💦💦 *ZABIN ALLAH*💦💦
~nake nema~*True life story*
*💦Talented writers forum*💦
*{T.W.F}*
*Written by husnah mb**🙏🏻Dedicated to Teemah jalo*🙏🏻
Thanks for ur support All the tym...*9⃣-1⃣0⃣*
Haka malamin ya gama musu karatu Nasreen ce ta fara bada hadda cikin sa,a kuwa dayan malamin nasun baizo ba aka tashesu da wuri tun 11.
Tana ganin yarinyar tashi zata fita nasreen tayi sauri tasha gabanta, yarinyar ce tace ke dalla malama matsamin na wuce murmushin takaici nasreen tayi sannan tace dama inaso na tambayeki ne meyasa zaki tunku dani dazu alhalin ban miki komai bah.
Yarinyar ne tace an tunkuda ki din ko zaki rama ne, na takaki kuma na taka banza da wofi jaka wawiya kawai tana maganan tana murgudawa nasreen baki irinna marasa kunya
Takaici ne ya kama nasreen dan ba karamin ciwon abunda yarinyar ta fada taji bah
Da batayi niyyan kulata ba dan batason fada a makaranta saboda kullum ummy da Yaya naseer suna mata fada akan karta yadda tana fada a school
" Yaran class dinne taji suna cewa karki barta nasreen dama haka take ta raina kowa a class dinnanMurmushi nasreen tayi tace dani zakiyi fada a tsiwace yarinyar tace ke wacece da baza,ayi fada dake ba, ashfat dake gefen nasreen duk jikinta rawa yakeyi sai cewa nasreen takeyi _my nasreen_ karki kulata dan Allah kizo mu tafi kinji wannan yarinyar tafiki karfi, yarinyar najin abunda ashfat ta fada ta kaiwa nasreen duka da sauri nasreen ta sunkuya yanayin yadda takai dukan da karfi shiyaja ta fadi kasa da sauri nasreen ta sunkuya ta kaiwa yarinyar mari danneta tayi tayita kai mata naushi yara koh sun samu abunda sukeso nan da nan class yadau magana sai ihu yara sukeyi suna dariya.
Malamin da yake cikin office din malamai kasancewa shi kadai ne ya saura malamai sun fara watsewa shi yayi hanzarin fitowa jin ihun da kuma dariya, ganin abunda ke faruwa yasa yayi saurin zuwa ya dakatar da nasreen yarinya kuwa babu abunda take banda maida nunfashi da kuka dan taji hannun manya.
"Nasreen ne tace yanzu ina bakin yiwa mutane rashin kunya da tsiwa kinga yanzu na koya miki hankali gobe ba zaki kara rainawa mutane wayo ba
Yarinya kam ta kasa cewa komai sai zurawa nasreen ido tayi tana hawaye shidai malamin kawai murmushi yayi jin abunda nasreen take fada duk da baisan meya hadasu ba yasan yarinyar ce batada gaskiya dan yasan tunda nasreen ta shigo islamiyya bata taba fada da kowa ba.
Tambaya yahauyi meya hadasu fada duk yaran class din suka hada baki da cewa Naela ce batada gaskiya malam saboda ita ta fara tsokanan nasreen kuma taki ta bata hakuri, da yake malamin yasan halin Naela tanada masifa kusan kullum sai,an kawo karanta office dinsu, hakan yasa bai dauki wani matakiba ya bawa naela hakuri kuma ya umarci nasreen ta bata hakuri, fuskan nasreen a tsume ta bawa naela hakuri itama ta bata sanna kowa ya futo yara sai tsaigumi sukeyi.Suna fitowa ashfat tace wlh nasreen ban zata zaki iya dukan naela ba bakisab yarinyar bane ga shegen masifa ga kuma karfi kaman doki shiyasa kowa tsoronta yakeji babu mai iya fada da ita duk class dinmu jiyama naji yan class dinmu suna cewa wai zata dawo _Matrix_ ni wlh har tsoro nakeji Allah yasa kar,a sata a class dinmu.
Murmushi nasreen tayi tace to an fada miki kowa matsoraci ne irinku ai wlh barin fada miki ni bazan kyaleta bah duk randa ta karamin tsiwa casata zanyi dan banson rashin kunya kuma ban iyata itadai ashfat ta kasa cewa komai sai dariya takeyi.
Saida nasreen ta raka ashfat har gida dan ta fuskanci ashfat tana tsoron kar Naela ta biyota ta rama a kanta saboda itace kadai kawar nasreen a islamiyya.
