Chapter 13-14

224 12 1
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We dont just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad

Dedicated to MOMMYN SULTAN😜

13 - 14

     "Inna lillahi wa innailaihi raji'un" cewar Alh. Aminu da ya razana da kalaman Daddy "Subhanallahi, Abdallah ka tabbatar da abun da kake fad'i kuwa? Shan giya fa kake nufi", murmishin yak'e Daddy yayi "Yaya ai da girma na kam bazan fad'a maka ba daidai ba".

     Ya Aminu ya girgiza kansa kaman mai kok'arin tuna wani abu sannan yace " amma lallai in hakane Asma'u tayi wauta da ta biya ma wannan yaron suna shirme".

    Daddy yace "you see, dama nasan had'in baki suka mun dan sam ban yarda da ita ba, gashi ka gani dai"

     "Ah lallai basuyi daidai ba Abdallah dan Allah kayi hak'uri ban san haka gaskiyar take ba da ban baka wahalar zuwa ba", inji Alh. Aminu.

       Daddy ya mike yana cewa "Toh kaji dai abun da ke faru wa ni zan koma dan ina kan aiki ka nemeni sai kayi wa d'an naka fad'a ko zai ji naka"

     "A'a da wuri haka ko wuni ma baza kamun bane in baza ka kwana ba", Daddy yace " A'a ba yau ba dai zan zo maka wani lokacin".

   "A'a toh shi Mahmoud d'in fa ba tare za ku koma ba ne?" Daddy da har ya iso bakin kofar yace "a'a ba tare muka zo ba ai dan haka sai ya koma randa yaga dama yauwa kuma kace masa an sama masa aiki a garin Lagos next Month zai resuming aiki a Office dan haka ya shirya", " ah irin labari mai dad'i haka bari ya shigo gidan nasan yadda zanyi dashi ai yau sai na kowa masa hankali".

    Daddy yana dariya yace "a toh ko kaima ka d'ana". Alh. Aminu yayi masa rakiya waje sannan sukayi sallama ya koma ciki yana magana shi kad'ai " lallai kaji ja'irin yaro wato so yake ya had'a ni da uban sa shi da wannan uwar tasa, zai zo ya same ni kuwa".

     Bayan Alhaji Aminu yayi wa Mahmoud nasiha sannan yace dashi yaje ya bawa mahaifin sa hak'uri. Hakan kuwa akayi hak'urin ya ba wa Daddy sannan Daddy ya basa sati biyu akan zai duba idan yaga changes na shiriya a tare dashi sannan yaje nema masa auren.

     "Wai yau Jannat ke kika yarda kika ban number'n yayan ki gaskiya babu wanda ya kaini farin ciki yau", cewar Salma da suke zaune tare da Jannat.

    Tab'e baki Jannat tayi " ki de yi a hankula dan kar ya gane ni na baki dan bana san masifar sa", d'aura hannu Salma tayi a kafad'ar Jannat tare da cewa "kar ki damu k'awa ta kinyi mai wuyar bazan baki kunya ba, Allah nikam son ya Mahmoud nake sosai Allah yasa kar ya dizgani", dariya Jannat ta kyalkyale da tace" da ko nasha dariyan da ban tab'a irin sa ba". Salma ta kai mata duka abaya Jannat ma ta rama.

     Siyamah ce ke kwance kan gado tayi ruf da ciki tana b'arga kuka, Antyn ta da take zaune gefen ta sai faman rarrashin ta take.

     "Siyamah ya isa haka kar ki haddasa wa kanki ciwon kai hak'uri zakiyi", cewar Antyn ta. Cikin muryan kuka tamayar mata " Anty me yasa Abba baya son ganin farin ciki na ne? Me yasa bazai bawa Mahmoud lokaci ba muna son juna zan iya jiran sa har zuwa lokacin da Daddyn sa zai amince da auran mu", ta sake rusa wa da kukan.

     Antyn ta ta shafa bayan ta tace "Siyamah baki san Abban ki gata ya miki bane da zaki fad'i hakan, har zuwa wani lokaci zaki jira Mahmoud bayan kinji abun da Abba yace, shekarun ki fa sai k'aruwa suke yanzu kina da 23 har nawa zaki k'ara kafin kiyi aure, kawai ki kwantar da hankalin ki tunda shi Saleh yana sonki kinga zaki ji dad'i bayan auren".

    "Toh amma ai ni ba sansa nake ke ba Anty", "a hakan zaki koyi sonsa Siyamah ki daure ki ci wannan jarrabawar daga Uban gijin ki", " yanzu shikenan na rabu da Mahmoud kenan?" ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciya.

    Mahmoud da yaji wannan sad news na an saka ranar Siyamah nan da two weeks za ayi bikin ta ya rasa ina zai saka kan shi dan bak'in ciki ranan a Bar(gidan giya) ya kwana.

    Mummy hankalin ta duk ya tashi ganin dare yayi sosai Mahmoud bai dawo ba, Daddy kuwa aransa yake jin nan wani irin b'acin rai da Mahmoud ke sasa sai kace shi kad'ai suka haifa dan haka kuma sai ya saki ransa ya kuma yin addu'an Allah ya tsare mar sauran yaran barin ma Musty dake tasowa yanzu.

    Wuraren asuba Mahmoud na kwance kan wata benchi cikin gidan giyar tasu wani mashayi ne irin masifaffun nan ya haushi da duka haka kawai. Cikin baccin sa ya tashi a razane sai bulo da aka kai mar a hancin sa, tashi yayi ya zage sukayi fad'a sosai da jini kaca kaca a jikin sa da k'yar wasu suka raba su.

   Zuwa yai wajen bottles na bear da aka jera cikin wani glass drawer ya ciro d'aya ya b'alla murfin ya kafa kwalbar a bakin sa sai da ya kwankwa d'e shi tas sannan ya saukar yayi wurgi dashi ya kama hanya ya fita.

     Wani dishi dishi idon sa ke gani ga yadda yake tafiya kana gani kasan mashayi ne karshe ga kuma jini da ya b'ata mar riga. Kamar wani mahaukaci haka ya iso gida da ikon Allah.

      Abud'e ya tarar da kofar dan Daddy da Musty sun fita masallaci. D'akin sa ya wuce direct ya fad'a kan gado.


Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now