page 4

3.1K 249 1
                                    

*🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*A gaskiya kuna sakani farin ciki ba kadan ba,sena tattare dukkan nazari na da tunani,ababen dake sarquwa a kwanyana dan gane da aika saqon fahimta duk se su tsaya cak,ni kanyi mamaki matuka yanda kuke nuna kaunar ku ga rubutuna duk kuwa dayake nidin karamar su ce acikin marubuta.....a wani bangaren mamakine kan kashe ni duk na tuna a shafin farko na book nawa kuke fara comments,dan Allah ku yarda dani ina sanku har raina*

04
Wuraren karfe 9 na daren ranar ya kuma kiranta amma sabida hafsa tafishi zuciya ga kuma rashin daukar raini ya sanya taki dagawa,msd col biyu ya bata,ranshi yaji ya sosu ba bad'an ba, daba dan momy bace wlhy Wannan Yarinyar da tayi kadan yasani sarai tana ganin col nashi tamasa banza,amma zata fahimci baya daukar raini Idan tashigo hannun shi....a bangaren Elham kuwa ta kudiri niyyan bazata kara daukar wayar saba,tunda kullum burin shi ya bata mata rai,ita banda munafurci ma batasan meye na kiran taba,washe gari kuwa bata ma tafi da wayarta sashen momy ba haka taje saddan,ayyukanta tayi tazo ta zauna cin abinci tare da momy da feenah,wayar feenah ya soma ringing, dagawa tayi ganin yaa Abdul ne

"Yaa Abdul ina Kwana" be amsata ba yace kije gidan su Elham ki kai mata Waya Kokuma kice da ita nace lallai ta kirani yanzu" tana kokarin sanar masa Elham na kusa kurun ya datse wayar tabe baki tayi ta kalli Elham tace

"Elly ina wayan kine?"" Kallonta sukayi har momy,sannan tace

"Tana sashen mu,agida na barta" dan yake tayi tace "Gwaramun me martaba ya kirani ban dauka ba nasan ze fahimci bana kusa akan yaa Abdul ya bani ko half msd c ne Idan akwai,ya tsani ya kira mutum yaqi d'agawa ko alama,yanzu kinga masifa yake wai na sanar dake ki kirashi yanzunnan" batayi magana ba shiru kurun tayi momy ce tace "ki tashi kije ki kirashi yanzu" mikewa tayi jiki ba kwari taje gidan msd col hudu ta tarar Nasa ,seta tsinci kanta da kasa kiranshi tsoro me tsanani ya shige ta,ta sani bazata iya gaya mai bakar magana ba amma fa batada juriyar wulakanci,tsaf zata kashe masa Waya Idan yanemi gaya mata ba daidai,daga karshe dai phone nata ta kashe gaba d'aya.... Ba ita ta koma part d'in momy ba se bayan isha sannan ta Shiga, suna wa momy tausa wayar feenah ta fara ringing tana dubawa taga Abdul ne,tana daga wa yace "Idan Elham tana kusa ki bata yanzu" batare da tayi magana ba ta mikawa Elham waya,tana karba tabar wurin seda tashiga d'akin momy sannan tace cikeda faduwar gaba

"Assalamu Alaikum" cikin tsawa yafara masifa

"Ke Elham me kika dauki kanki ne? Tun yaushe kike ganin col dina bakya dagawa kuma bakya kira back,kuma tsabar raini seki kashe wayar gaba daya,me kike tagama dashi kazama dake,ke badan umarnin iyaye ba da kin isa na rab'i hanyar dakika bima,iyayena naso su miki gata amma kina wulakanta musu yaro,ke bakisan halacci ba ko,dama mana tsinatacciyar mage ai bata mage,kisani wlhy talaka irin ki nafi karfin wulakanci daga wurinta,alkawrine nayiwa momy zan kiraki kullum so uku arana,dabadan uwa na uwa ba wlhy bazan kara kiran kiba,jaka kawai dabata san girman na gaba da itaba,kuma Idan kin isa Nakuma kiranki kimun banza,zan miki uzurin bakya kusa amma wlhy bazan miki uzurin rashin kirana back ba,idan katin wayane bakida zan miki VTU yanzunnan" kukane ya kwace mata,jin tana sheshekar kuka yasanya ya kashe wayar dak'yar ta iya saisaita kanta ta koma parlor d'in, momy ta zata wayar arziqi sukayi se washe baki taki,a daddafe ta gama abinda take ta koma gidansu,wanka tayi sannan ta kunna wayarta tayi adu'o in Kwanciya Sekuma ta kasa baccin ta soma kuka me tsuma zuciya,a haka ranar ta Kwana kuka tana mejin zafin zagin wulakncin da yamata,a rayuwar ta ta tsani a Rena mata iyaye da talaucinsu ko sabida kurun suna karkashin inuwarsu bashi ze basu damar wulakan tasu ba,mijin da zaka yana maka zagin na tozarci tunkan ayi auren hmmm...washe gari da ciwon kai ta tashi dama kuma sn fara final exam na kammala secondary skul,ranar ba skul basuda Exam kasa yin komai tayi,Wuraren 9 wayanta yafara ruri janyo wa tayi a wahalce,ta kara da kunne "Assalamu Alaikum" "Alaikissalama" ya fada cike sa isa

Hafsat ElhamWhere stories live. Discover now