page 7

2.7K 224 3
                                    

*🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

This is just for u Hafsat,kince 2 pages to gashinan kyauta,plss be happy.

                            07
         Uban waye kike zance dashi kullum a waje? A ina kika sanshi? Kuma ya akayi yasan kin zonan?" Rikicewa tayi gashi ya mata rikon da bazata iya daurewa ba,take ta fara zubar da k'wallah,

"Yaa Abdul Kayi hakuri dan Allah wlhy anan muka hadu kuma gaisawa kurun mukeyi" wurgar da ita yayi yace "Anan kika sanshi dakika tafi ina kuka had'u? Wato iskancin naki na kula ba akan faruk kadai ya tsaya ba har wasu kartin banzan ko" kukan tane ya tsananta jin furucin shi, janyo ledar yayi yace yana bud'eta "har agogo ma yake baki da turare,shiya sanya kike mu'amala da turarukan dasuka fi karfin talakan ubanki, kin daukar wa kanki rayuwar datafi karfinki ,dole sekinyi abinda wasu masu kudin sukeyi shine kike bin maza ko,wlhy Wannan kaddararren auren da banka d'ad'd'iya irinki asarane,dabadan nayiwa momy alkawarin aurenki ko bayan rantaba ba ba kaddarar dazata sanya na aureki,kuma ki shirya wa kanki zaman kunci a gidana,banza kwad'a yayyiya Wama ya sani ko asircemun iyaye kukayi keda talakawan iyayenki dabasu san halacciba,banza jaka kalli shigar ki menene marabar da yar tasha haihuwar bakin kasuwa,wane me hankalin ne ze ganki ya zaci cewar ked'innan musulma ce? Wlhy an cuceni had'ani dake Hafsat Allah ya isa tsakanina dake, Sekin d'an d'ana kud'arki a hannuna wlhy" fusata tayi yanzu kam tamik'e tsaye tace tana me k'ank'ance idonta cikeda masifa

