page 30

2.3K 180 0
                                    

☀️Hafsat Elham☀️

HASKE WRITER'S ASSO.

Wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa GA qawata Hafsat Abubuakar qaya.

30
Ethan abun duniya ya isheta,ta Kasa gane inda zancen Abdul ya nufa kome Tamasa ai bata cancanci wannan d'anyen hukuncin ba, shin Anya Kuwa Abdul Yasan Abinda yake shirin aikatawa? Da sauri ta miqe ta zari key na motar ta ta nufi fada tuqin takeyi Kawai amma Sam hankalinta baya Kan abinda takeyi se uban Kuka takeyi bata tab'a Zata cewar haka azabar kishi yakeyiba ji takeyi tamkar zuciyarta zata faso qirjinta ta fito wani tafarfasa da d'aci zuciyarta ke Mata ikon Allah ne kadai yakaita fada lapiya, Ko lucking car batayiba ta afka cikin gidan Kai tsaye part din mommy ta nufa, a parlo ta Sameta itada Abdul Suna hira Kai tsaye Saman cinyoyin mommy ta d'are ta soma Kuka da sambatu

"mommy Dan Allah Kiwa yaa Abdul magana yamun rai idan wani abun namasa yayi hakuri wlhy banason kishiya banso ya had'ani da kowa, karatun Kuma da bayaso shima na dena bazan ma koma qasar ba" kukan takeyita baji ba Gani,d'agota mommy tayi " Elham Karki Zamo cikin mataye Marasa yarda da k'haddara ina tunkafin kuzo me gidanki ya sanarmun Kinsan komai, shine kuma Yanzu zaki biyewa mutane su rikitar dake a karin banza,ina nan ina faman saka Miki albarka akan yarda da khaddarar dakikayi Ashe ba haka bane zaki biyewa mutanen banza su kaiki su Baro,to ki Sani zamu b'ata dake kishiya ba abun gudu bace 'yar uwace kuma abarso,karna kuma ganin kin Tashi hankalinki Akan zancen kishiya tunda mijinki Yana qaunarki, Maza tashi ki koma dakinki yanma nayi" mamakin Jinwai tun Kan Suzo ta Sani takeyi amma batace da mommy komai ba Tamata godiya jiki ba k'wari ta Kama Hanyar waje tun a Hanya kafin taje gun mota take ganin Jiri ya soma kwasarta har Abdul yafito tana nan bata qarasa gun Mota ba tana tafiya tana bin bango tana layi ,ta bayanta ya tsaya Yana nazarinta Harga Allah badasan ranshi zeyi aurennan ba amma yana mamakin sanda Elham tayi wayewar aikata abinda ta aikata ba wannan kadai zeyi ya rage jin zafinta aranshi, da k'yar ta isa mota koda tashiga ma sam batasan me yakeyiba, Allah shiyake halittar mata da mishi amma Elham tana daga cikin mataye Masu azababben kishin tsiya, da k'yar ta iya yin rivers ta harbawa motar wuta ,mahaifinta ma dayaqi yarda ya dena aikin gadin binta yayi da Kallo harta bacewa ganinsa ganin yanda batako tsaya sunyi sallamaba kuma yaga ta sharara da wani uban gudu na Allah ya kiyaye....... Ganin haka ya sanya Abdul juyawa ciki aranshi yana Mata aduar sauka lapiya.

Yana nan zaune wayar mommy ya soma ringing,d'agawa tayi ganin baquwar lamba ya sanya ta ajiye bata d'agaba ta mayarda dubanta Zuwa gareshi tace

"Babana lapiya dai ka tafi kuma ka dawo? " Sosa kanshi yayi yace " Kawai Naji bazan iya zuwa gidan Yanzu ba" kan tace wani abu wayar yafara ruri a Karo na biyu,ganin Sunan Elham NE, da Sauri ta d'aga

"Mamana ya akayi? " muryan namiji tajiyo "Haj bame wayar bace tayi accident Anan kan Hanyar government house kuma gata a kwance sedai ace Allah ya sauwaqa, Yanzu zamu wuce da ita babbar asibitin kwararru ta jiha shine muka Kira ganin Kamar number dinkine a sama kuma munma Kira wacce Muke tsammanin ta mijintane amma be d'aga ba" miqewa momyn tayi da salati d'auke abakinta

