Chapter 05-06

292 16 3
                                    

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate, we touch the heart of readers_*

05 - 06

   Mummy da taga fitan su a d'akin Mahmoud kuma taji Daddy na mita yasa take tambayar su "lafia meke faruwa?"
  
    Daddy bai ko kula ta ba ya fice sai Musty da ya juya yace mata "Mummy ya Mahmoud ne ya zo shi a maye kuma sai ya fad'i shine muka shigo dashi", hannu ta d'aura a ka tare da cewa " nashiga uku ni Asma'u d'an nan zai ja min masifa wajen Daddy'n Ku, shikenan tafi Musty".
  
  Nan ya juya ya fice ita kuma ta karasa cikin d'akin Mahmoud.

   Kwance tagan sa akan gadon yayi ruf da ciki, matso wa tayi ta gyara masa kwanciyar nasa sannan ta fita takaici duk yabi ya lullub'e ta.

   Bayan kaman awaya biyu ne Mummy ta had'o tea mai k'auri ta nufi d'akin Mahmoud dashi.

   Daddy na nan zaune a falo yaga wuce war ta, tab'e bakin sa yayi yaci gaba da kallon sa a TV.

   Fitan sa kenan daga bathroom yayi wanka ya d'auro alwala sai Mommy ta shigo, tana ganin sa ta sakar masa murmishi tana cewa "har ka tashi ne son?" Shima murmishin ya maida mata yace " eh mummy".

  Ajiye cup d'in tayi akan drawer tace masa "ga Tea nan kasha kafin kayi sallahn kar yayi sanyi", " toh, thank you" yace mata sannan ta juya ta fice a d'akin.

    Wuce wa tayi d'aki dan ta kwanta ta huta saboda aikin da tasha ita kadai dan Jannat bata wuni agida ba tana School.

   Daddy da yaga wuce war ta d'aki ne shima ya tashi ya bi bayan ta.

    Zama yayi akan gado yana kallon ta za ta shiga toilet ne ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunan ta "Asma'u!" Tsaya wa tayi ta juya ba tare da ta ansa shi ba, yace da ita "zo ki zauna za muyi magana ne".

  Zuwa tayi jikin ta a sanyaye dan tasan maganar me zai mata ta zauna.

   Sai da yayi ajiyan zuciya sannan ya fara maganar "Asma'u kinsan halin d'anki, ya kamata ki ajiye shi ki masa fad'a ko zaiji dan ni idan zan masa, zan masa da zafi ne kuma ba lallai ne ya shige sa ba, ke da kuka fi kusa sai kimar fad'a".

   Ita sai yanzu tayi ajiyan zuciyar dan ta d'au ka masifa zai mata sannan tace "Shikenan Alhaji kar ka damu zan masa magana", "yauwa kuma  batun neman aikin sa na yiwa wani abokina magana ya sama masa a Ministry'n su sai ki fad'a masa". " zan gaya masa in Allah ya yarda". Nan ya mike ya fita.

        Washe gari
    Abban Siyamah da Baffan ta ne a zaune sun gama tattauna wa kuma Baffa yayi convincing Abba da a bar Siyamah ta auri wanda take so dan tun farko kamata yayi a fara tambayar ta tana da wanda take so ne idan babu sanna a mata miji.

   Daga wayar sa yayi ya kira ta akan ta fito ta zo ta same su.
    Sallama tayi ta shigo ta durkusa har kasa ta gaishe su kanta na kasa suka ansa mata.
    
     Abban ta yayi gyaran murya kafin ya fara magana "Siyamah Baffan ki ya gaya mun abunda ke tafe dake, yanzu abun da za ayi ki fada wa yaron ya turo iyayen sa kuma ban son b'ata lokaci dan zan iya sauya ra'ayi na".

   Dad'i taji mara misaltuwa muryan ta na rawa tace " toh Abba nagode".

    D'aki ta shiga dan ta kira Mahmoud ta sanar da shi. Dailing number'n sa tayi taji shiru ba a d'aga ba ta k'ara kira har sai da tayi mar 5 missed call sannan ta kyale wayar da damuwan ina ya shiga yabar wayan nasa baya d'aga wa.

       _NASIR'S APARTMENT_
      Party ne suka had'a na gama karatun su.
    Music ne yake tashi mai karfin gaske, d'akin dim light ne a kunne ba'a gani mai kyau, sai abokan sa da suke ta rawa suna shewa sai shan drinks kala kala ake har da masu shan giya ciki kuwa harda Mahmoud.

   Sai can dare kowa ya watse. Mahmoud bai je gida ba sai kamar 11.

    Mommy da ta lura har 9 yayi bai dawo gida ba yasa ta kira sa a waya amma bai d'aga ba, tayi ta dailling number'r sa amma shiru take ji.

     Hankalin ta sai da yabi ya tashi saboda gudun fad'ar Baban su akan zama dare awaje on the other hand tana tunanin ko ya sake zuwa wajen mayen nasa ne gashi ta manta bata masa maganar da Daddy yace ta masa ba.

   Shiga d'aki tayi ta kwanta amma hankalin ta sam bai kwanta ba dan tasan idan Daddy yayi realizing baya gida toh akwai matsala, tunani take yi har bacci ya d'auke ta.

     Horn ya dinga yi amma ba ajisa ba dan haka ya sauko daga motar ya fara knocking na fitan hankali.

     Daddy da yake zauna gaban Laptop d'insa yana wasu aikin Office yaji wannan knocking d'in, a tsorace ya d'ago kansa yana kallon direction na shigo war d'akin sa yana salati, aran sa kuma yana tunanin wa zai dawo gidan at this time kodai b'arayi ne. Ya tashi dan yaje ya bud'e nan yaga Mommy na kokarin sneaking ta fita itama.

    

Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now