Chapter 25-26

168 12 0
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
  💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

Today is your day Khadija Yusi, wish you happy belated birthday dear. Fannah loves you more😘

I want to use this medium to congratulate my dear friend Aisha(lady fulanee) in completing her most sweetest novel HADEEYA. Welldone dear Allah ya kara basira da zakin hannu.😘

25 - 26

    Suna isowa gida Mummy ma tayi welcoming 'yarta Mufeedah da murna. A ranar sai da sukayi celebrating zuwan ta. Musty sai da ya fita da su yawo da yamma koda Mummy tace subari ta huta sai suje gobe amma Musty yak'i.

     Yaune first day na Mahmoud a office d'inshi daga 'Stephen Enterprises' a Lagos dan karatun Business administration yayi. Babu laifi the day went smooth for him but da ya tashi gaba d'aya a gajiye yake saboda tun safe har sai yamma suke tashi dan haka yana zuwa gida ya wasa drugs nashi ya kwanta.

      Sai da daddare Engr. da Daddy suka zo gida tare nan Engr. Yayi dinner'r sa yayi sallama da y'ar sa ya fice gidan sa.

       Washe gari Musty yace su shirya zasu sake fita yawo su Jannat dai albarkacin Mufeedah suke ci.

       Kwalliyar da Mufeedah ta cancare yau har yafi na jiya. Blue jean trouser da pink rigar da ya zomata har guiwa tasa tayi d'aurin ta na zamani da pink tie tasaka flat shoes and hand bag blue, light make up tayi amma tayi kyau sosai.

       Musty da yaga jiran da yake musu a waje ya ishesa ya yashigo har zuwa d'akin su yana fad'a "kai wai me kuke ne haka kuyi sauri mu tafi mana". Jin kamshin turaruka kala daban daban suna tashi a d'akin yasa ya juya ta inda zai ganta.

     Tsaya wa yayi kamar gunki a wajen ya kasa motsa wa dan sabar kyau da tamar. Ita kuwa bata kula da kallon da yake mata ba tace " haba ya Musty ai kaima kasan da mata zaka fita fa dole kasha jira ai" ta mik'ar da hannun ta kan gado ta d'au jakar ta.

     Takawa yake ahankali zaije wajen ta Jannat da ta lura da hakan gyaran murya tayi da gangan dan tayi distracting d'insa tace "kai ya Musty to muje mana". Nan ya ma Mufeedah smiling yace " kinyi kyau Baby", "Baby!" Jannat tayi exclaiming da k'arfi.

      Ita ma Mufeedah'r fari tayi da ido a ranta tace _wow baby! me yake nufi da hakan? Ya sha wuta na kenan. Crush number 1 @ kd_ ta ciza leb'an ta na k'asa Jannat ta kama hannun ta suka fita.

      Gaban motar Mufeedah ta bud'e ta shiga da sauri, suna had'a ido da Jannat ta mata signal. Dad'i Musty yaji ganin ta a gaba. Cool music ya kunna musu tare da a.c. Sai ji sukayi Mufeedah na mamin wakar.

      Tsaya wa yayi yana admiring cuteness inta while tana wakar tana kad'a kanta ga gum da take chewing magestically hankalin ta kuma na kan wayar ta.

      Jin har yanzu bai tada motar ba yasa Jannat ta lek'o ta gansa yana kallon Mufeedah.

      Mintsini ta masa a kafad'ar sa ya saki k'ara "auch". Nan Mufeedah ta d'ago kanta ta gansu da smile on her face tace " lafia akwai wanda muke jira ne?" Shima d'in murmushin ya sakar mata ya kunna motar.

      Jannat ko dariya kawai tayi suka fice a gidan. Tunda suke kan hanyar satar kallon ta yake har suka iso cikin Galaxy Mall.

      Ko da suka sauko gaba d'ayan su Musty zagaya wa yayi ta wajen Mufeedah suka shiga ciki.

      Duk wanda ya kalle su gwanin sha'awa suna hira suna takawa.

      Siyayyar su suke yi suna zaga wa sai Mufeedah ta tsaya wajen card cabinet tana karanta love messages dake jiki Jannat ta mata dariya tace "shima d'au ka wa zakiyi?" "Eh mana ai dole nakaiwa Habiby na", " amma Allah kina ji da Muhammad d'inkin nan", ta juya tayi gaba.

      Musty ko da yaji zata d'auka wa masoyinta sai yaji haushi haka kawai bai san dalili ba. Mufeedah na kallon sa tace "ah kai ma zaka d'auka wa Anty'n mu ne ya Musty?" Murmushi yayi shima ya bar wajen.

      Da daddare suna zaune gaba d'ayan su suna hira a parlour Mummy tace "Allah sarki d'ana Mahmoud naso shima yana cikin mu yanzu", Daddy yace "toh bari na k'ira sa mana".

      Daddy yayi dialling number'r shi yasaka a hands free bugu d'aya ya d'aga. Saida kowa ya matso ya gaisa da shi banda Mufeedah. Daddy ne yace masa " Mahmoud ya baka tambayi Mufeedah ba bacin kasan tana nan? Zo ku gaisa Mufeedah" yana mik'o mata wayar.

     Mahmoud ko tab'e bakin sa yayi yana tunanin shifa an damesa da wannan Mufeedah'r ko ya take ne oho. Muryan ta da yaji ne yakawo da shi daga tunanin "hello ya Mahmoud ina wuni?" Har tsakiyar kwakwalwar sa yaji zak'in muryan nata, kasa amsa ta yayi har saida ta sake magana sannan yace "lafia..." zai k'ira sunan ta sai yaji yamar nauyi a bakin sa sannan yace "ya gida?". Ta ansa shi suka gama ya ajiye wayar.

      Lumshe idanun sa yayi yana jin muryan ta na masa yawo a kunne sai kuma yace " why am I feeling so strange about this girl?".

*Kuyi hakuri zakuji ni shiru na kwana biyu saboda hid'imar Sallah, ayi celebrating lafia.*

Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now