page 9

3K 226 3
                                    

*🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*kandy  kishiyar Mrs j moon,Wannan nakine Mrs j moon k'awata ta roka abaki,wai kina kuka an bata kyautar page ke ba'a bakiba so chill Wannan nakine ki mata godiya lolxx*
      
                            9
Koda ta kammala wayanta ta juyo ya tafi,kwanciyar ta tayi bata kawo komai aranta ba,harga Allah ita be wani dameta ba,shi kuwa moris kasa koda kwanciyar yayi aranshi yana tunanin wanene Ibrahim? Hankalin shi ya tashi matuka,ya kasa gane mesa ya damu haka,wani barin na zuciyar sa yace dashi,kishi kishi ke damunka Abdul,yayin da d'ayan sashen na zuciyar sa yace dashi,kurun sabida zaka aureta ne bakajin dadin ganin tana huld'a da wasu mazan, "that's all" ya fad'a a sarari "Mema ze saka Nayi kishinta tunda ba santa nakeyi ba nikam" wanka yashiga ya fito ya saka jallabiya ya kwanta amma ya kasa bacci har karfe biyu na daren ranar idon sa biyu....cikin bacci Elham tasoma jin bata iya numfashi da kyau,dama kuma da mura sosai ta kwanta har tari takeyi,feenah ta tayar tace da ita "Feenah I'm sick,I cnt breath well,could u plss help me with my inhaler?" Mik'ewa tayi da sauri ta kunna side lamp d'in d'akin tace "Where d u keep it then,seda nace karki sha Wannan kayan sanyi amma bakyaji" kasa ansata tayi sabida abin ya taso mata sosai,ko ina feenah ta duba bata ga inhaler d'in ba,wayar ta,ta janyo takira Ashraf yana d'agawa tace dashi "Kazo yanzu plss Athsma d'in Hafsat ya tashi kuma gashi na duba ba inhaler d'inta" tashin baba karami yayi yace "Plss ka tashi muje gunsu feenah Waifa er matsalar nan Elham Athma d'inta ya tashi,shine zamuje muga halin datake ciki,zuwa sukayi suka yi cirko cirko akanta,se neman inhaler akeyi ita kuma tana fama da kanta, Ashraf ne yace " kaga K'arami kira yaa Abdul....." Yana zaune yana salati ya idarda da nafila kasance wa ya kasa bacci sabida tunanin Wannan Ibrahim da Elham ke waya dashi,yaji phone nashi na ringing,harta katse be tashi ba,harga Allah be kawo komai aranshi ba haka call d'in ya k'ara shigo yayi banza dashi,a tunaninshi wani balarabe ne dasuke huld'a dashi kasan cewar Su yanzu gari ya dade da wayewa,ganin fa Elham na shirin shrqewa ya sanya Baba karami ya soma danna mata k'irji,feenah ce tace "kunga dan Allah Kuzo mu kaita asibiti, Wannan athsma d'infa Idan ta tashi mata dole se anmata allura,da d'azu ne ma akaga inhaler ze sauka amma yanzu yayi nisa aminipilin injection kurun za'a mata ya sauka" Raihan ce tace "Hakane amma Inaga mu fara sanarwa Yaa Abdul koda ta zuwa d'akin sane tunda yana kusa" Ashraf ne yaje ya masa knocking,da mamakin sa ya bud'e ya k'urawa Ashraf ido,a rud'e Ashraf yace

"Zata mutu wlhy yaya mutuwa zatayi" kallon shi yayi da mamaki dauke a fuskar "kai ka nutsu mana wacece Zata mutu?"
"Yaa Elham ce fa Athma ya tasarwa,munyi kiran wayarka baka..." Ai bankeshi kurun Abdul yayi be tsaya ya karasa jin zancen ba,da gudu ya Shiga d'akin ganin k'arami na dannan mata k'irji ya sanya yaji wani bakin ciki ya taso masa,hawa kan gadon yayi ya dagota saman cinyar sa,gani yayi sam bata numfashi bata ma motsi rikicewa yayi lokaci daya ya kwasheta suka rufa masa baya seda ya sakata a mota sannan ya tuna da key,dagudu yaje d'akin ya had'o da wayanshi da ku d'ad'e,asibitin dasuka kaita ranar ya nufa,da sauri suka karb'eta aka danna mata ox da komai da injections,Abdul se zirga zirga yakeyi dawowa wurin Su Ashraf lokacin sun dawo sallar asuba yace "Waiku kuwa wane iskancinne ya hanaku kirana tun d'azu Idan da wani abin ya samu Yarinyar mutane me zakuce?"

"Yaa munfa kiraka baka d'aga ba,ka duba wayarka" kan wani yayi magana doctor d'in yace "Patient naku ta farfad'o,dama kunsan case na athsma yana sauka da Wannan injection da sauri,sedai ku kiyaye abubuwan dake saurin tayar mata da asthma" da sauri yaje d'akin, yana zuwa yaje wurinta ya riko mata hannu "Sannu Hafsat ya jikin?" Murmushi tamasa tace yaa Abdul zansha ruwa dan Allah" da sauri ya bude robar ruwan dake gefenta ya daga ta,asaman jikinshi ya kara ta ya bata tasha,gani yaye ta lafe ajikinshi ya sanya be d'aga taba yace cikin sanyin murya

Hafsat ElhamWhere stories live. Discover now