page 24

2.3K 179 3
                                    

        *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                            24
Zaman dirshan Abdul yayi ya qurawa Hafsat ido ganin ba'a ga sultan ba kwana uku ya sanya ko magana batayi kuma batacin abinci,shi d'in ma ba abincin yake ciba amma dai yafita dauriya kodan kasantuwar sa namijine oho,kyakyawan murmushin k'arfin hali ya sakar mata sannan yace "Blossom na plss kimun magana mana,nace Meyene kike sn ci na girka miki da kaina?" K'ur tamasa da ido kawai batace kanzil ba,hannu ya sanya ya tura hularsa bayan kansa ya shafi sumarsa

"Innalilahi wa inna ilaihiraji'un" itace Kalmar daya keta nanata,tashi yayi yabar wurin batare daya qara cewa komai ba,d'akinshi ya Shiga ya rusa uban kuka tamkar wani k'aramin yaro abubuwan sun had'e masa ga rashin sanin halin da sultan Hake ciki,gashi kuma Elham ko magana batayi bata kuma cin abinci,sanda yayi me isarsa sannan yazo ya dagata cak zuwa d'akin barcinsu,kwantar da ita yayi ya daura kanta saman hannunshi cikeda rarrashi yafara magana

"Hafsat dan Allah ki sassauta wa kanki yau kwanaki nawa bakyacin abinci kuma bakyawa kowa magana,dan Allah na rokeki ki nutsu kiyita adua,wlhy kina k'aramun damuwa ne mara misaltuwa,idan dai baso kike na haukace ba dan Allah Kici wani abin" kuka kawai ta saka ta rungumeshi k'ank'ameshi sosai tayi

"Yaa Abdul Nashiga ukuna har yanzu fa ba koda labarin sultan,wlhy zautar dani zasuyi idan ba'a nemomin sultan ba mutuwa kawai zanyi,me wannan d'an ta tsitsin yaron ya aikata wa mutane,yaa Abdul dan Allah ka taimaka ka nemonin sultan d'ina" k'ara matseta yayi ajikinshi yana jin zuciyar na masa tafarfasa lokaci d'aya kuma yanajin tamkar zuciyarsa Zata Faso k'irjinsa ta fito har cikin b'argonshi yakejin tausayin ta matuk'a wanan damuwar da hafsa ke ciki na cikin abin da ke qara harzuqa Abdul,rarrashinta yashigayi har bacci ya d'auketa"

     Wuraren k'arfe d'ayan dare me gadin gidan yaji motsi ana k'ok'arin bud'e k'ofar gate d'in a hankali yazo ya wuce jikin k'ofar gidan ya tsaya wayanshi ya janyo yakira Abdul,ya sanar masa,betashi Elham ba amma sarai taji sanda yake wayar kasancewar dukkanin su bawai baccin sukeba sedai dayake bacci b'arawo ne yakan sacesu wani lokacin suna tsaye a lab'e ya samu nasarar bud'e k'aramar k'ofar gate d'in da buhu D'auke a hannun shi ya ajiye ze juya Abdul yace me gadin ya bishi  da gudu me gadin ya bi bayanshi kan yakai k'ofar ya rafka masa uwar sandarsa,take ya fad'i wurin a sume,Shikuwa Abdul da sauri wurin buhun yayi wari ne yabugi hancinsa tunkan ya qarasa bud'e Buhun daurewa yayi ya haska fitilar wayarsa ya qarasa bud'e Buhun "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" itace kalmar dayake ta nanata wa yayinda yayi mutuwar tsaye warin ma ya denaji sabida ganin gawar sultan harta fara zagwanyewa,Elham da tunda yafito take binsa  isowa tayi wurin batare da sanin saba,ganin sultan a haka Abdul a tsaye ya sanya ta ture Abdul da hanzari ta wawusheshi,mamakine ya kamata ganin fatarshi ta sab'ule ga uban wari alamomi sun nuna yafi kwana biyu da mutuwa, baka ma gane shine seka kula da kyau,hauka cewa tayi ta soma sambatu kankace meye wannan tafita hayyacinta dak'yar Abdul ya riqeta yana bata baki,kallon shi tayi acikin hasken fitilar wayarshi a daidai lokacinda me gadin ya dawo wurin da gudunshi

"Kaga yaa Abdul kalli sultan na,sun kashe shi fa kalli mutuwar wulakanci,kalli yana warin gawa kalli yanda fatar jikinshi ya zagwanyewa daga jikinshi, anya kasan wahalar da yaronnan yake sha kuwa?? Wlhy baka sani ba cewa akayi damu gawa zafi takeji idan ana mata wanka ma,kalli sultan fatar shi duk a sale kalli idonshi,wlhy zafi yakeji yaa Abdul ka tasheshi mana,sudais na be mutuba wlhy" jijiigata yayi yace "kiyi hakuri Elham dan Allah ki nutsu mana,kiyi hakuri kinji" batace komai ba ta k'ura masa ido,se kuma ta kwashe da dariya cikeda hauka tace

"Mesa ba zaka tasheniba ina bacci, yaya zaka barni ina bacci ina wannan mugun mafarkin, dan Allah yaa Abdul muje ciki mana" ganin tana wannan abin ya tsoratar dashi matuk'a....miqewa yayi shima ya kamo hannunta "Elham na plss mana me haka?? Ki nutsu kiji ni da kyau haquri zakiyi kinji k'addara ta riga fata an rigada an cucemu se hakuri" dukan k'irjinshi tayi "so kake kace dani wai ba bacci nake yiba,da gaske kake wannan sultan nane wannan,kalli fa da kyau wlhy wannan kalarshi tsanwa ne ni kuwa sultan na fari ne qal" kurin seta sake saka kuka,a haka ta sulale a wurin bata koda motsi.....me gadin ya kalla yace "waye wancan"

"Wlhy yallab'ai sale ne?" Da mamaki ya kalleshi yace "wane salen kake magana?"

"Sale dai sale wanda ka sani yallab'ai" d'aga Elham yayi zuwa mota yazo ya kai gawar sultan ma yana matsar kwalla,yace da me gadin ya fara d'aure sale sannan ya watsa masa ruwa,zashi asibiti ya Turo police anan d'in........

Sosai Abdul ya girgiza jin cewar kan Elham ya tab'u saka makon wannan abin daya faru da ita,sosai abinda ta gani ya girgiza ta Baza suce bazata warke ba amma fa sam Baza suce ga tsawon lokacin dazata d'auka ahaka ba,sedai abinda Allah yayi,kuka Abdul ya sakawa momy sosai sam zuciyarsa bazata iya d'aukar wannan abin ba,wanda ya kawo gawar kuwa anyi anyi dashi Amma sam yaqi magana....

    A firgice Elham ta farka tana kurma uban ihu tana sambatu "Wai cewa suke dani Sultan ya mutu ni sam sultan d'ina be mukuba yaa Abdul me shine shaida agabanshi nabashi mama yasha,se kuma tasaka kuka tasoma kokarin kunce d'aurin da aka mata, sosai ta baiwa Abdul dake kusa da ita tausayi yasoma sharar k'wallah " Wlhy sun kasheshi kisan wulakanci fa ko binnewa beci albarkacin suka masa ba,gaskia nima sena kashesu,kuma bazan binne suba sesun dawo k'asusuwa sena mayarda su...sekuma ta kwashe da dariya...Abdul barin d'akin kurun yayi cikin tsananin k'unan rai ilahirin mutanen dake d'akin kuka sukeyi na matukar tausayawa Elham.

Mom Nu'aiym.

Hafsat ElhamDonde viven las historias. Descúbrelo ahora