"I have had enough now yaa Abdul! Nagaji! Nagaji! Kuma wlhy Nagaji! Duk iyakar abinda zakamun zan d'auka amma wlhy karka kuma sako mun iyayena,ba kinnan nawa dakake gani bashida ragowa,ni ba yar iska bace ba,kuma ban gada ba,jikina be taba haduwa dana wani ba dasunan zina kuma duk wanda kemun kallon mazinaciya na Barshi da Allah ciki kuwa harda kai,kasani wlhy badan ina sanka kodan wani abinka zan aureka ba,sabida darajar momy ne kawai dame martaba,naga alama abin naka nasan ya wuce gona da iri kana zagarmun iyaye to my face,ni ka sani iyayenka har abada iyayena ne, kuma duk wanda ya zagesu agabana se inda karfina ya k'are,sabida nasan darajar manya na,zancen zaman k'unci dakake cewa zanyi a gidanka Ai tunba Yauba na shirya wa hakan,bakada wani farin ciki karan kanka dazaka bani da har zanyi mafarkin zaman farin ciki agidanka,zancen yanayin Shiga I will admit it nayi laifi,kuma ina fatan kasan cewar Allah nawa laifin bakaiba so awurinshi nake neman gafara Ba kaiba,so na gode da tunatarwa,dan Allah karka k'ara zuwa inda nake,karka k'ara kirana awaya,kullum kamun d'aya daga ciki da bakin ciki nake kwana,dashi kuma nake tashi,ba abinda yafi mun ciwo irin wai ace mijin dazaka aura shine yake zargin ka....." Kasa karasa wa tayi ta durkushe awurin tana kuka me ban tausayi, Shikuwa jikinsane yayi sanyi,seyake ga koda hakane mazina ciyar ce cin zarafin yayi yawa,beside wane tsautsayinne yakaishi zagin iyayenta,shida kanshi yasani Baba hasan dattijo ne me kirkin gaske,sam bashida hayaniya shekaru kusan talatin yake gagi agidan,tun yana dan shekara 5 aka kawoshi gadi gidan kuma amana ta sanya haryau ba'a sauya wani ba,take yaji ya tsani kanshi kuma se wata zuciyar ke bashi watakil ma ba wani abin Elham keyi itada faruk ko wanin shiba,gwiwa asace ya juya ya bar d'akin gaba daga kansa ya kunce,basu feenah suka dawo ba se shad'a yan dare,zuwa lokacin zazzb'i me zafi yagama rufeta,kanta ba kad'an ba yake Sara mata,zuci yarta zafi takeyi sosai duk sanda ta tuna da maganganun Moris setaji tamkar kasa ta bud'e tashige sabida tsanar kanta da tayi,sosai wutar qiyayyar moris ta k'ara huruwa a birnin zuci yarta, ji take tamkar ta kurma ihu sabida tsananin zafin da kalamnshi ke mata a rai,kwanciyar sukayi batare da sun san meke damun taba,cikin dare Wuraren karfe hudu ta farka da wani razannanen ciwon kai,ga rawar sanyi tanayi jikinta yayi zafi rau tamkar gaushin wuta,dakyar tamatsa kusa da feenah ta d'an bubbuga bayanta,tsaki feenah taja tace dan La Elly rabu dani,bacci nakeji" haka tayita tashinsu basu tashiba,da asubar fari ta mike domin yin Sallah tana matukar ganin jiri,kasawa tayi taje ta kwata,Raihan ce ta tashi ta kunna fitilar d'akin ta dawo ta tashesu itama tashiga ban d'akin tai alwala,tana fitowa taga basu tashiba,ta kara tashin Elham aikam tana mikewa ta sulale wurin ta fad'i,da sauri Raihan ta tareta,jitayi jikinta zafi sosai ,tace "subhanallah Elham dama bakida lapia har haka baki sanar wa kowa ba?" Kasa ansata tayi,dakyar tace "Raihan ku kaini wurin Innah mutuwa zanyi kaina ze rabe gida biyu" feenah ma tasowa tayi tazo ta na tattab'a jikinta rikicewa sukayi ganinta galala,da sauri feenah ta janyo wayarta takira Abdul,yana d'agawa tace " yaa Yarima mun Shiga uku Elham zata mutu wlhy bata da lapia sosai, bata ma iya tashi faa" beyi magana ba ya kashe wayar dama yana d'akin kusa dasu daya kama jiya,aikam da gudun shi ya nufo dakin yayi knocking Raihan ta bud'e masa, yana zuwa ya dauketa ya dora kan gadon,sosai ya rikice jin jikinta tamkar wuta,yace da sauri feenah ta kira masa Ashraf Raihan kuma ta dakko masa ruwa me sanyi da towel,take yafara bata tapinsponge se rirrik'e sa takeyi abinda ya kula ma sambatu takeyi,Ashraf na zuzuwa da kanshi ya kwashe ta zuwa mota suka kaita wata alfijir hospital,likitan yace damuwa ce tamata yawa,jininta ke kokarin hawa amma dai be Hau d'inba,se an bata injection da k'arin ruwa,Abdul ya tsorata dajin Wannan zancen,kaddai maganganun shi na jiya neke daga mata hankali har haka!!! Koda akazo amata allura kasa Tsayawa tayi seda Abdul ya riketa, drip na karewa ta samu karfin jikinta aka sallamesu,Abdul da kanshi yake jinyar ta,Shifa arayuwa yanzu bala'in tausayin Elham yakeji ga masifar kunyar ta dayake ji,ita kuwa duk ta bud'i idonta ta ganshi tsanar sace ke kara ruruwa a cikin zuciyarta.
*Bayan kwana d'aya*

     Yana zaune kusa da ita yana bata ayaba dakyar takeci amma ko kallonahi Bata sanyi yakuma kula da hakan,kallonta yayi cikin sanyin jiki yace "Elham dan Allah kiyi hakuri akan abinda na fada miki 2  back wlhy bacin Raine,abinda na fada bawai har raina bane" banza tamishi ta k'ara dauke kanta,yace "Dan Allah Hafsat kice dani kin hakura mana,nasani kalamai na ne suka jefaki a Wannan halin dakike ciki,dan Allah kiyi hakuri kinji" kuka tasaka masa,Shikuwa ayan kwana kinnan tausayin ta yakeji yarasa dalili wlhy gashi kuma bata bashi fuska,cikin rudu yace "kinga Idan zancen ne bakyaso kiyi hakuri na dena wlhy kinji Hafsat" kukan tane ya tsanan ta,harga Allah bata koda sanjin muryar Abdul wlhy ta tsaneshi.....

Tir qashi ga alamafa Abdul ma ya jajibowa kanshi qiyayyar Elham matuqa,gashi shi kuwa yafara yin laushi,muje zuwa dai kuna tare da alk'amin mom Nu'aiym....

Hafsat ElhamDove le storie prendono vita. Scoprilo ora