page 5

3K 220 1
                                    

*🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

*Aunty Mejiddah Musa,Wannan shafin nakine kyauta duk ke kadai,na gode da kaunarki agareni*

05
Tana zuwa tayi Sa'a ba kowa kai tsaye dakinta ta wuce,fadawa tayi kan gado a rigin gine ta saka kuka me tsuma zuciya....duk'awa yayi ya dauki kwalin wayar da sim card d'in yabi bayanta dashi,da sallama ya isa gidan bakowa se k'anwarta Halima,tana ganinshi ta mik'e tsaye daga wanke kwanukan datake tace
"Yaya Yarima Barka da zuwa ina wuni?" D'an kallon yanayin gidan yayi ba laifi Ba kazanta sedai warin dabbobin dasuke kiwo a gefe d'aya, yace "lapia ina Elham?" Dan Sosa kai tayi tace "Ni kadaice agidan amma inaga sanda nashiga Sallah kamar naji shigowarta bara na duba d'akinta" batare data jira cewar saba ta juya zuwa d'akin, dage labulen kofar tayi tace "Aunty Hafsat ga Yaya Yarima yana magana dake" d'an saisaita kanta tayi batare data juyo ba ta ce,banasan tsayuwa a waje,ki kawoshi cikin d'a kinnan" juyawa kurun tayi domin tasan da matsala taje ta kawo shi har kofar dakin tace ya Shiga.....A yanda ta kwanta kife haka yazo ya sameta still kukan takeyi mara sauti sosai,sosai yaji ba dad'i,harga Allah kukan mace na karyar masa da zuciya ya sani kuma sam be kyauta ba yanda ya sakar mata maganganu,Shifa Wannan kurin da nuna cewar ita watace shine yake bashi haushi dashi,dakin yafara bi da kallo komai k'al k'al,gashi bazakace d'akin acikin gidan yakeba se tashin kamshi yake ya hade da Air conditioner dake dakin,kai dubanshi yayi zuwa ga mirror nata,mamakin manya manyan turarukan dake kai yakeyi,albashin ubanta baze siye daya daga cikin suba,lallai momy ta sangartar da Yarinyar nan,a hankali ya tako yazo daf da ita zama yayi kan gadon ya sanya hannunshi ya d'ago ta,batayi musu ba ya dauki kafarshi ya daura har saman gadon ya juyota ta fuskance shi ya sanya hannunshi ya tallafo kanta ya sanya hannunshi ya share mata hawayenta,so yakeyi yace mata tayi hakuri amma girman kai ya hana,tausayinta yakeji amma yanajin kiyayyarta can kasan zuciyar sa,yayi iya yinsa harshen sa ya furta Kalmar hakuri amma ya kasa,ganin haka ya sanya yanjanyota zuwa kirjinsa,a hankali yake patting bayanta,shida ita bazasu fad'i tsawon lokacin da suka dauka a haka,kawai dai gani yayi jikinta duk ya mace dagotan dazeyi yaga tana bacci,mayar da ita yayi kirjinshi yana mamakin kanshi bayaso ya motsa yakasance bacci nta beyi nisa ba ta farka,yakusa 30 mnt tana jikinshi yana jin yanda har lokacin take shasheka tana sauke ajiyar zuciya, ganin baccin nata yayi nisa ya sanya ya kwantar da ita da kyau ya mik'e tsaye yana kura mata manya manyan dara daran inuwanshi,lumshe ido yayi yana mamakin dalilin dayasa yake Kallonta, waige waige ya soma yi a d'akin can ya hango sckool bag nata ya dakko ta ya zaro paper da pen ya rubuta dakyar "I'm sorry Elly,plss call me as soon as u wake up" ya dakko wayar ya zura mata layinta ya kunna sannan ya jona caji ya bar gidan gaba d'aya..

