Chapter 47-48

149 12 0
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

47 - 48

      Bayan sun kammala cin abincin su Mahsin ta tattare wajen da ta komo Musty baya nan ya tafi d'akin sa. Itama d'akin ta ta wuce tayi wanka ta kwanta kan gado tana chatting har barci ya d'au ke ta.

      Musty kuwa bayan ya shige d'akin sa Laptop ya d'auko ya zauna yin wasu danne dannan sa. Sai da ya kai almost half an hour sannan ya mik'e ya shiga toilet yayi wanka ya saka bak'ar jallabiya ya fito zuwa d'akin Mahsin.

      Kwance ya same ta tana barci wayan ta na hannun ta alamar tana wasa dashi baccin ya d'auke ta, murmushi yayi ya cire wayar daga hannun nata ya kashe ta gaba d'aya ya ajiye kan bed side drawer ita kuma ya gyara mata kwanciyar ta ya d'an rufe ta da blanket ya seta A.c'n d'akin daidai yadda bazai dame ta ba sannan ya kashe wutar ya fita zuwa nasa d'akin.

      Mufeedah bata tashi daga barci ba sai kusan 11pm, yunwa take ji sosai dan haka bayi ta shiga ta wanke bakin ta ta fito parlour, Mahmoud tagani kwance kan three seater yana barci ko ta kansa bata biba ta d'auki abincin ta ta wuce kitchen tayi reheating a microwave sannan ta juye a plate ta koma d'aki taci acan.

      Washe gari da safe Musty ya shigo d'akin Mahsin ya yaga bata d'akin, kitchen ya je nan ya tarar da ita, ahankali ya tako zuwa inda take ta bayan ta yadda baza taji ba ya tsaya, tunanin ya rungumeta yake amma sai ya kasa, hannu kawai ya kai kafad'ar ta ya tab'o ta, a firgice ta juyo ganin mutum na tsaye dab da ita nan ma tsora taji ta saki ihu tare da rufe idonta.

      Runguman ta Musty yayi wani shock sukaji gaba d'ayan su Mahsin zata sake rusa wani ihun Musty ya kai bakin sa kan nata ya had'e waje d'aya. Ko shima baiyi zaton zaiyi haka ba balle kuma Mahsin, shiru tayi gami da jin kunyar abunda ya faru, sakinta Musty yayi yace "am sorry banzo na tsorata ki ba kiyi hak'uri", kanta ta sadda k'asa ta kad'a masa kan ta juya taci gaba da abun da take yi.

     Zuwa yayi ta gefen ta yace " breakfast kike mana?" Kai kawai ta iya gyad'a masa dan har yanzu a tsorace take, shiko da ya gane hakan murmushi yayi ya d'aura hannun sa a kafad'ar ta yace "toh menene kuma? Dan na tab'a ki shine kike jin kunya ko kin manta mijin ki ne kar ki damu calm down kin ji", ajiyar zuciya tayi ta k'irk'iri murmushi tace da shi " ina kwana", dad'i yayi ya kad'a mata kai sannan yace mata "kiyi breakfast d'in tare da su ya Mahmoud nan za su zo su karya", dudum taji zuciyar ta ta buga, Musty ya juya yace "bari naje na fad'a musu nan za suzo muci abinci tare".

     Ci gaba da aikin ta Mahsin tayi tana mai jin haushin taraiyar ta da Mahmoud a daa duk da bata san dalilin da Abban ta ya had'a ta da Musty ba amma tayi wa Abba alkawarin zama da mijin ta lafia bayan wasu nasihu da yayi mata.

     Musty na zuwa part na su Mahmoud ya tarar da Mufeedah zauna kan dinning tana shan tea. Sallama yayi ya shigo ta amsa masa cike da jin dad'in ganin sa, ya k'araso zuwa table d'in yaja kujera ya zauna.

