Chapter 37-38

186 11 1
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

37 - 38

Bayan kwana biyu Daddy yabawa Mummy makudan kud'i dan suyi siyayyan kayan da za su bukata wajen amfani dashi a bikin Mahmoud da kuma kayan lefe dazasu had'a wa Mahsin dana aure dukka.

A kwana a tashi yau saura kwana biyu bikin nasu. Cikin kwanakin nan Mahmoud da Mahsin sun shak'u sosai dan ko da yaushe suna tare a gida ko kuma Abban ta yasa driver ya fita da su outing.

Da daddare Mahsin na zaune da wata friend d'inta Hafsah kuma cousin ce a gare ta suna hiran ya za su gudanar da kamu da za suyi gobe Amina ta shigo d'akin.

Zama tayi a tsakanin su ta kalli Hafsah tace da ita "Hafsat dama jira nake sai ranar da kika zo kwana na gaya miki dan Allah kiyi wa wannan k'awar taki magana da ta chanza wannan shawaran da ta yanke na auran Mahmoud, he is not deserved to get married to any of us saboda kinsan d'abi'un da yayi a baya sannan kuma ace mace zatayi curing d'insa yanzu? Ai wannan wahala ne wa y'ar mutane".

Maganganun Amina suka b'ata wa Mahsin rai ta mik'e tsaye immediately tace " haba ya Meena, abunda kike fad'a akan ya Mahmoud sam baiyi ba na gaji da jin k'ora fi da kike akai na, tun ranar da akace an basa ni kike bakin ciki, ke kince bakya so to ni ina sonsa, ina son abuna kuma na yadda zan warkar dashi daga matsalan da yake ciki dan haka pls ki rabu dani".

Ganin Amina bata ji dad'in yadda tayi acting ba yasa kuma ta durkusa a gaban ta ta riko hannun ta tace "kiyi hak'uri ya Meena nasan kina gudun mun kar na shiga cikin wahala akan ya Mahmoud amma karki damu tunda inason sa shima yana sona zamu zauna lafia insha Allah baza kuji kanmu ba kuma na miki alkawari duk abunda banji dad'in sa ba a gidan sa ai bani da wacce ta fiki zan zo nasanar dake and zaki ban shawara mai kyau akai isn't it my sister?" Ta marairaice kai tana kallon cikin idonta.

Murmushi Amina ta kirkiro ta gyad'a mata kai ahankali tace "yes dear", shafa mata kai tayi da hannun ta na dama ta sake ce "shikenan sister Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agare mu gaba d'aya". Mahsin ta mik'ar da hannun ta ta goge wa Amina d'an guntun kwalla da ta sauko daga idanun ta".

Hafsah ta lek'o tana dariya tace "how cute sisters you are, kuna burge ni Allah amma Mahsin kece mara sa jin magana all the time sai kin b'ata wa ya Meena rai". Suka saka dariya dukan su.

Family'n Barr. Abdallah jiya suka zo su Maiduguri saboda bikin Mahmoud da ya gabato. A family house na su suka sauka banda Jannat da ta sauka a gidan su Mufeedah.

Mufeedah da Jannat sunci kwaras sun sha kwalliyar zuwa wajen kamu gidan su Amarya Mahsin, Jannat tace " ai na manta mutuniyar ban nuna miki pre wedding pics na ya Mahmoud da matar sa ba, sai kinga yarinyar y'ar k'arama sai pallin bala'i fa hmm".

Karb'ar wayar Jannat Mufeedah tayi tana viewing pictures d'in tace "kai kai gaskiya k'arama ce in ba ya Mahmoud ba ya wannan zata iya fama da d'awainiyar sa?"

Jannat tace hmm "ni ba wannan bama kinsan kowa sai zancen sa yake duk dangi kowa yasan abun kunya dashi da matar sa sukayi. Wacce uban y'anmatan ya basa daban shi yace kanwar ta yake so ita da tafisa rashin kunya kuwa wai tana son abunta zata raine shi ya warke gata ko secondary bata gama ba mtsw".

