💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
~nake nema~*True life story*
*💦Talented writers forum*💦
*{T.W.F}*
*Written by husnah mb**🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
Thanks for ur support All the tym...*3⃣-4⃣*
Haka Nasreen tayita bashi labarin school dinsu shidai babu abunda yake banda dariya har magrip ta gabato sannan ta rakashi gate ya tafi.
_The next day_
As usual tun bayan nasreen ta idar da sallan asuba ta farayiwa ummy aikace aikacen data sabayi mata kullum kafun ta tafi school, da yake yanzu anyi hutu a school bayan ta gama yiwa momy aikin komai da komai dakinta ta gyara wanka tashiga tayi around 8 ta koma bacci.
_Around 10 o'clock_ affan ne ya shigo hannunsa dauke da leda yana kwallawa Nasreen kira Anty amarya ce ta fito tana tambayanshi lafiya kuma yaketa irin wannan kiran murmushi affan yayi tare da cewa antie Ina nasreen ne ta shiga ne yaukam nasan dai anyi musu hutu amma tun dazu naketa kwalla mata kira shiru bata fito ba anty amarya ce ta amsa da waya san mata ne amma ina tunanin tana dakinta ka shiga ka duba manah owk ya amsa dashi tare da nufa hanyan dakin Nasreen
_"Handle_ din kofan dakin ya murda tare dasa kai ya shiga kwance ya hangota saman gado tanata sharar bacci kaman wanda tasha kwaya _Nasreen!_ _Nasreen!_ shiru bata amsa ba bakin gadonta ya kariso tare da dukan dogayen sawunta da sauri ta mike cikin magana irinta masu bacci tace
"Yaya affan lafiya kuwa affan ne yace dallah malama nikam ki bude ido muyi magana kinzo kin kwanta kinata sharar bacci kaman wata macecciya bude idonta tayi sannan tace bari kawai yaya affan wlh ina biyan bashin baccin dana dade banyi bane dariya yayi tare da mika mata ledan da yake hannunsaNasreen ne tace bro meyene acikin nan kuma murmushi yayi sannan yace abba ne ya bani kudi jiya yace na sayo miki da sauri ta karbi ledan ta bude.
_Wow Thank You so much my abba_ Allah dai yabarmin kai ta fada tana dariya affan ne yace nikuma dana sayo baza,amin godiya ba koh dariya Nasreen tayi tare da ajiye ledan da yake hannunta ta rungume affan.
Thank You Yaya affan na gode sosai murmushi yayi tare da cewa _Never mind my kanwa_ ai kin wuce haka_Really_ ta fada sounding very excited daga mata kai yayi alaman eh
Sakeshi tayi tare da dauko tab din da yake cikin ledan ta budeAffan ne yace maza my kanwa kisashi a charger zuwa anjima intayi full zanzo nayi miki Settings din komai da komai kinji
"Asawa tayi da TohTashi yayi zai fita har yakai bakin kofa sannan tace my kanwa intayi full i should know kinji ina dakina To ta amsa mishi dashi tare da saukowa daga kan gadon tayi flugging din Tab din a charger
Daga kanta tayi dan ta duba agogon dake manne kan bangon dakin ganin har fast 10 yasa tayi saurin fadawa toilet dan tasan yanzu tayi latti wanka tayi shaf shaf tayi shirin zuwa islamiyya.
Dakin abba ta fara shiga tsugunawa tayi ta gaisheshi abba ne yace mama na zaki tafi islamiyya kenam amsawa tayi da eh abba har nayi latti mah bansani ba murmushi yayi tare dace mata to maza tashi ki tafi kar,a zanamin ke harta isa bakin kofa saita tuno batayiwa abba godiyan tab din daya saya mata ba da sauri ta juyo inda yake cikin tsamin murya tace abba ya affan ya kawomun Tablet din da chocolatey
_Thank You so mucu my abba,_ i love You so much dariya yayi tare da cewa love You too mama nah.