Wanka yayi ya shirya kwanciya,har ya Hau gado ya kwanta yayi adu'o insa Amma ya kasa bacci, duk motsi d'aya tunano yanayin da suka kasance atare dazu yake,dogon tsaki yaja yace a sarari "Wannan er iskar Yarinyar ta gama sabawa da maza,har ta samu damar yin bacci a jikina muna fukar banza,tagama nuna wa momy itadin ta kwarai ce" har bacci ya daukeshi yana mamakin kanshi yanda ya kasa manta Wannan moment din,dakuma yanda kwalwarsa keta tariyo masa uban tsallen da ta doka a shop dasukaje dazu,yarasa dalilin daya sanya tsallen ke bala'in bugeshi.

Elham ba ita ta farka ba se asuba da mamakin kanta ta duba agogo,tayi mamakin baccin datayi iya saninta bazata tunano sanda tayi bacci sanye da kaya ajikinta ba,ga kuma fitila a kunne,tunano abinda ya faru tayi jiki a san yaye ta tashi taje tayi wanka ta daura alwala tazo tayi sallah,nan ta zauna tana ta adu'a, Idan aurenta da Abdul ba alkhairi bane kar Allah ya tabbatar dashi,tana aduar neman gafarar kwanciya da tayi ajikinshi har tayi bacci alhalin hakan ya haramta a tsakanin su,nan dai ta ga saqon shi,taga wayarta,banza ta mishi se Wuraren karfe bakwai da Rabi ta fito ta gaisa da mahaifiyarta ta daura musu breakfast soyayyen dankalin hausa da kwai,ta hada ruwan shayi ta kai dakin Innah sannan ta dauko nata tazo tadan tsakura,ta ajiye....wayar tane tana yana ringing tana dubawa taga Abdul ne,d'agawa tayi tamkar bata san magana tace "Yaa Abdul ina Kwana" gyaran muryarsa yayi "lapia lau kin tashi lapia elly?" Shiru tamasa yace "karfe tara ki shirya zamuje Kano dake da feenah da Raihan,se bayan sati d'aya zamu dawo Idan munje,zan koma ne nanda wani satin kuma da siyayyar da zamuyi" langwabe kai tayi tace

"Yaa Abdul banida wanakken kaya fa,mafi akasarin dogawen riguna suna gun wanki plss Abari gobe mana,Idan na karbo" sosai ta bashi haushi yace

"Kinga nifa ba laifi na bane,momy ce ta ce lallai yau zamu tafi so kije da kanki ki sanar mata uzurinki" da sauri tace

"Kayi hakuri yaa Abdul bara kurin na ebi laces da atmfa,momy ta hana ni tara wanki fa,kuma kaga jiya na kammala exams ban samu na kaiba"
"Karfe 9 ya miki a mota kinji bana san Wannan African time na kau yanci" kantayi magana ya kashe wayar sa ya kama hanyar part din momy,a gurguje taje ta sanar da Innah da Baba anan takejin seda aka tambayi baban ta ma,har hada ka yanta tayi ta fito waje kai tsaye part din momy ta nufa taje kusa da ita ta zauna tace " momy na shirya" Shafa kanta tayi tace "Allah ya kiyaye Mamana,dan Allah ki kula da kanki sosai ki tsare mutun cinki kamar yanda nasan kinayi,kuma ki kula da mijinki daidai gwargwado,kai kuma Babana lallai ka kular mun da Mamana amana ce na baka kakuma san yanda amana take ko" girgiza kai yayi,ta zaro wayar daya siya mata tace tana kallon momy tana Murmushi "Momy kinga wayar da yaa Abdul ya siyamun jiya,momy ki tayani godiya dan Allah jiya jiyannan tawa ta fadi ta cinye screen d'in" Murmushi momy tayi,har ranta taji dad'i tace "Angode Babana Allah ya saka da alkhairi ya kara bud'i" shima yaji dadin adu'ar ta matuka,a haka sukazo wurin mota dukkansu,Abdul ne ya kalli kannenshi Baba karami da Ashraf gasu feenah yace "Baba karami,Ashraf,feenah da Raihan ku karbi key din range dinnan ku biyo ni abaya,da mota biyu zamu tafi ni zan tafi da Elham" yana fad'a tamkar yayi kuka,Wannan tsarin momy ne,su kuwa masoyan dama haka sukeso se murna sukeyi zasusha hira soyayyah,Ashraf d'ane wurin yayan momy daya rasu kuma a hannunta yatashi, shine ze auri Feenah a yanzu haka yana aikine da kamfanin MTN,kayan lefe ne akace suje hadowa shine zasuje.....