  " Besty tea kike sha kardai har kunyi breakfast?" "A'a yunwa naje ji ne shi yasa na had'a tea d'in yanzu zan shiga na girka mana", " yauwa toh tunda baiyi ba Mahsin tama breakfast harda ku sai muje kudi a can ko", murmushi tayi tace "toh shikenan tunda Besty na ne ya gayyace mu, juya wa tayi ta kalli k'ofar d'akin Mahmoud sannan ta juya kan Musty tace " ya Musty please kayi checking ya Mahmoud sai ku tayo tare bari naje na d'an tayi Matar yaya k'arasa aikin ta mik'e tayi hanyar fita shima ya tashi tare da cewa "OK" ya juya sai ganin Mahmoud yayi tsaye bakin k'ofar sa yana kallon su.

      Murmushi Musty ya masa yace "laa yaya ashe ka fito", had'e fuska Mahmoud yayi yace " me ya had'a ka da Mata ta ka zauna hira da ita haka tana washe maka hak'ora?", da mamaki Musty ke kallon sa yace "wani irin magana kake kuma ya Mahmoud Mufeedah ce fa, ko ka d'auka yau na fara ganin ta ne ka manta y'ar Daddy Ahmad ce?" "Nasan da hakan ai, tambayar da na maka shine me ya had'a ka da ita kuke wa juna hira da dariya" "haba ya Mahmoud k'awa ta ce tun a da ma yanzu kuma tana matsayin Matar yaya na", gyad'a kansa Mahmoud yayi yace masa " I don't like such foolishness and this should be the first and last", sanin halin yayan nasa yasa Musty bai damu ba yayi murmushi yace "kai yaya wai kishi, ni ma fa ina da tawa matar yanzu dai muje muci abinci a gida na. Nan suka fito zuwa b'angaran sa.

     Mufeedah na zuwa ta je kitchen ta samu Mahsin suka gaisa ta taya ta kwaso coolers na abincin zuwa dinning dan har taga su. Zama sukayi kan kujera su Musty ma suka iso wajen suka zauna, ko da wasa Mahsin bata d'ago kanta ta kalli Mahmoud ba, Musty ne yace da ita " Mahsin baki ga ya Mahmoud bane banji kun gaisa ba", kanta na kasa tace "ina kwana", Mahmoud ya ansa ta ba yabo ba fallasa.

      Mufeedah ce ta fara serving kanta sai Mahsin tayi serving Musty sannan ta zuba nata, ganin Mufeedah batayi serving Mahmoud ba sai taji kamar ta zuba mar amma sai tayi ignoring wannan thought d'in ta fara cin abincin ta. Ganin wannan matar ta sa bata da Bihar zuba masa yasa ya mik'e ya zuba da kanshi, Musty na son ce da Mufeedah me yasa ba zata zuba wa mijin ta ba sai kuma ya fasa dan gudun maganar yayan nasa.

     Shiru kake jin wajen duk anutse suke cin abincin su, Musty ya d'ebo abinci a spoon nasa ya kai wa bakin Mahsin, kin karb'a tayi ta girgiza masa kai shima gyad'a mata kan yayi tuno nasihar mamarta tayi lokacin da take ce mata ha'a yiwa miji musu koda zaki b'ata wa kanki rai yana da kyau ki fatan ta masa ko ta halin kaka, turo cokalin yayi cikin bakin ta ta amshe sa a kunya ce d'aga ido da zata yi sukayi ido hud'u da Mahmoud da ya kura mata ido, haushi da kunya taji ta tashi ta bar wajen ta nufi d'aki da gudu.

      Musty ya fahimci saboda Mahmoud tayi hakan murmushi yayi ya kalli Mahmoud ya kuma kallon Mufeedah yace "excuse please", ya d'au ki plate nata ya je shi samun ta a d'akin nata dan ya rarrashe ta. Mufeedah ko sai abun ya burge ta gonin ban sha'awa tayi smiling ta fi gaba da cin abincin ta. Mahmoud sai yaji wani ciwo a ransa wanda baisan dalilin hakan ba ya mik'e ya fita bai k'arasa cin abincin ba.




Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now