Chapter 69-70

184 12 2
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.com

*_Happy birthday to the most dearest sweet PML sister Ummahanifa, y'ar gatan Sadnaf or the name which you were known with MISS B~HALL. You are too much you know, all this names oh my god i just like them, May Allah brings success, khair and blessing in your entire life. Fannah LYSVM_*😘

69 - 70

        Suna iso wa gida kowa ya sauka ya shiga cikin gidan babu wanda ya tanka wani cikin su. Gaba da baya suke tafiyar Mufeedah ce a gaba Mahmoud na biye da ita bai gani ba cikin rashin sani ya d'an taka takalmin ta tabaya nan Mufeedah ta kwad'a ihu zata fad'i da sauri Mahmoud ya kai hannu ya taro ta.

     Hamdala ta sakar dan ganin she is saved amma sai taga ashe tana hannun Mahmoud ne daga idanun ta tayi suna kallon cikin idon juna. Sai da suka d'auki kusan mintuna biyu kafin Mufeedah tace "toh kasake ni mana", maganar da tayi ne yakawo dashi daga tunanin da yake yace da ita " dan kinga na kare ki daga fad'uwa ko", bud'an bakin ta arrogantly tace "toh wa ya saka da kasake ni na fad'in ai", dajin hakan immediately yasake ta 'Bam' unexpectedly taji kanta akasa " auch" ta saki k'ara.

    Juya wa yayi yabar wajen bai kula ta ba ya shige ciki amma kuma bai ji dad'in abun da ya aikata ba dan yasan bata da lafia kamata yayi yabi ta ahankali. Tashi tayi ta karkad'e rigar ta tare da cewa "mugu kawai kuma sai ka gani" ta bi bayan sa zuwa ciki.
       D'akin ta tashige shima Mahmoud d'in yana can d'akin sa.

       Washe gari da safe ta tashi ta shiga kitchen ta had'a musu breakfast tayi arranging akan dinning ta zauna ta ci rabonta ta tashi taje d'aki ta koma barci. Around 10:30 ta farka ta fito parlour zuwa tayi dan ta tattara kan dinning d'in ta lura da Mahmoud bai ci ba.

       Zuwa tayi tashiga d'akin sa kai tsaye amma baya nan toilet ta duba nan ma bata gansa ba, zama tayi dirshan a bakin gadon d'akin ta fara tunani, shin meye sa kwana biyun nan Mahmoud baya kula ta gashi ji take tadamu da hakan batasan me yasa ba, jiya baici tuwon dare ba gashi yanzu ma baiyi breakfast ba ya fita.

       Tashi tayi taje side na su Mahsin dan ganin ko yana wajen. Mahsin kad'ai ta samu tace da ita sun fita tare da Musty kuma anan ya karya. Mahsin gani tayi kamar da alamar damuwa atare da ita hakan yasa ta  da ita take tambayar ta ko lafia, nan Mufeedah take gaya mata duk abun da ke faruwa a tsakanin su. Sosai y'ar kanwar tan nan ta bata shawarwari akan zaman da zatayi da mijin ta kamar yadda iyayen ta suka mata nasiha ta d'auka gashi tana jin dad'in zaman ta.

      Godia Mufeedah tamata tare da yin alkawarin gyara rayuwar auren su nan ta tashi taje b'angaren ta dan d'ora tuwon rana.

       Mahmoud bai dawo gida ba sai dare, Mufeedah na sallah a parlour ya shigo, d'akin sa yayi direct. Tana idarwa bayan tayi addu'an ta ta mik'e dan zuwa wajen sa, k'ofar d'akin ta turo ta shiga abunda batayi tsammanin sa ba a yanzu tagani, kwalbar giya ce a hannun sa yana shirin b'alla murfin yasha, da gudu ta k'araso ta durka sa a gaban sa tare da warce kwalbar tace "ya Mahmoud meke damun kane dan Allah me yasa ka zab'ar wa kanka wannan rayuwar?"

       Hannu ya d'aga mata alamar ta dakata yace "babu ruwan ki dani banga amfanin zaman ki dani ba Mufeedah kinsan abunda ke damuwa kinsan dalilin auren mu amma sam kin kasa bani had'in kai dan haka kyale ni na koma rayuwa ta na da maza miko mun kwalbar", ya kai hannu zai karb'a ta hana sa jani in haka suke da wannan kwalbar kashe dai ta sub'uce ta fadi a k'asa.

     Fashe wa yayi ya tarwatse a wajen Mahmoud ya kalle ta cikin tsananin haushi yace " what the hell have you done now, get out of my room" ya karashe maganar da tsawa ya sunkuya zai kwashe kwalbar, Mufeedah duk da tsoran da ya bata wajen yin tsawar amma ta dake ta sunkuya itama tace "kayi hak'ura dan Allah ba da gangan nayi ba amma an gara da ya fashe" daidai lokacin ya kai hannu zai tsinta wani k'aramin kwalba kuma ya d'ago kai zai kalle ta cikin zafin rai ai kuwa tuni kwalbar ta shige hannun sa "ahh" ya tsaki kara, arikice Mufeedah tace "oh my God ya Mahmoud" takai hannun ta kan nasa dake zubar da jini ta sake cewa "its all my fault am sorry please".

