page 21

3K 188 5
                                    

         *🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

                             21

Momy nifa na damu sosai,Shiyasa naketa gudun wannan auren da baiwar Allah nan,yanzu gashi sunaso su firgita y'ar mutane,kuma abun haushin nine batasan koda gani wlhy"
"Babana ka kwantar da hankalinka Mlm na Maiduguri nakan hanya fa,inshaa Allah komai zezo da sauqi" shiru be tankaba sabida bashida abin cewa d'in.....da yamma Mlm yazo,a d'akin datake kwance aka kaishi domin ya dubata  ,adua aka Shiga yi mata da karatun alqur'ani amma abin mamaki ko gezau ba tayiba,kallon me martaba Mlm yayi yace

"Wannan asiri ne kuma suna sane da zuwana,dama abin tsoratar da ita kurun yakeyi bawai ajikinta yake zama ba,an sanya mata qiyayyar mijinta ne dakuma gidanshi shi gaba d'aya wata halitta yake zo mata me matukar ban tsoro sabida haka inaga se zuwa gobe zamuyi maganin abin" godiya sukayi masa Abdul ranshi a bace yake wayene yakeso ya rabashi da farin cikin rayuwarsa Ellyn sa,aikam idan ya kamashi seya yabawa aya zaqinta..... Dama ya baiwa kallamu motarsa akai masa wurin wanki se kurun yayi amfani da d'aya daga cikin ta gidansu,ya wuce gidansa domin dauko wani sako, mamakin ganin khamis na magana da me gadinsa yayi matuka,k'in karasa wa yayi har k'ofar gidan,parking yayi daga gefe ya tsaya yana kallonshi harya gama bashi wani qulli a Leda yana nuna masa yanda ze bad'a mamakinsa ne ya qaru ganinfa ya Ciro kud'ad'e ya baiwa me gadin,yana gurin harya masa sallama yabar wurin kai tsaye shima yafito daga motar har yana had'awa da gudu ganin me gadin yashiga cikin gidan yana kunce k'ullin,labewa yayi yana kallonshi ya barbade tundaga kan inda yake parking har zuwa matattakalar dazata sadaka da k'ofar Shiga gidan,yana dawowa gate ya ganshi atake rashin gaskiya qarara ya bayyana a gareshi,murtuk'e fuskarshi yayi yace

"Ard'o me kakeyi acikin gidan ne?" D'an Sosa kanshi yayi yace "Ban d'aki naje yallabai" miqa masa key na cikin main Gidan yayi yace "A parlor Idan ka Shiga zakaga jakar computer na saman kujera ka dakko mun" muzu muzu Ard'o yayi baya son shiga,Abdul yayi yai dashi yaqi,aikam a waya yakira Baba k'arami da Ashraf ba'afi mintuna goma sha biyar ba se gasu sun iso a tare,

"Yaa Yarima lapiya dai" agaban Ard'o ya zayyane musu komai,yace yanzu kunga na aikeshi yaqi Shiga menene shawarar ku?" Ashraf ne yace "Na rantse da Allah seya taka masifar daya barbad'a ta koma masa" atake kuwa ya kira wani Friend d'inshi soja,suka zo suka dannamai bindiga dole yana kuka ya taka,aikam yana dawowa wurin yafara soshe soshe haukan tuburan Ard'o ya haukace,seda suka d'aureshi,kai tsaye kuwa akaje aka kamo khamis sojojinnan suka Hau jibgarshi da kanshi yayi confess ganin zasu aika dashi gaba da lahira....wani soja da haushi ya isheshi bindiga ya kwala masa yace

"Wancen Ibrahim da da ze auri Hafsat,dakuma Abdul Kaine Kayi asiri har wancen ya mutu ko?" Gaddama yayi aikam suka Shiga dukanshi dole ya fad'a waida so yayi duk su mutu sabida yanaso ya auri Elham,take aka wurga hege ga hukuma akan yayi kisan kai yana kuma shirin haukatar da wani akan mace.....abinda yafi baqanta wa Abdul rai shine ciwon daya sakawa Hafsat,seda aka kama har bokan dake masa wannan mugun aikin ya karya komai shima yaga kanshi court d'an banza mushiriki....

*Bayan kwana biyu*

     "Momy nifa na tsorata da garinnan,abin ya wuce cikin gida amaka asiri harda na waje,abun ai yayi yawa wlhy,gaskia ni London zan d'auke Hafsat mu tafi Yafiye mun kwanciyar hankali" Murmushi momy tayi"Ba wanda ya isa ya hanaka tafiya da matarka duk inda kaga dama ammafa kasani ko ina kuke se ku riqe Allah,dan ka bar katsar bashi bane,lafiyar Allah zakana riqa nema muku ako da yaushe ana yawaita karanta alqur'ani me girma ana adu'a, sannan kuma seta mirmire zaku tafi" b'ata fuska yayi

Hafsat ElhamWhere stories live. Discover now