a tsakar gida ta tarar da ummy gaisheta tayi ta kuma sanar da ita zata tafi islam... addu,a sosai ummy tayi mata sannan ta tafi.Tana fitowa a hanya ta tarar da Naseer tsaye shida Abokinshi Sadeeq tana hangoshi ta fara dariya da sauri ta karisa inda yake tana fadin
"Good morning Bro
Morning how are You lil sis am fyn ta amsa dashi
sadeeq ne yace oh ni baza,a gaisheni ba kenam murmushi nasreen tayi sannan tace _oh am so sorry_ abba wlh banma ganka ba nikamSadeeq ne yace ina zaki ganni daughter kinata surutu da yayanki, murmushi Nasreen tayi sannan tace kasan bro din nawan aina daban ne
Murmushi Naseer yayi tare da cewa lil sis muje na rakaki kinji rabuta sadeeq karyasamin ke kiyi latti dariya tayi sannan ta tafi ya bita a baya, jakan hannunta ya karba ya rike mata suna tafiya suna tadi harsuka isa,
Har bakin class dinsu ya rakata, jakanta ya mika masa godiya ta masa tana dariya hartashiga class sannan ya juyo._Wanene Naseer_
Naseer dane daya tilo wurin Alh umar faruq da Hj hafsa.
Hajiya hafsa ta kasance mace maison danta kasancewar shi kadai Allah ya bata hakanne yasa ta dauki don duniya ta daura masa hj hafsa mace ce maison jama'a hakanne yasa kullum gidanta baya rabo da mutane. Alh umar faruq dan kasuwa ne asalinsu da hj hafsa yan garin kashare ne kasuwanci ne ya kawoshi garin gombe
Sauran yan uwansu suna kashare har illah yau._Naseer_ ya taso cikin kulawa kasancewa shi kadai Allah ya bawa iyayensa duk da kuwa ba masu kudi bane suna bashi kulawa daidai yadda ya kamata kuma suna nuna mishi kaunar daba ko wani 'da yake samu daga wajen iyayensa ba duk da kasancewarsu talakawa hakan baisa sun gaza wajen bashi ingantacciyar rayuwa ba.
Yayi pry&Sec school dinsa a ma'ahad bayan ya kammala secondary skull dinsa yayi joining diploma gombe state university (gsu) inda ya karanta _social studies_ a yanzu haka ya samu aiki yana koyarwa a _hamdan collage primary nd secondary school_
A matsayin teacher da student suke matukar sonshi kasancewa yanada fara,a dason yara._Cigaban labari*_
Around 12 aka tashi su Nasreen daga islamiyya
"Ana tashinsu daga makaranta Nasreen harzata fito taji an jawo hijabinta. Da sauri ta waigo wanda ta ganine yasa ta saki murmushi juyowa tayi ta isa inda yake malam ne yace haba Nasreen yau kuma ina kike sauri haka zakije bakizo mun gaisa ba sosai kai tayi alaman tadanji kunya sannan tace wlh malam yau zanje gidan kaka ne shiyasa naketa sauri na koma gida dariya malam yayi sannan yace Nasreen yar kaka kenam gaisawa sukayi sama sama dan gabaki daya hankalin Nasreen yayi gida.Nasreen na fitowa harta kama hanyan gida sai kuma tace bari ta fara zuwa gidansu Yaya Naseer kafun ta koma gida ta shirya kasance gidansu ya naseer yana bayan gidansu ne makota ne.
Hakan yasa nasreen bata zarce to inaba sai gidansu naseer yana daki zaune shida umma shi ya shiyo sallamarta da sauri ya futo fuskanshi dauke da fara,a tana ganinsa da gudu taje ta rungumeshi tana dariya Nasir ne yace baby nasreen harkon taso kenam dariya tayi sannan ta eyii wlh yaya an tashi harzan tafi gifa nace barina fara zuwa na gaisheka tukun murmushi yayi tare da cewa to godiya nake bby nasreen
"Bro where is umma ta fada murmushi
Tana daki ya fada yana kallonta
Muje na gaisheta toh saina tafi koh
Owk let's go ya fada tare da wucewa gaba ta bishi a baya a falo suka tarda umma tana kallo da sauri nasreen ta isa inda umma take tsugunawa tayi ta gaisheta cikin fara'a umma ta amsa tana fadin nasreen yan makaranta, ya ummy ki lafiyanta qlau nasreen ta amsa dashi maza inkinje gida kice ina gaisheta kinji toh tace tare dashi tace umma barin tafi
Gaba tayi naseer ya bita a baya
YOU ARE READING
ZABIN ALLAH
RomanceWannan labari ne akan wata yarinya data fada tarkon soyayya wanda ya kunshi abubuwan da suke faruwa da dama a duniya musamman mah" ga ma'abota soyayya