Yamma likis suka isa Kano,a Tahir guests palace hotel sukayi masauki,kallon Baba karami yayi yace"k'arami wayannan matan a kama musu suit Babba,ku kuma kujewa d'aki d'aya " kallon shi yayi yace "Yaya Abdul kaifa?" Wrist watch nashi ya kalla yace "Ba anan zan sauka ba ku dai ku zauna anan,kuma dan Allah banda shishirta,kusan wayannan yaran matsayin kannen ku suke ku kula da mutuncin su" haka kawai Elham taji ba dad'i tace tana shagwabe wa "yaa Abdul dan Allah kaima ka zauna anan" kura mata ido yayi nay'an dak'ik'u yace yana mayarda kallon shi ga Baba karami "Zan muku waya goben ku shirya early,zamu fita da range dukkanin mu" Da sauri ta sake jakarta tazo ta rike masa hannu "yaa Abdul dan Allah ka zauna anan hotel d'in" cikin fad'a ya warce hannunshi yace "ke Wannan wane irin rashin hankaline,kece zaki gayamun inda zan zauna kokuwa,bakida hankali" take idonta ya ciko da k'wallah su feenah suka kwashe da dariya sosai Wannan ba karamin bata ran Elham yayi ba,har ranta taji zafi.....bece komaiba ya ja motar shi yabar harabar hotel d'in, dakin da aka saukesu kowa tayi wanka aka kawo musu abinci suka ci banda Elham yoghurt kurun tasha tace ta koshi,silent ta saka wayarta ta fito waje,tasamu wurin flower bed dake zagaye wurin ta sadda kanta tana kuka me ban tausayi,kyakyawan saurayin datun fitowarta ita yake kallo yazo ya zauna wurin yace,cikeda iya tsara kalamai

"K'anwata duk abinda yayi zafi magani nsa Allah,da Wannan kukan dakike dama zuwa kikayi kika daura alwala kika nafila ki mikawa Allah kukanki,kuka baya maganin kowace irin damuwa a rayuwa dan Allah ki sassauta kukannan my sister" a hankali ta d'ago ta kalleshi tana Murmushi tace "Nagode da kulawarka dan uwa,Allah yabar zumunci zan gwada inshaa Allah" Murmushi yamata yace, ko zaki taimakamun da phone number dinki,ina tare da mahaifina Munzo wa'azin kasa da akene kuma yanzu zamu tafi" batayi musu ba ta bashi number yabar wurin yana mata Murmushi, bata saniba komai daya faru akan idon Abdul ne. Cikin dare tasha kuka ba ka danba,washe gari kuwa kowa yashirya fita banda ita,sukace da ita tazo suje tace bazata ba,mamaki sukayi Raihan tace "wa kikeso ya zab'a miki kayan to? Banza ta musu sukayi tafiyarsu,koda sukazo mota yaga Batanan,yace dasu tana na? Wai tace bazata ba,bece komai ba ya nufi d'akin,kwance ya sameta yaje ya zauna kusa da ita yace " Elham I'm sorry kinji" kallonshi tayi tace what for" dakyar yace "about yesterday mana" juya masa baya kurun tayi ta soma.
C

Hafsat ElhamWhere stories live. Discover now