Harta kama hanya sai kuma taga ai yau da wuri aka tashesu gidansu Nasir ta nufa a kofar gida ta tarar dashi yana zaune yana hangota tundaga nesa yasan yau an taba masa lil sis dinshi da sauri ya taso ya nufi inda take,
Hannunta ya kamo lil sis _what happen with You_
danke hannunshi tayi fuskanta babu alaman fara,a tace bro wata jakace ta batamin rai a islamiyya murmushi yayi sannan yace to muje mu gacan benchi ki bani labari to tace.Kan benchi suka zauna nan ta kwashe labarin yanda sukayi da Naela ta bashi dariya ce ta kubuce masa nasreen ne tace bro kaima dariya kakemin koh shikenam babu damuwa na tafi ta fadi maganan kaman zatayi kuka da sauri ya riko hannunta ya zaunar da ita
''A,a lil sis nifa bake nakeyiwa dariya ba da wanda kukayi fada wlh nake dariya an fada mata sis din tawan batada karfine ai gara da kika mata haka kinga gobe bazata kara rainaki ba murmushi tayi da sauri tace haba dai bro kace nayi daidai da sauri yace
_Excellent_ amma fa kinsan meyene daga masa kai tayi alaman a,a karki sake fada a school kinji lil sis babu kyau wannan yazama na farko kuma na karshe duk wanda ya nemeki da fada ki shareshi saboda karnuka ne suke fada kinga inbaki kulashi ba shine ya zama karenDariya tayi sannan tace to shikenam bro insha Allahu bazan sake fada da kowa bah
_-''promise_? _Yes i promise_ ta fada tana dariya..._yawwa to maza muje na rakaki gida kinji tashi tayi sai kuma ta tsaya kaman ta tuno wani magana nasir ne yace lil sis lafiya kuwa da sauri tace bro plss zakana min lesson murmushi yayi sannan yace ina uncle sagir din kuma?
Ya mutsa fuska tayi sannan tace ai yanzu ya daina min lesson
Meyasa lil sis ya fada da sauriBro wlh bai iya maths ba ko kadan kullum inyazo banda shirme babu abunda yakemun kuma bro inna masa gyara sai yacemun babu abunda na iya ni kuma kasan na tsani acemun jaka
murmushi nasir yayi yace a.a lil sis ai tanada ilimi shine dai bai gane ba murmushi tayi tace da gaske bro, daga mata kai yayi alaman eh
Bro ina zakanamin koh Shiru yayi sannan yace zanna miki manah lil sis_"Are You serious ta fada da sauri?
Yes am very serious
Tsalle tayi yawwa bro _Thank You so much_Naseer ne tace to muje maza na rakaki gida kinga rana tayi koh.
Tafiya suke tana bashi labari har suka isa kofar gidansu gida ta shiga shi kuma ya juyo.
Tana shiga gida da murnanta dakin anty amarya taje tana tambayan ko abba ya dawo eh anty amarya tace mata da murnanta ta fita tabar dakin.
_''dakinta ta fara shiga sanda ta canza kaya sannan ta nufi dakin Ummy
"Ummy dai mamaki ne ya kamata ganin yanda taga Nasreen tana cikin farin ciki wanda batasan dalilinsa bah ummy ne tace habibty lafiya kuwa murmushi nasreen tayi tace ummy nah lafiya qlau barinje gun abba na dawo to ummy ta amsa dashi nasreen tayi ficewarta,Dakin abba ta wuce direct a falo ta tarar dashi yana kallo da gudu ta karisa inda yake tana dariya abba ne yace mama na kin dawo kenam na dawo abba ta amsa mishi dashi.
Abba ne yace mama nah yau lafiya kuwa na ganki cikin farin ciki, lafiya qlau abba dama nazo ne muyi wata magana murmushi yayi yace to meya faru hajiyata ina jinki
Yawwa abba dama inaso ka canzamin uncle din lesson ne wlh uncle sagir yanamin shirme in munyi lesson yamin maths innaje skull teachers dinmu suna cemun ba correct bane kumafa abba nayi masa correction yacemun wai nine jaka kumafa abba shine yakeyin shirme ba teachers dinmu bah
Abba dai shiru yayi yana jaddada ilimi irinna nasreen harta iya yiwa malami gyara shirun da abba yayi ne yasa nasreen tace abba yaya kayi shiru tana maganan kaman zatayi kuka.
YOU ARE READING
ZABIN ALLAH
RomanceWannan labari ne akan wata yarinya data fada tarkon soyayya wanda ya kunshi abubuwan da suke faruwa da dama a duniya musamman mah" ga ma'abota soyayya