"Malam injin dai Tana da rai? " ta wurgo masa wannan tambayar "Haj bazan iya cewa komai ba, Sabida banida masaniya,kurun dai na kula she's unconscious" a gigice ta ajiye wayar ta Kalli Abdul

"Babana tashi muje ba lapiya, Elham tayi accident a Hanyar government house" haukace mata ne kurun beyiba amma Kam ya kusan zaucewa, Kasa tuqin yayi kurun yafito ya tsaya yana tunanin wane Hali Illy take cikin, seda driver yazo yajasu,suna zuwa wurin da akayi accident d'in Abdul ya dakatar dasu Kallo daya Abdul yayiwa motocin guda biyu zufa ta keto masa Sam dazaran kaga Motan Elham Kasan akwai Marsala, fitowa yayi yaje wurin mutanen dake tsatsaye a wurin " Malam Dan Allah meya faru? " ya tambaya bayan ya musu sallama "AI malam wlhy wani mummunan hatsarine ya afku, wata yar matashiyar budurwace tazo dagudu k'addara ta afka mata Kasan wani lokaci idan ajalin mutun yazo bayan Sanin me yakeyi kurun baiwar Allah nan tayi maja da waccen motar ta ibar yashi kaga yanda motar ta ta dawo wlhy malam bakaga yarinyar ba gwanin ban tausayi ni inaga wlhy ko aure batayiba amma mutuwa tazo mata a bazata" wara idonshi yayi ya dafe k'irjinshi dake masa zafi yajuya zuwa mota maganganun da mutumin ya fad'a suna masa yawo aka, ya Kasa gaskata zancen mutumin,koda yashiga motar suna masa maganr kasa amsasu yayi kukan ma ya gagareshi a haka har suka k'arasa asibitin, shine ya fara fitowa daga cikin motar ya nufi cikin asibitin.....

Kallon nutsuwa likitan yayiwa Abdul kan yace " Yarima tun kafin faruwar wannan accident d'in binciken mu ya nuna mana cewar matarka na cikin matsanancin damuwa, Zama mu iya cewa shine yayi sanadin wannan accident data Samu Sabida Tana d'auke da matsanancin ciwon zuciya Wanda akalla zefi shrkaru goma acikinta faruwar wannan abun ya sanya gaba d'aya ya taso mata lokaci d'aya had'uwar sa kuma da wannan accident yasanya kuma lokaci d'aya zuciyarta ta buga!!!" cike da razani Abdul ya d'ago ya kalleshi "Bugawar zuciya fa kace doctor? Mekenan Kake shirin sanarmun? Kuma ni iyakar sanina matana batada ciwon zuciya mema ze haifar mata da ciwon zuciya??" tasowa likitan yayi ya zago ya dafa kafad'arsa yace "Abdulrahman ko bansankaba bazan make k'aryaba balantana muntaso Dakai tun Muna Tara atare, ba dalilin maka haka,abu na gaba kuma ka sani matarka wannan ciwon ya jima ajikinta Danma Tanada qananun shekarune ya shekaru ne ya sanya be bayyana kanshi ba,na tabbatar damuwane ya haddasa mata wannan accident d'in Sannan kuma fad'uwar gaban data Samu yamun faruwar wannan Al'amarin shine ya haifar mata da Bugawar zuciya sabida a zahirin Gaskia bataji wasu raunuka masu yawaba dazasu kaita ga wannan abinba, buguwane kurun Se goguwa kad'an" nisawa Abdul yayi cikeda damuwa

"To Yanzu doctor Meye abinyi?" shima doctor d'in nisawa yayi kan yace " Tsakani da Allah Abdul duk duniyarnan babu Wanda ze iya sanar maka halin da matarka zata kasance daga Yanzu zuwa kowane lokaci Allah ze iya bata lapiya kazalika daga Yanzu zuwa ko wane lokaci zata iya Rasa rayuwarta!" miqewa yayi "Haba Dr marwan ai ba'a Yankewa mutum hukunci irin haka, nasan Allah shike rayawa da kashewa amma Dan Allah ka taimaki rayuwar Hafsat da ikon da Allah ya maka kaji" Sosai likitan Yamasa bayani akan ciwon Nata sannan Yakoma d'akin da take ya qura mata Manya Manyan idonshi yana sauke siraran hawaye a hankali aranshi yanajin zafin abubuwan daya aikata agareta gani yakeyi tamkar ciwon zuciyannan Nata shine sanadi,momy ce tazo ta dafashi Taja hannunshi zuwa cikin d'akin tanemi sanin Meke damun Elham yana kuka ya sanar mata komai da doctor ya fada masa, ya qara da cewa

