Chapter 57-58

140 8 1
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.com

57 - 58

      Su Musty na fita daga ward d'in suka ci k'aro da Daddy'n Mufeedah dan tuni Daddy ya sanar dashi, koma wa Musty yayi ya masa jagora zuwa d'akin da aka kwantar da ita.

      Suna shiga cikin motor kenan wayar Musty yayi ringing, ya d'auka Mahmoud ne saboda duk sun damu susan inda yake ashe Jannat ce ya d'aga "hello Jannat", " ya Musty ina kake? Ka biya gida ka d'auke ni pls yanzu Mummy take fad'a mun abunda ya faru", "OK gani nan zuwa sai kiyi sauri ki fito".

       Gidan su Jannat d'in suka fara zuwa suka d'auke ta sannan suka wuce gidan su duba Mahmoud. Da sauri suka k'arasa ciki saboda wani k'ara da suka ji, k'ofar ma a kulle yake Musty ya bubbuga da k'arfi suka samu shiga. Mahmoud suka gani da kwalbar giya a hannun sa yana kok'arin balla murfin yasha.

      Da gudu Musty yazo ya karb'e kwalban yace " haba ya Mahmoud har yanzu baza kabar wannan halin naka ba kowa ya d'auka ka daina sha", Mahmoud ya d'aga murya yace "ina ruwan ka munafikin banza, ka d'auka bansan abunda kake bako, toh Allah ya bud'e asirin ka na gane ashe son Mufeedah kake kullum kana wani shisshige mata toh baza ka same ta ba dan ta riga da ta zama Mata ta".

     Jannat ta bud'e baki cike da mamaki tace " ya Mahmoud kayi misunderstanding ya Musty ne amma shi babu ruwan sa da Mufeedah tunda aka aura maka ita, da ne dai ya so ta kuma baima sanar da ita ba saboda yasan akwai wanda take so amma sai ta kasance matar ka".

       Musty yace "ya Mahmoud baka san abunda yake tafiya bane saboda wannan lokacin baka ma gari amma ya yarda dani babu wani abu tsakani na da Mufeedah kaman yadda Jannat ta fad'a maka naso ta amma ban sanar da ita ba dan tana da wanda take so yanzu kuma ganin kan wata kuma matar yaya na nake mata".

      Kan sa Mahmoud ya kawar zuwa gefe d'aya, Musty yace " yanzu dai ba wannan ba Mufeedah bata da lafia an kwantar da ita a asibiti fad'uwan da tayi anan jiya yasa ta samu fracture a spinal cord d'inta", a sauri Mahmoud ya juya yana kallon Musty da baki a bud'e, da k'yar ya iya magana muryan sa na rawa yace "Musty are you serious", " ba'a k'arya da ciwon ai ya Mahmoud Mufeedah ta samu matsalar kashin baya bata ma iya mik'e wa ta tsaya".

     Hawaye ne suka fara gangarowa daga idanun sa ya d'aura hannu a hab'arsa ya durkushe k'asa muryan ta yafara ji yana masa yawo a kwakwalwar sa lokacin da tasaki k'ara ta fad'i tana kuka take cewa bazan iya tashi ba ya mahmoud kazo ka taimaka mun yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, I did it its all my fault", sai kuma ya fashe da kuka, Su Musty dai sam basu gane me yake nufi ba shima ya durkusa a gefen sa ya shiga basa hak'uri duk da baisan shine sila ba, Mahsin da Jannat ma duk sun tausaya masa har da hawaye a idanun su.

    Da k'yar suka kwantar masa da hankali sannan suka nufi asibitin. Mummy kad'ai suka tarar dan tuni su Daddy sun bar asibitin saboda suje su fara shirye shiyen tafiyar su. Hawaye cike a idon Mahmoud ya k'arasa ciki ya gaishe da Mummy, mik'e wa tayi tace da su Mahsin mu basu waje ko. Mufeedah na kallon sa ta kau da kanta gefe. Zama yayi a side na gadon ya d'aura hannun sa akan nata, janye hannun ta tayi da sauri, shiru ne ya biyo bayan na wasu mintuna sannan Mahmoud yayi magana da muryan sa kaman mai son yin kuka yace " me yasa baki fad'i gaskiyan ba kika b'oye nasan nayi babban kuskure ga kuma kishinki da nake shine na kasa controlling anger na namiki aika aikan nan?"

    Juya wa tayi ta kalle sa da d'an hararan ta tace "kar ka d'auka halarci na maka ina sane da abun da nake dan haka ka jira sakamakon ka", ya mai da kallon ta d'ayan gefen. Mahmoud sam baiji dad'in abunda ta fad'a ba amma ya dake yace " please Mufeedah ki sani ina sonki ne bana son yadda kike treating d'ina I can't leave you in this pain na miki alkawarin sama miki lafia very soon Insha Allah, wallahi baki san yadda naji ba sanda Musty yake gaya mun abunda ya same ki", doguwar tsaki Mufeedah taja masa sannan tace "da Allah Malan ka bani waje ina bukatar hutu", hawayen da ke mak'ale a idanun sa ne suka sauk'o daidai hannun ta taji hawayen ya fad'o, mik'e wa yayi ya nufi hanyar fita sai da yazo bakin k'ofar ya waiwaye ta amma kanta na gefe ko kallon sa ba tayi sai ya juya ya fita.

     Tana jin rufo war k'ofar ta d'ago hannun ta tana ganin inda hawayen nasa suka sauk'o akai tab'e baki tayi tace " kad'an ka gani sai nasaka zubar da hawaye sosai, ba kai d'an giya ba", tayi murmushin yak'e.



_kuyi hakuri da wannan wallahi duk agajiye nake muna biki ne_

Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now