direct ya fad'a kan gado.

Daddy na shiga ya rufe System d'insa ya fad'a toilet wasa ruwa dan wani zafi yake ji.
Mummy ma haka tayi addu'ar ta ta kwanta.

Sai da gari ya waye Mahmoud yaga irin missed calls da Siyamah ta mar dan bayan wancan ma ta k'ara wasu.

Kiran ta yayi ya bata hak'uri akan baisan inda yabar wayar bane sai yanzu ya samu dan yana silent sannan ta basa good news d'in da Abban ta ya mata, shima yayi farin cikin hakan sannan ya ce zai je mata hira anjima kuma zai sanar da iyayen sa.

Jannat na kwance tana chatting a wayar ta kawar ta Salma ta k'ira ta. Da fara'ar ta ta d'aga wayar dan tana son kawarta ta sosai "Hello Friendy ya kike?" "Kalau fa kina gida ne na k'araso miki dan ina anguwan ku". Ihuu Jannat ta sakar na farin cikin zuwan kawar nata dan baswa gajiya da kallon juna, "kai wannan ihun haka ai sai ki fasa mun dodon kunne, kina nan ne ko kuwa?" "Haba kema daga jin murna ta ai kinsan ina nan, ki k'araso da wuri please", ta kashe wayar ding, ta tashi da gudu ta shiga wanka dan tun da safe ba abunda take yi sai chatting.

Bayan kamar 30 minutes ne taji an bud'e kofar gate ta leka ta window ganin Salma da tayi ta ruga aguje za taje ta same ta kenan ta bangaje Mahmoud da shima yana shirin fita suka yi karo a kofar parlour.

Tsawa ya daka mata " are you out of your senses ko bakya gani ne?" Jannat da ta tsora ta tayi fuskar tausayi tace "ayya am sorry ya Mahmoud bangani bane", hannu ya d'aga mata " its ok, ina zaki shiga haka da gudun nan", murmishi tayi sannan tace "kawata zan tare awaje", jin sallamar da tayi ne ya hana sa magana ya juya kallon kofar.

Tsalle ta daka tare da amsa mata da kuma fad'in Oyoyo Salma suka rungumi juna.

Bi yayi ta gefen su zai fita Jannat tace " Yaya ga kawata Salma fa", murmishi yayi creating ya juya kallon ta "gaskiya kam sai yau nagan ta dan sunan ta kam yajima ina ji", gaishe sa tayi da zazzakar muryan ta ya amsa ta ba yabo ba fallasa sannan ya fice.

Binsa Salma tayi da kallo tace " Wow! Jannat your Brother is breathe taking, kardai shine ya Mahmoud", zungure ta Jannat tayi ta had'e rai tare da fad'in "kinji ki ke kuma shine mana me kike nufi?" Fari tayi da ido tace "kin gane me nake nufi mana", " hmm, ke da shegen san kyawawan maza ni dai ki dau'ke idan ki kan yaya na", dariya tayi tace "Allah baki isa ba ni dai sai kinyi fixing d'in mu", " lallai kam, yanzu dai zo muje ku gaisa da Mummy", taja hannun ta suka je d'akin Mummy.

Da yamma Mahmoud ya dawo yau anyi abun arziki dan bai sha komai ba ya samu Mummy a kitchen tana girki.

Shiga kitchen d'in yayi ya tsaya kusa da ita, Mummy da ta d'aga kai ta kalle sa taga kaman da damuwa a ran sa tace "ah'a Mahmoud ka dawo ne?" Jin shiru bai ansa ta yasa ta bar a bunda take yi ta maida hankalin ta kansa "me ke damun ka ne?"

"Erm, erm Mummy dama Siyamah ce", sai kuma yayi shiru tace " meya samu Siyamah'r?" "A'a ba komai bane Abban ta ne ya ce ta fidda miji kuma yana bukatar ganin iyaye na shine na ke so ki taya ni fada wa Daddy". Murmishi tayi ta dafa kafad'ar sa tace " shine kake mun wani kame kame kar ka damu bari Daddyn na ku ya dawo zan gayamar".



Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now