"Mommy wlhy nasani nine Sila,wata qila zafin qaryar dana mata ne nace dake tasan zanyi aure batasan da zancen ba dawowarnan namune dazu takeji abakin Raihan, kuma Nafi watanni uku Bana kulata akan naga Tanasha qwayoyin Hana d'aukar ciki na sanya ta dakatar da aikinta na kuma tilastata barin zuwa makaranta, sabida taqi dena zuwa makaranta ya Sanya nadena shiga harkarta kuma na dakko zancen aure batare da sanin taba,hasalima yarinyar dazan aura ban Santaba seda Nazo nan Moh ne yanemamun ita dukdan na baqanta Ranta a zatona batasan haihuwa danine sabida taga qaddara na yawan fad'awa zuri'armu, Yanzu abinda doctor kecemun dama Anaso suna d'aga wa haihuwa qafa sabida condition nasu lapiya bata wadacesuba" Sosai mommy ta zazzaga masifa daga baya ta saka kuka sabida batasan yanda zatayi ba inhar Elham ta rasu .......

*Bayan Sati biyu*
Elham taji sauqi Alhamdulillah, sedai har wannan lokacin batawa Abdul magana, idan ze shekara yana mata magana sedai ta tasashi agaba da kuka, bata ce masa ci Kanka amma takan d'an tab'a hira dasu mommy, Suna yawan kwantar mata da hankalin Kamar yanda doctor yace, a haka har taji sauqi ta warke Sarai aka sallameta....... A yanda Elham ta zata yau saura Kwana uku d'aurin auren batada labarin cewar tun Ranar datayi accident mommy ta Hana wannan maganar kuma Koda bata hanaba abun gaba d'aya ya ficewa Abdul akai,tana zaune a parlo ta gama Shan magungunan ta tana kubar fresh milk a hankali,zuwa yayi ya zauna kusa da ita yajanyo hannunta ya cura a nasa "Blossom ya jikinki?" da dan mamaki ta kalleshi kasancewar tasan ya dena kiranta da wannan sunan, a hankali ta kalleshi ta saya d'an murmushi a fuskarta sannan tace "Ango kasha mai Yanzu Kake shigowa" murmushin Shima yayi "Angon hafsatul Elham ba" bata kulashiba Yakuma cewa

"Blossom Dan Allah kiyi hakuri ki gafarceni abin da na miki,wlhy Sam banzata akwai dalilin ki Nashan k'wayoyin Hana d'aukar cikiba kuma zancen auren danamiki Shima na janye har abada" gyaran murya tayi tukunna tace cikeda nutsuwa

" Bance ka fasa auren kaba sabida ni nayi kad'an na haramta maka abinda Allah ya halatta akanka sedai Nasha mamakin sauyawar halayenka akan laifin da bakayi bincike akanshi ba,sabida ina tunanin damuwar dazaka Shiga idan har Kaji cewar ina cikin wannan halin na ciwon zuciya na boye makane sabida Karka shiga damuwa Nabi sha'warar doctor ne nayin tsarin Iyali sabida condition nawa,nakuma kasa sanar maka sabida kurun Karka gano ciwon dake damuna kashiga damuwa, Ashe Kai a wurinka ba haka bane kana iya watanni baka kulani zabida Kawai Dan wannan abin,amaimakon ma kazo ka sanarmun laifin dana maka Seka dauki wannan matakin" D'an dakatawa tayi sannan Taci gaba " Dama kaje ka auri wacce kayi niyyar auren Danni wlhy bazan zauna dakaiba kaficemun arai kuma karkayi tunanin samuna akusa" tana gama fad'ar Hakan tamiqe tabar wurin,da ido kurun ya bita bezata words Nata har zuci bane.......

Wasa Farin girki fa Wuni d'aya cur ba Elham ba kayanta ya zaga gida da dangi kaf be gantaba kuma wayarta akashe hankalinshi ya tashi Matuka bashiba bar mommy......

Mom nuaiym

Hafsat ElhamWhere stories live. Discover now