END

338 16 2
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
💝

Written by F k Ahmad

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's_*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
IG PML WRITERS
https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
http://maryamsbello.blogspot.com

*My IG Fkahmad*

Dedicated to all fans of this novel MAHMOUD.

Pure Moment Of Life Writers ban manta daku ba a kullum kuna raina, Allah ya barmu tare.😘

*_THE END_*

73 - 74

Washe gari Mahmoud da Mufeedah ne suka je gida ziyara. Shigar su kenan cikin parlour'n suka tarar da Jannat da Salma zaune suna hira nan Jannat ta daka ihun murna da gudu taje ta rungumi Mufeedah tana mata oyoyo ta kama hannun ta suka wuce cikin d'akin, Salma da ke kallon su tsaki ta ja ta kau da kan ta, Mahmoud dake tsaye a gun yace "ke lafia kike wa mutane tsaki?"

Kallon sa ta juya tayi ta fara murmushi tace "babu ya Mahmoud k'araso ka zauna mana", harara ya mata sannan ya k'ara da " ai gidan ubana ne nan dan haka basai kin min tayin zama ba, dallah tashi ki bar mun nan", da sauri ta mik'e tana kumbure kumbure ta shige d'akin ta samu su Jannat, ko kula su batayi ta samu waje ta zauna.

Mummy ce ta shigo d'akin nasu farin ciki ne tattare da ita tana k'wala wa Salma k'ira "Salma, Salma ina kike?", Salma ta d'aga murya tace " na'am Mummy gani" tare da tashi, turus Mummy ta tsaya sakamakon kallon Mufeedah da tayi, washe hak'ora tayi tace "la Mufee 'yata yaushe kika zo?" Har k'asa Mufeedah ta sauka ta gaishe ta tare da murmushi d'auke a fuskar ta.

Mummy tace "a haba taso mana yaushe zaki daina wannan kunyar taki ne? Ina kika bar Mahmoud din?" "Yana can parlour a zaune" cewar Mufeedah. Mummy ta juya kan Salma tana dariya takamo hannun ta tace " Salma 'yata yanzu muka gama waya da Ummar ki take sanar dani anjima za azo saka ranar ki da wani dan uwan ki, ina taya ki murna sosai Allah ya sanya alkhairi".

Jannat dake kan gado ta saki ihu ta sauko da gudu ta fad'a kan Salma tace "oh besty shine baki fad'a mun na taya ki murna ba", Salma dai kanta na sunkuye a k'asa bata d'ago ba hasali ma fuskar ta adamk'e take, Mummy tace "ke dai Jannat baza ki bar haukan ki na tsula ihu wa mutane ba" Jannat tace "o'o Mummy irin albishir haka ba dole nayi ba", Mummy tace " toh ke ma ki fitar da mijin auren mana", Jannat ta d'aure fuska tace "Mummy Allah ya kawo mana", "oh bari na bar muku d'akin naje na sami baban nawa a parlour", nan Mummy ta juya ta fita.

Mufeedah ta matso kusa dasu murmushi d'auke a fuskar ta tace da Salma "ina taya ki murna besty'n Jannat", kallon banza Salma ta mata Allah yaso Mufeedah bata gani ba dan tuni ta kau da kai. Jannat ta zungure tace " ni meye abun had'a rai toh mai makon kiyi farin ciki", Salma tace "kinsan dai ba wanda nake so bane so banga abun farin ciki wajen nan ba".

Jannat ta sauke ajiyar zuciya dan tasan lallai Mahmoud ne aranta, ga kuma Mufeedah zaune ita bata san dabar garin ba, nan tace mata "Salma kar ki tada hankalin ki da yardan Allah wanda iyayen ki suka zab'a miki shine alkhairi agare ki", tsaki Salma taja tace " ni tashi ki raka ni gida ma zanje", "kai da wuri haka". Suka mik'e gaba d'ayan su suka rako'ta bakin titi suka koma.

Mufeedah da Mahmoud shak'uwa da soyayya mai k'arfin gaske ne tashiga tsakanin su, inda Mufeedah take ji babu wanda ya kaita sa'ar miji aduniyan gaba d'aya.

Bayan sati d'aya Mahmoud ya shirya ya tafi da matar sa Mufeedah garin Lagos inda yake aiki nan ya kama musu gida suka zauna, inda Daddy yasa a sama mata admission a Unilag, hakan kuwa akayi.

MAHMOUDWhere stories live. Discover now