      Hannun nasa ya janye tare da d'aga kai zaiyi magana kawai sai yaga hawaye na bin kuncin ta duk cikin damuwa take, samun kansa yayi cikin kasa yi mata magana ganin yadda tadamu, tashi yayi kawai ya wuce toilet bai mata magana ba ita kuma ta goge hawayen ta ta je ta d'auko parker tayi clearing wajen.

       Abincin sa ta d'auko akan plastic tray taje dashi d'akin sa, bata same shi ba saboda wanka yake nan ta ajiye ta fita zuwa nata d'akin dan yin wankar itama. Bayan ya fito ya shirya yana kwanciya kenan Mufeedah ta shigo ta same sa.

      Bata masa magana ba ta zauna ta zuba abincin ta mik'e ta je kan gadon, ahankali ta k'ira sunan sa tace " ya Mahmoud please ka tashi kaci tuwon nan badan ni ma, am really very sorry upon how i've being to you before amma yanzu insha Allah i'll act as a wife to you".

      Tabbas yaji dad'in maganar da tafad'a amma ya dake ya ki kula ta. Surutai ta d'in ga yi masa na basa hak'uri amma sam yaki kawai dai cewa yayi "naji ajiye abincin ki bar mun d'aki", jin furucin nan nasa itama tayi zuciya ta tashi ta ajiye plate na abincin ta fita a d'akin.

       Washe gari Musty da Mahsin ne suka shigo part nasu Mahmoud, Mufeedah kad'ai suka tarar nan tayi murnan ganin su Musty ya mik'a mata ice cream da ya siyo musu dad'i taji tayi masa godia, Musty ya tambaye ta ina Mahmoud tace yana ciki bari ta masa magana nan ta tashi ta shige d'akin sa.

      Samun sa tayi gaban mirror yana feshe jikin sa da tura re ta k'arasa wajen sa anitse tace " ya Musty da Mahsin ne suka shigo kuma suna neman ka fito muyi hira gaba d'ayan mu", bata jira amsar sa ba ta juya ta fice.

      Mufeedah ta d'auko roban ice cream nata tafara sha ahankali suna hira tare da Mahsin da Musty. Shima Musty nasa ya d'auko ya bud'e murfin yana sha, koma wa kan cushion da Mahsin ke zaune yayi yazo dab da ita ya rad'a mata magana a kunne yana cewa "so nake Ya Mahmoud da Mufeedah su shirya dan haka inaso ki saki jiki muna creating scenes a gaban su hakan zai sasu gyara marital life nasa" murmushi Mahsin tayi tace "OK dear".

      Mufeedah da ta zuba musu ido ta had'a taceb" ni ban yarda ba wani gulmar ka mata akaina ya Musty", Mahsin tayi dariya tace "karki damu sis I'll tell you later dan yanzu ba bari na zaiyi ba", Mufeedah tace " oh hakane ko toh nayi fushi" ta kame waje d'aya daidai lokacin Mahmoud ya fito.

       Mufeedah na ganin sa tace "yauwa ya Mahmoud gara da ka fito kaga duk suna gulmata ko kamun maganin su" kallon da ya juya ya bita dashi kadai ya ishe ta amsa nan ta tuno ashe dai baswa wannar wasan tare, haushin kanta taji sosai.

      Mik'e wa Musty yayi da murmushi d'auke a fuskar sa hakan shima Mahmoud d'in suka yi musabaha ya samu waje ya zauna. Hira suke tab'a wa kad'an kad'an wanda Mahmoud sam he's not comfortable a wajen kawai dai zama yake.

      Musty ne yayi wa Mahsin signal ya lakato ice cream ya kai bakin Mahsin karb'a tayi tare da cewa "yum kasan meye?" Yace "a'a sai kin fad'a" tace "ji nayi wanda ka bani ya fi dad'i sosai fiye da nawa so ka k'ara mun", Musty ya mak'e ka fad'a yace " uhum uhum naki sai ke ma kin bani naki na d'ana" nan Mahsin ta lakato nata ta kai bakin sa yace "wow! Kinsan dad'in sa kuwa?"

     Duk abunda sukeyi akan idon Mahmoud da Mufeedah ne dan suyi drawing attention nasu suma suyi. Musty ne ya d'auko leather'n dake k'asa tare da cewa "sorry ya Mahmoud na manta ban baka naka ba here you go share it with your wife", shi da dama satan kallon su yake tun d'azu yace "no thanks" ya mik'e ya koma ciki.
       Mufeedah da ke zaune jikin ta duk yayi sanyi ganin su Mahsin sai taji dama ace itace da mijin ta.






Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now