Dariya Mufeedah tayi tace "ke mu tafi kar afara babu mu". Fito wa sukayi parlour suka tari Mamar Mufeedah (Hajiya Kaltum) ita ma ta gama shirin ta tace dasu " Jannat Mummy'n ki tace na biya musu za mu tafi da kayan lefen dan sai yau za'a kai ko za kubini ne?"

Atare suka ce eh Mama mutafi, nan suka yo family house nasu Jannat. Jama'a tun ayau sun fara taruwa da yake gobe ne auren. Mummy tace suyi sauri su tafi kafin a fara kamun, nan sauran Anty's d'in dasu Jannat suka kwashi akwatuna da sauran jakakkunan kayayyaki suka je gidan su Mahsin.

Dangin su Mahsin da Mamar su sun karb'e su hannu biyu da fara'ar su, su kuma sunji dad'in hakan. Bud'e kowani akwati aka shiga yi a d'akin ana duba irin dumbun kayan da Mahsin tayi arzikin su. Bayan an gama duba wa kowa na tofa albarkan bakin sa wata kanwar baban su Mahsin tayi magana tace "a gaskiya kayakin nan duk sunyi daidai amma saide bamu ga zanin kaka ba da kuma darduman uban ta dan haka muna bukatar su".

Anty'n su Jannat ma ta lura babu aciki ko manta wa sukayi shine tace " ayi hak'uri dan Allah inaga manta su mukayi agida". Matar nan wato Antyn su Mahsin ta mik'e tsaye tace "aiko wallahi bazaiyu ba sai an kawo mana".

Kowa sai da yayi mamakin rashin hak'urin ta awajen masifa tayi sosai da kyar aka bata hak'uri akan za aje a d'auko a gida nan abun ya lafa.

Wajen kamu, an fitar da Amarya da tasha ado sosai kowa na rurutawa akanta, kawayen ta ne suka mata rakiya wajen Royal chair da aka musu ado saboda couples d'in. Mahmoud na zaune a wajen sai wasu abokan sa da suke gefen sa. Haka ma Mahsin itama kawayenta na gefen ta.

Wajen yayi kyau sai celebration ake ana kid'e kid'en gargajiya. Jannat da Mufeedah na zaune can baya suna kallo suna shewa. Kowa fito wa yake yayi liki ya koma. Amarya da Ango aka bukaci su fito su taka rawa nan Jannat ta ishi Mufeedah da suje su musu liki.

Sabbin kud'i suka fitar cikin jakar su suka tako zuwa gaban Amarya da Ango a filin rawar. Jannat ce agaba Mufeedah na biye da ita tana d'auke da killer smile a fuskar ta hannu takai tayiwa Mahmoud liki akan goshin sa ya d'ago kai dan ganin ko wacece. Sauke idanun sa yayi cikin nata ras suka had'a ido murmushi tayi masa, gaban sa ne ya fad'i ganin irin kyakkyawar mace irin Mufeedah agaban sa sai yaji ta masa kwar jini kuma.

Takawa tayi taje tayi wa Mahsin ma liki, suka d'an taka rawa da Jannat suka je suka zauna.

Tun daga wannan lokacin Mahmoud kejin wani kasala a tattare dashi ji yake kamar wani abunne zai same sa wannan yarinyar da yagani duk ita ce sila to wacce wannan? He kept wondering kuma yana son sake kallon wannan fuskar but inda yake ya masa nisa da inda Mufeedah ke zaune ga kuma mutane suna tare shi ganin ta.

Haka aka gama wannan kamun aka watse lafia kalau sai hamdala Anty's na Mahmoud suke da bai musu abun kunya ba awajen dan sun san he is not used to irin wannan abun gargajiyan nasu.

_Toh reader's me kuka ce gamida Mahmoud?_

_Team Mahsin_
_Team Mufeedah_

Nidai nace Mahsin nake so.

Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now